INAYAH 31-40

Tsit taji gidan duk da dama basuda wani manyan motsi a gidan Amma tsit taji da alama kaman umma yaganah basa gidan.
A dining yake zaune yana Shan ruwan yakasa cin abincin dake jere gabansa
idanuwansa sun sauya sosai sbd yau wani irin daci ne da quncin zuciya tareda damuwar shekaru suke tasowa suna komawa sababbi fal Kaman yanda komai yafaru alokacin bayan…,
Baitaba sanin zai Kuma fuskantar maimaicin abinda yafaru dashiba alokacinda yake cikin radadi da zafin maraicinsa abayaba.
Rintse idanuwansa yayi cikeda daci Mai tsanani dayake sake cika maqoshinsa…
Qamshin Turaren Inayah duk da Bata wani sakaba da yawaba yasashi bude idanuwansa dasukai jajir Yana kokarin basarda yanayinsa sbd kada tagani ta daga hankali da tambayarsa abinda yake damunsa.
Jin takunta ya nufi wani direction din yasashi waiwayowa ahankali ya kalli hanyar.
Riga da wandone ajikinta na masu Fadi sosai Amma basuda nauyi ko kadan sai suke saka kirjinta da bra rawa qaramar hular kayan ce kawai akanta Bata Gama rufe baqin gashintaba da akaiwa gyaran aure Amma auren baiyiyuba.
Dauke kansa yayi daga kallon gurin tareda miqewa ya nufito ganin hanyar palon dazatakl kaita gurinsa ta nufa Kuma yasan su Alhaji babbah da dangin Hadiza da Hadizan suna ciki sbd maganganun da zaayi…
Shigarta hakan gurin zai iya bayyanarda raunin tarbiyarta ga Hadiza da danginta dake gurin harma da Dr Abdul Wanda zai Mata kallon da zai iya Zama laifi ga ubangiji.
Qaramin palon daya rabasu da palon Abbin ta Isa Zata shige taji anriqo hannunta ta baya.
Batada qarfin razana Amma duk da hakan a tsorace ta waiwayo sbd riqon bana mace bane hakama tasan basuda namiji a gidan dazai shigo har nan bayan Abbinta.
Tana juyowa acikin idon Abbin idonta yafara fadawa akaron farko dataji tsoro da fargaban kallon idon Abbin…
Da sauri ta maida kallonta kansa tana bayyanarda tsoronta da damuwarta tace”
Abbi..
Kasa magana tayi sbd idanuwanta dake kokarin cikowa da hawayen da batamasan na menene ba ita dai tasan Abbinta shagwabarta akansa ta qare Dan haka yanzuma tasan bazata iya dainawa sbd kallonsa kawai nasa taji duniyarta alhmdllh sbd samun tsayayyen uba kamansa sai Mai saa irinta.
Matsowa tayi tana sake riqe hannunsa cikin hawaye tace”
Abbi Dan Allah kayi hakuri idan fushi kakeyi sbd na nace Akan zuwa asibiti dubo heart…
Tun jiya Banda lafiya sosai abbi baka..
Saketa yayi tareda zare hannunta daga riqon datai Masa
Tabisa da kallo tana jin sabon kuka na zuwar Mata sbd ganin kaman fushi yake da ita sbd ta saba riqe hannun mahaifinta ko bayan ta girma Bata daina riqe hannunsa Amma yau din ya zare batareda ya kalletaba.
Juyawa yayi Yana komawa palon ya zauna Yana cewa”
Akwai baqi aciki koma ciki anjima zansa Dr farhat tazo ta dubaki.
Kuka ya fashi dashi tareda zuwa gabansa ta durqusa tana hawaye masu gudu tace”
Abbi Dan Allah kayi hkr idan nayi laifi,
Kamun hukuncin laifin ma
Amma Dan Allah kada kabari a rabani da Heart Abbi…..
MAMUH
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Shedar biya????
07040727902
MTN card????
09134848107
[11/2, 10:00 AM] It’s Queen Meenali????: 36
Arewabooks@Mamuhgee
Ahankali ya waiwayo ya kalleta
Ganin irin kukan datakeyi yasashi Dan sauke ajiyar zuciya Yana nazarin halinda tashiga duk tabi ta sauya sbd kuka da damuwa da tashin hankali lokaci kankani.
Dr Abdulsamad ne ya sulale daga palon batareda sanin kowaba ya shigo ciki Yana Jin idan ba ganin Inayahn yayiba bazai fahimci dukkanin abinda akeson fadaba a zaman.
Umma yaganah data lura da fitarsa ta miqe ta biyo bayansa sbd fargabar abinda shedan zai iya sawa su aikata shida Inayahn idan sun hadu,
Itakuma yanzu Kam tunda aka daura auren INAYAH da MAJEED batajin tanada abinda yakai Mata wannan auren mahimmanci sbd dai basuda yanda zasuyi aure an daura Dan haka kowa hakuri zaiyi a runguma wannan qaddarar gabaki daya.
Shigowar Dr Abdul yasa Inayah dakatawa daga rokon datakeyiwa Abbi ta zubawa Dr Abdul din idanuwanta tanajin kaunarsa na sake karyar Mata da zuciya..
Meyesa ummansa Bata tashi bayyanaba sai alokacinda zasu mallaki junansu.
Dr Abdul ma kasa riqe hawayensa yayi dukda zamtowarsa namiji agabanta.
Qarasowa yayi ya durqusa gaban Abbin shima tareda sunkuyar da Kai Yana tsiyayar hawaye cikin yanayi na damuwa Mai tsanani da quncin dake cinsa cikin zuciya yace”
Sir Dan Allah kada ka rabani da Inayah idan ta haramta aguna matsayin Mata Dan Allah kabani ita matsayin ‘yar uwa tunda hakan Bai haramtaba.
Kukan tausayin Dr Abdul din yakuma zuwarwa Inayah ta kalli abbin dayaqi ko kallonsu yayi shiru cikin nasa nazarin.
Idanuwansu sun rufe suna roqonsa
Inayah roqonsa takeyi akan ya warware auren da aka daura sbd har abada bazata iya karban Abbinta amatsayin mijiba.
Irin kukan datakeyi shine yake Sosa ransa ba girman kalaman datake fadaba,
Har cikin ranta take bayyanarda quncinta na auren,
Bazata iya karban wannan aurenba,
Ta zabi yaci gaba da Zama ubanta har qarshen rayuwarta…
Umma yaganah dataga irin kuka da Inayah keyi ya daga hankalinta sosai Musamman ganin shima MAJEED din yanda idanuwansa suka sauya sosai batareda ya juyo ya kalli su Inayahn ba.
Miqewa yayi tsaye ahankali ganin tana neman shaqewa sbd kuka numfashinta Yana hardewa alamar wani attack dinne Zata Kuma samu…
Idanuwansa ya juyo ya zuba Mata Yana kallon yanda numfashinta ke kokarin rabuwa da kirjinta duk akan aurensa daya rataya akanta,
Meyesa tun farko ya aminta da auren sbd tunanin shine mafitar da Zata Hana kowa karban Inayah daga hannunsa…
A zuciyarsa kusan yafi kowa Jin kunci da shiga matsananci hali akan wannan yanayin dahar yakai ga wannan auren Wanda shima yasan yin auren kawai akai bazai taba kallon ‘yarsa amatsayin maceba bare matar da….kasa qarasa tunanin yayi sbd nauyin da dacin kalaman.
Da gudu umma taqaraso tana kokarin kamo Inayah
Inayahn ta miqe da sauri tana sake rarrafawa gaban Abbi tana roqonsa numfashinta ko fita daidai bayayi.
Cikin tashin hankali umma yaganah ta sake tarota tana miqar da ita tsaye tace”
INAYAH kinada hankali kuwa?
Kinsan me kike fada?
Wane auren kikeda qwarin gwuwar cewa araba?
Cikin kuka tace”
Umma yaganah wlh bazan iyaba,
Bazan iyaba,
Rayuwar auren da akeson ayi tsakanin ma’aurata bazan iya yinta da Abbi ba wlh,
Rayuwar auren dazanyi bazan taba yinta da Abbi ba,
Umma bazan iya kwanciya gado……
Suka umma yaganah takaiwa bakin tanajin baqin ciki da takaici harma da tashin hankali sbd yanayin MAJEED duk kannewarsa Yana bayyanarda bacin Rai da griman tasirin da maganganunta keyi a ransa.
Ajiyar zuciya Mai sanyi abbin ya sake Yana kallon yanda numfashinta ke kokawa da Isa yasake sauke numfashi Yana Dan dauke idonsa daga kallon kirjinta dake harbawa sosai sbd halinda take ciki.
Fuskarta ya kalla ahankali cikeda kulawa ya kalleta tareda riqo hannunta daga jikin Umma yaganah ya zaunar kan kujera tareda kallonta Yana nazarin kalamanta dasuke bayyanarda haqiqanin Gaskiar abinda yake ranta.
Cikin nutsuwa da sautin muryarsa Mai nutsuwa da kamewa yace”
Inayah!!!!!
Kasa dagowa tayi ta kallesa sai hawayenta dake gara gangarowa daga Idanuwanta dasukai mummunan kumbura.