INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 56-60

56
Arewabooks@Mamuhgee
Umma yaganah kinfi kowa sanin halinta da tarbiyarta tunda sbd ke ne kika riqeta…

Haj umma please for God sake haryanzu Inayah yarinyace ki Dena biyewa wautanta haryanzu kaman babyna c….
Umn I mean she’s too young for all ths manya manyan maganganun..”””

Haj umma kasama cewa komai tayi Dan Kuma ai kaman Al’amarin yafi qarfinta tun bayan barin Inayah gurin takasa dauke idonta akan hanyar databi shiyasa ma maganganunsa ba duka ta fahimtaba Dan tashiga tunani Kuma.

Umma yaganah Kam sanyi jikinta yayi duk da Daman Bata taba kawo wani banzan tunani ko zargin komaiba akan Inayah Dan MAJEED dinne kawai zai nuna Mata sanin Inayah Amma kome zaa fada ko akawo Mata tasan Inayah bazata taba aikata wani banzan abuba bare kawo tunanin ta kwana wani gurin,

Dama tunda ta sanarda Haj umman Bata gantaba hajiyar ta ringa fada tana masifa tareda fadan maganganu marasa Dadi akan Inayar shine fa tafara Kiran MAJEED din a waya Dan ta sanar Masa komai yasan matakin dauka tun kafin ‘yar tagama lalacewa ya miqawa uwarta ita tunda so take abata ‘yar saiga wannan sabuwar maganar.

Barin palon yayi Kai tsaye ya nufi dining room sbd bawani lokacin zai bataba yanada gurin zuwa.

Yana Zama Haj umma ta iso itama ta zauna tana kallonsa fuskarta ba walwala ko kadan magana zatai dashi.

Umma yaganah Kam Bayan Inayah tabi dakinta
Tana shiga ta tadda Inayah din na shiryawa hankali kwance sai Qamshin khumrahs masu Dadi da Black opium dinta ke tashi.

Kallonta umma yaganah takeyi dakyau tace”

Inayah kinsan idan Baki nutsu kin Dena wannan shashancinba Zan Dena biye Miki,

Meyesa Zaki tsaya gaban mahaifiyar ABDULMAJEED kice Mata a dakinsa kika kwana?

Kallon umman ta juyo tayi a sanyaye tace”

Umma yaganah kiyi hakuri bafa Karya nakeyiba wlh acan na…..

Kinga banson ji amma ko can kika kwana be kamata ki kalleta ki fada Mata hakanba
Shi kansa MAJEED din kunya kike sakasa agaban mahaifiyarsa.

Shiru tayi umma yaganah tayita yimata fada kafin tadawo nasiha da rarrashi.

Hakuri Inayah ta Bata kaman yanda tasaba duk qanqantar lefi Bata Jin gazawa ko nauyin cewa ayi hakuri.

Cikin fluid Palazzo black da milk Waverly wrap top ta shirya sai scarf da qaramin veil data nado akanta suka fito tareda umman fes da ita fuskarta ba kwalliya Amma lip balm dintanda eyeliner dinda shine abinda yake qarawa kyakkyawar farar fuskarta kyau koyaushe.

Sun shigowa dining room din akanta idanuwansa suka fara sauka
Itama kusan akansa idonta ya sauka din.

Murmushi tasake Wanda yasashi dauke Kai ahankali yana Dan gyara maqoshinsa dayaji Yana bushewa take..

Haj umma kallonta tayi tana Dan Kama kanta Dan maganarta datayi da majeed din akan Inayah dataga kaman Babu abinda yake ganewa idan akan lefin Inayah ne,

Tarasa masifar datafi Inayah a rayuwarta sbd akanta ‘danta ya zabi yabarta shekarun baya Kuma ko yanzu idanba bude Masa Ido yayi akan munafurcin maceba zai sake rufewa ne.

Zama INAYAH tayi gefen Abbin tana satar kallonsa
Shikuma gabaki daya indanuwansa nakan wayarsa dayake duba Sako saidai kusan hankalinsa baya kan wayar yanajin qamshinta na shiga hancinsa Wanda ya talasta Masa ajiye wayar gefe tareda juyowa ya kalleta da idanuwansa dasuka sata Jin tsikar jikinta tashi saidai takasa iya juyowa ta hada idon dashi sai kawai ta maida hankali kan serving dinsa tanajin idanuwansa akanta Wanda shikuma idanuwan Haj umma na kansa tana kallon ikon Allah dayafi karfin bawa.

Har aka Gama cin abincin yau Babu Wanda yayi magana sai Inayah data bude Baki tabawa Haj umma hakurin abinda yafaru dazu cikin sanyi da son hajiyar ta hakuri.

Shiru hajiyar tayi taqi amsawa…

Aje spoon dinsa yayi tareda miqewa tsaye can qasan maqoshi yace musu saiya dawo.

Yanayinsa kobai fadaba yasa Haj umma jikinta yasake sanyi da Al’amarin Dan kuwa tasan zuciyarsa ta sosu ne da shirun dataiwa Inayah.

Inayah ma miqewa tayi ba damuwa a fuskarta tace”

Umma yaganah na tafi Abbina zanbi ya ajiyeni,
Haj umma bye…

Handbag dinta ta sauka tareda wayarta tabi bayansa.

Ko data fito harabar gidan motar data gani setin kofa tasan shine zaiyi tuqin da kansa Dan duk aka fiddota to shine zaiyi driving da kansa Dan haka ta nufo motar Kai tsaye ta shiga gaba.

Zaune yake cikin motar da alama ita yake jira kenan ko Bata ambataba Abbinta yayi niyar kaita aikin da kansa.

Tada motar yayi tareda juyowa ya kalleta
Ya maida idanuwansa ya zuwa shigar jikinta Yana kalla….

Ahankali yace”

Ina coat naki?

Gefenta ta nuna Masa tana cewa”

Gashinan tareda handbag Dina.

Motan yaja suka fice Yana maida hankalinsa kan driving dayakeyi saidai qamshinta na neman rarraba hankalinsa Wanda ya rasa meyasa hancinsa yake daukan qamshinta komai kankantarsa tun ba yanzuba.

Suna Isa asibitin ya ajiyeta tareda kallonta yayi Mata ta kula yaja motar ya wuce itama ta shige akan idon umma Hadiza data Kira umma yaganah tace Mata Inayah din na hanyar zuwa aiki.

Inayah Bata qarasa shigaba Hadiza ta iso gurinta tana kallonta cikin kulawa ta Kira sunanta.

Inayah na ganinta ta sake murmushi tana cewa”

Good morning.

Dariya Hadiza tayi tana kallon yanda farin ciki ke kwance kan fuskar Inayah din tace”

Yaya jikin?
Harkin warke wannan farin cikin na fuskarki fa?
Nasan bazai wuce na Abbinki Daya kawoki bane.

Kallon Hadizan tayi tareda sakin murmushin Daya qarawa fuskarta kyau tace”

Harkin sanni haka da wuri?

Dadin maganar Hadiza taji ta riqo hannun Inayah din tana sake murmushin farin ciki tace”

Bakida wuyar fahimta Ayshatouh sbd bakida wahalalliyar zuciya da rayuwa halin mahaifinki kika dauko baida damuwa ko kadan duk yanda rayuwa tazo Masa karba yakeyi hannu babbiyu…

Sanyi jikin Inayah yayi ta zame hannunta ahankali tana cewa”

Allah yaji qansa”

Amma zuciyarta har lokacin batajin Hadizan da mahaifinta data ambata kaman yanda takejin Abbi daya cike gurbindaya kamata su zauna a zuciyarta duk da ko ahakan yanzu tanajin kaunar Hadiza aranta.

Bata shigaba daganan ta juya tabar Inayah itama Takoma gida.

Inayah ma shigewa tayi tana waya da Neesah datake kiranta suna maganar wani abun dabam.

Sai yamma tadawo gida a Dan gajiye Kuma Hadiza ce tadawo da ita gida batai Mata tayin shigowaba sbd haryanzu Abbinta baice komaiba akanta da Hadizan itama Hadizan Bata damu da shigarba sbd tanason bashi lokaci da kansa ya sauko ya Bata Daman kasancewa da yarta aduk lokacinda taso hakan.

Tana shigowa ta taradda Dr farhat a gidan Bata wani damuba sbd Abbinta yace Mata ba auren zeyiba Dan haka Babu abinda ya shafeta da Dr farhat.

Fuska ba laifi ta tsaya ta gaidata tunda sosai ta girmeta ba kusaba.

Haj umma ta kalla itama cikin girmamawa ta gaidata kafin ta qarasa gurin umma yaganarta ta Dan rungumeta tareda Mata sannu da gida ta wucewarta zuwa bedroom dinta.

Wanka tafara Yi ta sanya gajeran wando Mai Fadi blue da light vest ta fito bayan tayi sallar la’asar ta nufi kitchen gurinsu zubbi tasa Salimat ta dafa Mata noodles da kwai taci acan suna Dan Mata fira tana dariya sbd tanajin dadin firarsu
Suma sunajin dadinta sbd ba ruwanta acikinsu sakewa take tana dariya idan suna Mata fira da labari masu ban dariya.

Sai gab da magriba ta fito kitchen din sbd ta Dan saka hannu a aikin tace Zata fara koyan girki sosai sbd Abbinta tanason Nan gaba itace zatana Masa abinci.

1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button