BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 64

Chapter: 64 Share:
Report
BABU SO View: 167 Words: 2K
Chapter 64 64
……..Dariya take tana masa gwallo. Fuska ya

ɓata, da harɗe hannayensa a ƙirji irin yayi
fushin nan. Yanda yay ɗin sai ya saka Anaam
shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin.
“Kai Yaya shagwaɓa kuma?! ALLAH kamafi
ƙyau a haka fuskanka so cute”. Ta ƙare
maganar da kashe masa ido dariyarta mai
ƙaramin sauti na bayyana fararen haƙoranta.
Ta nuna lips ɗinta da kaɗa masa idanunta
dake cikin gilashi.
“Indai lipstick ɗin nan ne Yaya ba shansa
zakai ba garama ka haƙura”.
“Oh oh haba princess kiji tausayina mana”.
Yaya maganar da matsar da fuskarsa gab da
tata.
Baya taja dasa hanunta ta kare bakinta,
“Babu wani princess na daɗin baki fa Yaya,
barima kaga na shanye abuna, idan baka
ganiba ai dole ka haƙura”.
Yana ƙoƙarin riƙota ta tura lips ɗinta cikin
baki da sauri.. Idanunsa ya waro sosai yana
kallonta cikin langaɓe wuya. Ta fito da lips ɗin
tana dariya da masa gwalo. “Sai kaci abinci yanzu babu”.
“Ni ko? Yarinya zan rama ne”.
Dariyarta ta cigaba dayi ƙasa-ƙasa, shiko ya
ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin aincinsa
fuskarsa da ɗan murmushi.
“Nifa yaya karka cinye min abinci na”.
Idanunsa ya ɗago yana kallonta, sai kuma ya

ɗibo abinci ya nufi bakinta, “Ba marowaci bane irinki ai hahh”.
Bakin ta buɗe ba musu ya zuba mata, a
hankali ta shiga taunawa da faɗin, “Nima ai
bana rowa”.
“Kika min yanzun?”.
“Baga abincina kana ci ba”.
Murmushi kawai yayi batare da yace komai
ba. Itama bata sake magana ba, ya cigaba da bata abincin shima yana ci. Suna gab da kammalawa wayarsa tai ring, ɗauka yay ya duba, ganin Khaleel sai kawai ya ɗaga. Bata san mi’akace masa a wayarba, sai gani tai ya miƙe da kama hanunta….
Da mamaki take kallonsa zatai magana ya girgiza mata kansa. Baki ta ɗan tura dan ita dai bata ƙoshi da abincin ba, sai dai babu yanda zatai dole ta bisa. Hango Khaleel jikin wata mota mai ƙyau fara tas jingine ya sata zare hanunta cikin nasa, bai ce komai ba har suka ƙaraso. Ita ta fara gaida Khaleel ɗin, ya amsa mata fuska da murmushi sannan ya maida hankalinsa ga Yayansa. Gaisheshi yay
da girmamawa. Ya amsa masa da kulawa. “Daga ina haka mazan fama?”.
Murmushin Khaleel ya faɗaɗa dan yana son Yayan nasa ya kirasa da sunan nan. Wani ɗan ƙaramin gi! ya ɗakko a gaban motar, ya dubi Anaam dake kallon motar da ita kanta an

naɗeta da zaren gi!. Sai kuma ya sake maida kallonsa ga Share” ɗin da shima dai motar yake kallo. “Saƙone daga Abie. Abawa Granny”.
Idanu ta waro matuƙa da kai hannunta duk biyu saman bakinta, sai kuma ta dubi Share” da shima murmushi ke shimfiɗe akan fuskarsa. Shine ya amsa ya buɗe key na mota ya bayyana. Ai batama san sanda ta rungume Share” da faɗin, “Wayyo Yaya daɗi zai kasheni”.
Rungumeta yay shina da sakin dariya kamar yanda Khaleel shina ke dariyar. Ɗagowa tai ta amsa key ɗin tana kallo, sai kuma ta ɗagasa a saitin fuskar Share” tana kaɗa masa. Murmushi ya sake saki mai faɗi da faɗin, “ALLAH ya sakama Abie da alkairi Congratulations dear”.
Da amin ta amsa, Khaleel ma ya amsa da
kallonta. “Congratulations Granny. Saura
kuma tukuyci na, k ko Yaya wazai bani?”. “Karka damu Yaya Khaleel, saika zaɓa”. Ta
bashi amsa da shigewa motar da Share” ya buɗe mata, daidai nan Fadwa ta fito hakama Aysha. A tare suka ƙaraso wajen, Fadwa da gaba ɗaya ranta ke’a jagule tun maganganun da Share” ya yaɓa mata ta dubi Khaleel fuska a tsuke. Kafinma tai magana ya nuna musu

motar ita da Aysha yana murmushi. “Ƙyautace daga Abie aka kawoma Anaam”.
“Woow!!” Aysha ta faɗa cikin zaro ido da
shafa motar tana kallo, Fadwa kam mutuwar
tsaye tai. Dai-dai nan Share” da Anaam dake
cikin motar suka fito kowanne fuskarsa har
yanzu da murmushi. Khaleel ya miƙa mata
hannu, “Nifa a tafamin tukuycina”. Kafin tace komai Share” dake danna
wayarsa ya miƙa masa, saka details ɗinka”. “Woow da kyau babban yaya da gudu kuwa”. Yanda Yay ɗin ya saka Anaam da Aysha
kwashewa da dariya. Shigar saƙo a wayarsa yasa bai tankasu ba, ya buɗe da sauri, “What!”. Ya faɗa yana ɗago kai da sauri ya kalli Share”. “Yaya duk tukuyci?”.
Murmushi Share” yay da kallon Anaam,
“Idan tace a ƙara maka ma sai a ƙara maka
ai”. A salon da yay maganar da ɗage mata gira
ya sakata rufe fuskarta da dukkan tafin
hanunta dan taji kunya. Matsota yay tare da
ranƙwafawa saitin kunenta. “Nima ina jiran
nawa tukuycin yanzun nan, inba hakaba a
gaban Khaleel zanyi…..”
Da sauri ta buɗe idanunta… “Kayi mi?”.
Maimakon amsa sai ya nuna mata lips ɗinsa cikin kashe ido. Sarai tasan zaiyi ɗin, amma sai ta kauda ido da nufin cewa a’a. Akan Fadwa da sam bata san da wanzuwarta a

wajen ba ta saukesu. Sukaima juna kallon ido cikin ido, ita ta fara kauda idonta da sakin wani tattausan murmushi mai ma’anoni da yawa ta maido dubanta ga Share”. Murmushi ta sakar masa shima ta ɗan saci kallon Aysha dake a mota hankalinta baya kansu, ta maida ga Khaleel, ganin shi ɗin dai zaiga komai sai ta ɗanyi jimm na tunani. “Yaya Khaleel kalla can”. Ta faɗa da sauri tana mai ɗane Share” a bazata ta manne tausasan lips ɗinta kan nasa lips ɗin.
Numfashinsa neman shiɗewa yay saboda
rashin zaton hakan daga gareta. Baya ta nema
janyewa ya ƙara cafkesu da saka hannu biyu
saman ƙugunta ta zuba masa mintsini a gefen
ciki da janye jikinta kunya kamar ta nutse.. Khaleel daya waiga baiga komai ba ya juyo
da nufin hararar Anaam, ai babu shiri ya sake
maida kansa gefe da sauri yana dafe bakinsa
da sakin siririyar dariya. Aysha da bata san
mike faruwa ba ta fito a motar tana rungume
Anaam da faɗin, “Wayyo blood motar nan ta
haɗu wlhy ALLAH yasa a kashe da kai”. Wani
bahagon tari ya sarƙe Fadwa, cikin sassarfa
kamar zata kife ƙasa dan sauri tabar wajen
hawaye masu azabar zafi na kufce mata. Gaba ɗayansu kallonsu suka maida gareta,
dan sai yanzu ma shi Share” yasan Fadwar

na’a wajen. Cike da son basarwa itakam Anaam ta rungume Ayshar. “Thanks you blood, thanks you”. Shima dai gogan ya basar a binsa kamar komai bai faru ba, ya nunama Khaleel hanya alamar su shiga ciki idonsa akan Anaam. Anyi sa’a itama ta ɗago suka haɗa ido. Baki ta ɗan murguɗa masa. Ya taune lips dinsa da sakin murmushi alamar azakizo hannu. Kafaɗa ta ɗage masa da labe baki irin na i don’t care taja hanun Aysha suka koma motar…
Da ƙyar Fadwa ta iya kai kanta sashenta
saboda jiri dake ɗibarta da lulluɓe ganinta
gaba ɗaya. “Subahanalillhi. Hajiya lafiya?”. Mmn Abu ta faɗa da nufo Fadwa da sauri
dake neman zubewa ta tareta. Kuka ta sakar mata kamar wata karamar yarinya, maman Abu duk sai ta rikice. Kamata tai har bedroom. Tana son tambayarta mike faruwa tana jin tsoro, dole ta fito ta barta cikin damuwa. Tadai san labarin kitse baya wuce ƙoƙi dan ta jima da fahimtar Fadwa na cikin jerin mata masu tsananin kishi. Gata da hali irin na ɓoye abu a rai da idan bakai dogon nazari akanta ba saika ɗauka kishiya cutarta take musamman irin Anaam da bata iya ɓoye abinda ke ranta. “ALLAH ya ƙyauta”. Ta faɗa

da komawa kitchen ta cigaba da aikinta…..
Anaam kam da tuni sun koma ciki tana can cikin farin ciki tana waya da Mamie da Abie ta video call. Addu’a take zubama iyayen nata harda hawaye, yayinda suma suke kallonta murmushi shimfiɗe a fuskokinsu da tsananin ƙaunarta da tausayinta harma da alfahari da ita na kai mutuncinta gidan aurenta. Dan aunty mimi ta sanarma Mamie komai, hakama Mamie ta sanarma Abie, shiyyasa ya danƙara mata mota najin alfahari da ita akan riƙe tarbiyyar da sukai mata. Sai dai su kansu sun san sun kaita wani filin gwagwarmayar rayuwane na yankin kaddararta, amma sukanji sassauci da tunawa zumincin ALLAH suke son karfafawa insha ALLAHU sadaukarwarsu bazata taɓa zama a banza da wofi ba..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button