61
Arewabooks@Mamuhgee
Bedroom din Dr iklimat takoma ta qarasa gefen Hadiza dake zaune kan kujera ta zauna tana kokarin boye sanyin jikinta na rabuwa da Abbin sbd bude Mata idon da zasu iyayi da fada tunda since karta nuna ala Dole Jan aji zasu koya Mata basusan Batasan wannan ba idan akan Abbinta ne.
Dr iklimat ce ta shigo daga baya itama daukeda ruwan kankana da Madara ta miqa Mata tana Zama bakin gado fuska asake tace”
Hadiza lallai wannan sirikin namu yafimu idon yawon duniya.
Murmushi Hadizan tayi tana kallon Inayah dake kurba drink din ahankali tanajin tsikar jikinta na tashi da abubuwan dasuketa Bata tun Rana tana Sha.
Hanata tunani sukai da zantukansu na sabbin abubuwan dasuke koya Mata Wanda suka shafi hanata maganganu da yawan sangartarta.
Sosai suka dage cikin dubara da lallabawa suka koyar da ita wasu abubuwan data rasa daga rashin Zama da mahaifiya.
Sai dare sosai suka kwanta bayan tayita ganin sakon Abbi na tambayarta
ta kwanta?
Tayi bacci?
Is she ok?
Zata iya kwana a Nan ko yadawo ya dauketa?
Wainnan sakonnin nasane sukaita shigowa tana gani ta kasa replying nasa ko so daya sbd jikinta dayake amatuqar mace da abubuwan datasha dakuma farin cikin kwana gado Daya da mahaifiyarta.
Dan kusan ma akan cinyarta tafara bacci sai daga baya ta kwana kan gado tana Jin ranta fes duk da Kuma kewar Abbinta na cinta Amma Kuma shima yawan text din nasa yasata Jin sanyi aranta Dan tasan yakasa baccine Yana tunanin ko Yaya Zata iya bacci anan.
Washe gari tana tashi Kiran abbinta ne yafara shigowa wayarta a kasalance ta dauka tana shagwaba murya tace”
Aslm alkm, Good morning my Abbi.
Ajiyar zuciya da numfashi yafara saukewa a boye kafin cikin nutsuwa da kulawa yace”
Kintashi lfy?
Lfy kalau Abbi kewanka kawai nakeyi….
Ahankali yace”
Kinyi bacci kuwa?
Tashi zaune tayi tana cewa”
Yes Abbi,
Abbi kayi missing nawa?
Kayi bacci?
Wani boyayyan numfashi ya sauke Mara sauti ahankali sbd gabaki daya zuciyarsa Bata samu nutsuwar dazai iya ko kwantawaba bare baccin
Zaune yaga asuba kan kujera Yana jiran reply dinta Amma shiru shiyasa Kai tsaye yakira da safen.
Yes” kawai yace Mata a taqaice Yana cewa”
Ki shirya in time zamu wuce zuwa 2:30 Amma kafin can zamu tafi gidan juwairiyyah da safiyyah.
Ok Abbi.
Sallama sukai ya ajiye wayar tareda rufe idanuwansa dasukai nauyi Yana Dan dafe kansa.
Tashi yayi tareda kashe wayarsa gabaki daya ya nufi gado ya hau a natse ya kwanta sbd yanzu zai iya samu ya Dan Yi baccin kafin anjima.
Acan gidan Dr iklimat kuwa su umma Hadiza wasu mayun turaruka masu shegiyar tsada da mayen qamshi suka siya gurin wata qawar Hadizan Dake Nan Abuja tun daren jiyan sukai Mata waya sai gashi da safen driver yakawo.
Harhada Mata su sukai tareda wasu sabbin fitinannun kayan baccin da Dr iklimat ta fita da kanta ta siyo Mata shima a gurin neighbor dinta me Saro designers daga waje.
Sam Inayah Bata saka mini skirts sbd batadasu a kayanta Amma hardasu suka siyo Mata.
Qarfe daya tagama shiryawa suka zauna jiran zuwan Abbi.
Lafewa tayi jikin mahaifiyarta tanajin kaunarta sbd kwana dayan Nan dasukai duk sun sake saka Mata kaunarsu da Jin dadin dawowarsu rayuwarta gashi suma sunata lallabata kaman yanda Abbinta ya sabar Mata duk da suna Mata fadan wani abin Amma akwai kaunarta sosai ataredasu.
Qarfe daya da rabi ya iso gidan Bai shigoba saidai suka fito.
Fitowa yayi motar suka gaisa dasu a mutunce Yana kallon gefen datake a fisge sbd ganin kaman tasauya Masa sbd harda skin scrubbing sukai mata.
Itama shi take kallo zuciyarta na cika da son kayanta suna hada Ido ta shagwabar da fuska tana sakin murmushin farin cikin ganinsa.
Ahankali Yana Mata wani mayen kallo yace”
Muje ko?
Jikin umma Hadiza ta qarasa ta rungumeta tana cewa”
Kidawo da wuri kema.
Murmushi kawai tayi Tana cewa”
Allah yakaiku lfy Ina gaida su umma yaganah da Haj.
Dr iklimat ta runguma itama tana cewa”
Mommy kince zakizo
Ki cika alqawari kinji?
Gyada Mata Kai tayi tana cewa”
Zanzo Inshallah ki gaida mutan gidan
Allah ya tsare,
Kuma kindai ji abinda na fada Miki.
Gyada Kai tayi tana cewa”
Yes Mommy.
Mota ta juya ta nufa Dan already Yana ciki Yana kallonta da idanuwansa dasuka kasa daukuwa daga kanta.
Tana shiga motar driver yaja suka wuce.
Bai juyoba sbd yawan kallonta matsala ne agurinsa Dan haka ya Dan maida hankalinsa kan waya Yana son Kiran safiyyah dasu juwairiyyah suna gidanta gabaki dayansu da Yara.
Bayan ta dauki wayar da qyar ya riqe kansa tareda kamewa ya sanar da ita suna hanya ya kashe sbd wani mayen Qamshin dayakeji Yana tashi daga jikinta ahankali Yana Shiga hancinsa Yana neman buga kansa.
Gashi taqi zuwa ta maqalesa kaman yanda ta saba tana zaune itama tana duba sakon Neesah data turo Mata ta WhatsApp.
Hankalinta na kan Abbin nata tannuwanta da zuciyarta dasuka Saba zuwa garesa sai kokarin hanasu zuwan takeyi sbd fadan su umma Hadiza dake yawo cikin kanta na hanata zuwa koyaushe tabari yazo da kansa.
Daqyar kowannensu ya iya riqe kansa harsuka Isa gidan anty safiyyah suna fitowa motar su Anty juwairiyyah da ‘yayansu suka sake zuba idanuwansu kanta sbd Babu abinda yake jikinta Mara kyau da tsada tun daga kan kyakkyawar halittar da Allah yayi Mata har tsadaddiyar suturar jikinta da wasu matsiyatan designer handbag da takarmin Stuart W.
Babbar ‘yar anty juwairiyyah rumanah itace ta saki fuska sosai tareda rungume Inayah din tana cewa”
Uncle sannu da zuwa,
Welcome matan uncle.
Murmushi Inayah tayi tana amsawa ahankali.
Gaidasu anyu juwairiyyah tayi cikin girmamawa da sanyi.
Amsawa sukai anty safiyyah na qarewa Inayah kallo tana yaba kyanta da komaima dan itakam take Inayah Tai Mata Dan shekaran jiya Basu ganta dakyauta sbd dare ne yanzu Kam taganta Kuma wlh tafi Dr farhat komai ta fada a fili tana cewa”
Gskia Inayah is the perfect match wa MAJEED.
Haj umma Dan Allah ta Dena maganar wata macen Kuma.
Dadin maganar Inayah taji Amma Bata kalli Abbinba sukai ciki gabaki dayansu.
Abinci sukaci a babban dining din palon gidan sunata fira da ‘dan uwansu yaran Kuma sunatayi da Inayah wadda kusan hankalinta yafi kwanciya da yaran dasuka nuna Mata kauna sai Anty safiyyah Amma Kam anty juwairiyyah Dr farhat sukeyi wuta itada Haj umma.
Sosai anty safiyyah ta sauke kanta tabawa ‘dan uwanta hakurin abinda ya faru baya
Bayason tada komai Dan haka ya dakatar da maganar yace abarta ya wuce kawai.
Karfe biyu Saura suka baro gidan bayan yayiwa yaran dasu kansu uwayen yaran kyautar girma Data sake sasu jinjinawa MAJEED din sukaita godiya da Jin Dadi suka rakosu suka wuce.
Kusan late suka Isa airport Dan hakan suna Isa ba Bata lokaci suka tashi.
Ko a jirgi dai Babu wata doguwar Hira data shiga tsakaninsu sai mayen kallo dayake binta dashi Yana Jin sabon yanayi akanta.
Itama yau jinsa take cikin ran nata sosai sbd tunda suka hadu ko hannunsu be haduba Dan haka takejin kaman zuciyarta Zata fashe da sonsa.
Charles ne yazo daukansu airport da Daya daga cikin lafiyayyun motocin gidan.
Saida suka kamo hanyar gida ya kasa hakuri ya juyo ahankali ya kalleta tareda kamo hannunta dake kan cinyarta ajiye tana kallonsa.
Kama hannun nata da yayi kusan atare kowannensu ya saki ajiyar zuciya a boye.
Cikin idonta ya kalli tareda bude Baki ahankali yace”