GURBIN IDOINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 31-40

Kukan dakikeyi Zaki jawa kanki ciwo akan wannan unnecessary Al’amarin,

Auren ne yasaki wannan halin right?

Gyada Kai tayi wasu zafafan hawaye na Kuma ganganro Mata.

Kai tsaye Bai tsaya komaiba yace”

namiki alqawarin sauke Miki wannan auren daga lokacinda kika yarda da qaddara kika San aure tsakaninki da Abdul ya haramta,

Zan sauke Miki auren ki koma hannun mahaifiyarki da Abdulsamad kimun alqawarin bazaki Bari shedan ya Shiga zuciyarkiba kiyi watsi da tarbiyar Dana Baki.

Dago jajayen idanuwanta tayi da basa iya budewa sosai ta kallesa Jin Zata bar hannunsa Wanda ita Batasan wannan yarenba kwata kwata bazata taba barinsa Koda Zata rasa kowa a duniya.

Juyawa yayi ya kalli umma yaganah zaiyi magana
umma yaganah tayi saurin zubewa qasa tana neman fashe Masa da kuka tace”

Dan girman Allah MAJEED kada ka furta kalma daya data danganci rabuwar wannan auren…..

Rintse idanuwansa yayi Yana sake hadiye yanayin dayake ciki ya kalli Inayah dake kallonsa Ido na tsiyayar hawaye tana jiran kalamansa da zasu warware auren su koma matsayinsu na uba da ‘ya.

Tunda umma yaganah take Bata dukan Inayah ba bare ma agaban Abbi sai yau dataji kaman tayiwa Inayah din duka tashi Kisha ruwan gishiri Dan haka Batasan lokacinda ta ringa dukan Inayahn da mayafin Jikintaba tareda damqar hannunta tayi ciki da ita bayan ta kalli cikin tsakiyar idanuwan Dr Abdul dake zubarda hawaye shime ta buga Masa wani irin mummunan gargadin dayasa shi kallon Abbi Wanda yakasa cewa komai sbd kansa daya toshe Yana sake daukan zafi.

Wucewa yayi yabar Dr Abdul din a tsaye gurin Yana bin hanyoyin dasuka bi da idanuwa cikin tashin hankali sbd Koda yasan bazai taba auren Dan Inayah ba zaifi samun nutsuwa da sauki idan yasan ba auren kowa kanta.

Umma na shiga daki da Inayah tayi wurgi da ita tsakiyar dakin tareda kallonta cikin tsananin takaici da bacin Rai tarasa wane irin duka zataiwa bakin Inayahn,

Cikin kuka Inayah ta cusa kanta cikin tsakiyar qafafunta tana jin hankalinta Kuma na tashi da kalman Abbi na miqata ga matarda ake Kira da mahaifiyarta wadda haryanzu basu sake haduwaba tun ranarda tazo gidan komai ya lalace.

Daqyar umma yaganah ta samu danne zuciyarta Takoma palon Wanda dama MAJEED ake jiran yazo afara maganar da zaayi.

Koda Isa palon zaman taron yaqara yamutsewa sbd Dr Abdul da jikinsa ya rikice Dole suka bar gidan.

Umma Hadiza kaman zata Dora hannu akai tayita rusa ihu takeji sbd wannan masifar dake Neman dawo Mata,
‘danta daya Wanda take ganin ta Kama qwaqwalwarsa na Neman juyewa sbd son ‘yar uwarsa
Gashi tana neman rasashi batareda wannan datake ganin tasamoba Bayan shekaru tazo hannuntaba.

Bataso tafiyaba saita hadu da Inayah Amma MAJEED ya hanata ganin ‘yarta sbd yaqara nuna Mata ikonsa akanta.

Bayan barinsu gidan umma yaganah qin zuwa Inda Inayah take tayi sbd wannan karon tayi mummunan Kona Mata Rai.

Matuqar auren MAJEED yabar kanta Bata tunanin Inayah Zata samu mijinda zai kaisa agurin kulawa da ita Dan haka zatai iya kokarinta gurin ganin wannan auren baitaba rabuwaba Koda hakan na nufin da qarfin hali ta cusa Inayah gun MAJEED ya dirka Mata ciki taga yanda auren zai rabu kowama ya huta har Hadizan da ‘dan su huta dasu akan raba auren.

Ranar gidan ko abincin dare Babu Wanda ya fito ci sai Neesah kawai data fito itama snacks kawai taci takoma daki ta kwanta.

Acikin daren Abbi yayi booking ticket na zuwa Abuja akwai Wanda zai gani daga can zai wucewarsa Dan Yana buqatan kansa ya sake.

Washe gari qarfe 8 na safe yayiwa umma yaganah txt driver ya wuce dashi airport jirginsu ya tashi qarfe Tara.

Koda INAYAH ta tashi da safe jiki a mace tasan Bata kyautaba Musamman da umma yaganah ta matse fuska sosai Bata wani sake Mata ba
Duk saitaji tasake Shiga damuwa dan haka ko wanka bataiba da Riga da wandon bacci masu tsantsi ta wuce palon Abbinta Dan basa hakuri sbd Bata iya juran fushinsa akanta ko kadan,

Kuma ta wani bangaren gaskiyarta ce tafada bazata iya rayuwar aure da Abbinba sbd asalin life takeso arayuwar aurenta wanda Zata iya nuna soyayyar mijinta agaban kowa Kuma shima zai iya nunawa agaban kowa Dan haka Babu ta Inda Zata iya wannan rayuwar da Abbi Wanda takewa kallon ubanta Kuma uwarta.

Shine ya koyar da ita yakuma Bata tarbiyar fadar Gaskia komai dacin dazata kawo shiyasa koyaushe ake ganin wautarta Dan ita tasaba gaskiyarta take fada daga zuciya ba boye boye ko munafurci.

Kayan jikinta umma yaganah ta kalla lokacinda ta gaisheta tareda juyawa Zata nufa sashen Abbin.

Floral pyjamas ne na bacci ajikinta masu santsi farare,
Babu bra ajikinta Dan haka kirjinta dasuke tsaye qyam suna bayyanarda basa cikin bra din.

Ko hips dinta sosai suka fito a wandon kayan sbd santsin kayan yasa suka Dan lafe a jikinta.

Da adah ne umma yaganah hanata zuwa takeyi gaban Abbinta da kayan bacci sbd kusan rayuwar Inayah din babu ruwanta kusan koyaya tana iya zuwa gaban mahaifinta da towel ne kawai Bata iya zuwa gabansa sai guntayen Kaya Amma Dan kayan bacci dasu leggings duk ba komai bane agunta.

Umman na sane Sarai ta qyaleta ta Kama hanyar palon nasa batareda tace Mata taje ta sauyaba kokuma sanya wani Abu akai.

Ja’irar yarinya Allah ya nunan ranarda wannan bakin naki zai mutu yayi hankali.

Shima MAJEED din da haryanzu yake biye Miki yaqi bude Baki ya magantu dakyau ki dawo hankalinki.

Inayah nakaiwa kofa massage din MAJEED nashigowa wayar umma na cewan yayi tafiya.

Sanyi jikinta yayi tanajin tausayin MAJEED din sbd abubuwan sun Masa yawa gashi wannan Yar banzar na Neman qara zafafa Masa kai da haukarta.

Cikin gatse tace”

Hajiya saiki dawo MAJEED din yayi tafiya yace
Saiki dawo kici gaba da kuka tunda Baki aura Dan rayuwar dakike burin samun aureba.

Maganar umma na cewan abbin yayi tafiya yasa hankalinta sake tashi saidai Bata nunaba sbd umman karta cigaba da Mata wannan fadan na baqar magana Dan haka ta juya jiki mace Takoma dakinta.

Tana shiga daki ta zauna tareda daukan wayarta Kai tsaye tasaka kiransa tana sake Shiga damuwa Mai tsanani,

Abbinta akaron farko dasuka kwana suka wuni basuyi wayaba basuyi maganar arzikiba,
Yanzu Kuma yayi tafiya batama saniba hakama umma yaganah kawai ya fadawa.

Hawaye taji idanuwanta na cikowa dasu indai kuwa akan Abdulsamad Abbinta zaiyi irin wannan fushin da ita Zata hakura dashi…
Tama hakura dashi
Zata bawa Abbi hakuri bazata sake ko maganar Abdul dinba barema ummansa.

Kiran wayarsa tahau yi Amma takasa samu Dan haka taji kaman wani zazzabin na neman kamata Dan haka ta silala tayo wanka ta shirya cikin doguwar Riga breakfast dinma Dan Dole ta fito taci tana qarfafawa kanta sbd Abbi yadawo anjima ya taddata ta sake zaifi saurin yafe Mata sbd fushin Abbi shine abinda Bata taba dauka da wasaba.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107[11/3, 10:19 AM] It’s Queen Meenali????: 37
Arewabooks@Mamuhgee
Sukuku ta wuni ranar zuciyarta ba Dadi hakama umma har lokacin ta fuske Mata ga Neesah nata shirye shiryen tafiyarta ga abbin sai Kira takeyi takasa samunsa duk saitaji kaman tayita rusa kuka
Gashi umma na fushi ko tayi kukan tasan ba rarrashinta umman zataiba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button