INAYAH 31-40

Har qarfe biyar na yamma tana jiran dawowar abbin sbd Bata tunanin tafiyarsa Mai nisace kokuma kwana bare barin qasa dazai tafi Bata saniba tana matsayin ‘yarsa daya tal……
Shiru tayi daga wannan tunanin sbd tunowa da auren da har lokacin Batajin ta sauko ta karba auren,
Ta hakura da Dr Abdul sbd kaucewa fushin abbin Amma ita maganar aurenta dashi batajin Zata taba karban wannan.
Ganin zaman Yana neman Cinna Mata hauka yasa ta fito Palo tana kokarin nufar hanyar dakin umma yaganah saiga qarar akwai baqi a kofa.
Duk da tasan ba Abbi bane Amma sbd tana buqatan ganinsa yasa taje da sauri ta bude tana adduar Allah yasa shi dinne.
Anty Hafsat tagani da CM da sauri ta rungume anty Hafsat tana Jin hawaye na ciko idonta kawai sbd Daman tana neman Wanda Zata fadawa kukanta.
Cikin kulawa Anty Hafsat ta dago bayan ta zare jikinta tace”
Muna tareda baqi Inayah behave yourself idan mun nutsu mayi magana.
Fuskarta still da sauran hawaye ta juyo ta kalli baqin.
CM tafara kallo cikin nutsuwa tace”
Daddy Ina wuni?
Murmushi yayi cikin kulawa shima yace”
Lfy kalau Inayah,
Yaya umma yaganah?
Ki gaidata idan Kun shiga bazan tsayaba sauri nake saidai idan nadawo.
Anty Hafsat ya kalla yace”
zanje na dauko Alhaji babbah sbd suma su Haj Hadizan suna hanyar qarasowa nan din kafin su iso akai su hajiya suyi sallah su huta sun biyo hanya.
Juyawa yayi ya kalli farar dattijuwar dake tsaye gefe cikin ash Australian lace da lafaya baqa a nade da ita yace”
Hajiya ku qarasa Bara na dauko Alhaji idan kafin Ku huta.
Gyada Masa Kai kawai tayi ahankali tareda maida kallonta kan Inayah data kasa daukewa Ido.
Cikin nutsuwa Inayah ta kalli matar wadda itama tsura Mata Ido yayi sosai sbd haskenta sosai da Kuma ganin kamanninta sosai da Abbinta Dan kuwa kusan Tama fisa kyau sbd tana mace saidai kawai manyancin datai sosai.
A natse cikin kasa boye mamakinta sosai tace”
Ina wuni?
sannu da zuwa.
Sam hajiyar Bata amsaba Wanda ita Inayah Sam Bata luraba juyawa tayi Takoma ciki tana sake saka Kiran Abbi a wayarta.
Cak hajiyar tayi agurin taqi saka kafarta a palon.
‘yarta dake gefenta wadda a shekaru tafi anty Hafsat shekaru sosai ta kalli hajiyar zuciyarta na quna kaman yanda ta hajiyar ke quna Kai tsaye ta bude Baki ba boye boye tace”
Hajiya inaga mu koma gida kowai kokuma kokuma muje gidan Alhaji babbahn shida kikazo sbd alfarmar daya nema ta zuwan naki.
Batareda hajiyar tace komaiba kuwa suka juya
Anty Hafsat ta juyo da sauri tareda binsu a rikice tana bawa hajiyar hakurin su dawo.
Hajiyar tafiyar kawai takeyi Amma zuciyarta a rufe take….
Ciwon hawan jininta Dana zuciya daf yake da tashi sbd dacin da zuciyarta ke dauka..
Kasa jurewa tayi ta tsaya cak tana Dan dafe kirjinta.
Da sauri anty Hafsat da ‘yar tata wadda anty Hafsat takira da Anty juwairiyyah suka riqota suna Kiran sunanta da cikin kulawa.
Ganin tana neman faduwa agurin yasa ba yanda anty juwairiyyah ta iya suka Jata suka koma cikin gidan.
Umma yaganah data fito palon Jin ance sunyi baqi Bata ga kowaba tana Shirin juyawa suka shigo da hajiyar a rirriqe.
Da sauri cikin kulawa tace”
Subhanallh,
Hafsat baqin namune ba lafiya?
Bari Akira Dr farhat da sauri kafin Nan Bari Neesah ta fara dubata.
Ciki umman tayi takira Neesah saidai Ashe Neesah din ta fita Dole sai dr farhat suka kira da gaggawa.
Agurin wayar anty Hafsat tace”
Umma yaganah ki sanar da ita umman AA MAJEED ce da kanta da Allah ta iso da wuri……..
Wuta umma yaganah ta dauke tareda bude dukkanin idonta tana kallon hajiya.
Sai alokacin taga zallar kamannin MAJEED atareda hajiyar dan haka take jikinta Dana Inayah data fito lokacin mutuwa sbd tsananin farin ciki.
Umma na aje wayar kuwa ta kalli anty Hafsat tace”
Mahaifiyar MAJEED ce kikace?
Eh umma itace.
Maida kallonsu kan hajiya sukai itada Inayah lokaci daya fuskar Inayah daukeda farin ciki Batasan lokacinda ta furta”
Yau Naga daya da cikin kakannina kenan…
Ashe munada dangi muma,
Abbi na ummansa na raye..
Da sauri umma yaganah ta Dan kwabeta kada ta sauka layi
Cikin sakin fuska da bayyanan farin ciki tafara yimusu sabuwar sannu da zuwa tana miqewa Anty juwairiyyah ruwan roba da aka kawo Mara sanyi tace”
Bata Tasha Zata Dan ji dama Dama kafin Dr farhat din tazo.
Daga hajiyar har anti juwairiyyah Babu wanda ya iya magana har lokacin sbd Babu Wanda zuciyarsa Bata cikin dacin rai na shigowa gidan.
Ganin yanayinsu yasa umma datake Babba ta fahimci akwai damuwa Dan haka tace Inayah tayi ciki har hajiyar ta samu nutsuwa tukunna.
Babban dakin bakinsu dake gefen na umma yaganah aka gyara take duk da Baya buqatan wani gyaran sbd komai na dakin fes yake Kuma Babbane da toilet.
Dubari su Anty Hafsat suka ringa yiwa hajiyar ana mata firfita duk da sanyin AC sbd asamu Dr farhat ta iso.
Dr farhat na isowa aka Kama hajiyar aka Kai dakin da aka Gama gyara musu sanyin AC da qamshi sai tashi yakeyi.
Ba wata matsalar bace kawai jinintane ya hau take.
Maganinta da batazo dashiba shi Dr farhat tasa aka kawo suka Bata
Cikin Yan mintuna kuwa sai gashi tadan samu tafara dawowa daidai.
Fita akai aka bawa hajiyar da Anty juwairiyyah guri su but suyi sallah da sauransu tukuna.
Bayan fitarsu ganin yanayin hajiyar yasa Anty juwairiyyah data Gama cika da baqin ciki aranta tun na shekarun Dana yanzu datake gani gabanta yasa bataiwa hajiyar maganar komaiba ta nufi toilet tashiga Dan yin alwala.
Hajiyarma saita huta Zata iya sallar sbd tanajin jiri har lokacin da bugawar zuciya da sauri Dan haka rufe idanuwa tayi daga kwancen tanajin zuciyarta na karye fiyeda shekarun data debo bada ABDULMAJEED dintaba sbd Bata saniba Ashe Yana Nan ya Gina sabuwar rayuwa da sabuwar uwa…Jin tayi hawaye na taruwa acikin idonta Amma kaman koyaushe Bata barin su gangaro sbd zubda hawayen uwa akan danta matuqar bana farin cikiba babbar masiface ga ‘da.
Inayah kuwa cikin farin ciki take Neman wayar abbin Amma still Bata samuba sai taji murnarta ta Kai sbd duk Wanda Zata samu a rayuwarta matuqar Bata daidai da Abbinta Bata cikin farin ciki da nutsuwa Dan haka take murnar ta sace Mata ta zauna daki tareda zubawa wayarta Ido.
Umma yaganah kuwa hidima tashiga kitchen da kanta tafara yiwa su hajiyar MAJEED din sbd tasan matsayinsu sun wuce abar ‘yan aiki da hidimarsu Dan haka tahau aikin abinci Lafiyayye Mai lafiya.
Saida akai Kiran magriba aka Gama komai aka kwasa a jere da kuloli aka Kai dakinsu har lokacin daga hajiyar har Anty juwairiyyah Babu Wanda ya saki fuska ko nuna sakewa Amma hajiyar taji sauki tana zaune tana waya a sanyaye da babbar yarta.
Umma yaganah Bata damu da rashin sakewarsuba bil haqqi take musu hidima tana sake bayyanar musu da mahimmanci dasuke dashi Mai girma a gidan duk da yau suka fara zuwa.
Acan Kuma Inayah nason magana da anty Hafsat Amma anty Hafsat din ta hana sbd Dr farhat na gidan Bata wuceba Kuma Batasan da MAJEED aka daura aurenba a qataice bakowane yasan meye dalilin fasa auren Inayah da Dr Abdul ba hakama bakowa yasan da waye aka daura aurenba sbd duk har lokacin a uban Inayah suka Sansa.
Dr farhat na tafiya saiga su Alhaji babbah sun iso daidai tareda motarsu umma Hadiza da ‘yan uwanta.
Dunguma sukai suka shigo ciki gabaki daya babban palonsu umma yaganah.