INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 56-60

Koda ta fito har lokacin Dr farhat Bata tafiba Haj umma tace tunda magrib tayi ta tsaya tayi sallah anan suyi dinner da ita tukuna.

Itama Bata wani musaba ta zauna din sbd tanason ganin MAJEED koba komai sbd gobe tafiya zatai zuwa Abuja daga can Kuma Zata koma Australia Amma duka daka bazata wuce wata dayaba zuwa biyu Zata dawo gida gaba daya tunda aurenta da MAJEED din yanata sake kankama.

Wanka Inayah tafara Yi kafin tayi sallar magriba ta zauna tana yiwa Abbi txt din be dawoba.

Tana tura sakon reply dinsa ya shigo Mata Ada alama wayar ba hannunsa sakon yashiga.

Murmushi tasake tana karanta abinda ya turo,

“Ina tareda cm”

Love you my Abbi” kawai ta tura Masa tareda ajiye wayar ta miqe ta nufi dakin umma yaganah.

A Palo ta taddasu har Haj umma da Dr farhat Dan haka gurin umma yaganah ta Isa ta zauna tareda kwantar da kanta a cinyarsa tana cewa”

Umma kaina na ciwo kadan..

Dan fara massaging kan tai tana cewa”

Rigimarkice datai yawa
Ki rage sai kan ya Dena ciwo akai akai.

Dr farhat ce ta saki murmushi cikin kulawa tace”

Gaskiyar umma ne Inayah kullum cikin daga hankalinsu Haj umma kike da umma da rigimarki kaman ba likita ba…

Dariya Mai kyau Inayah tayi tana cewa”

Babyn Abbinta ce fa Ni,
Idan na Dena Masa rigima waye zai masa?
Kullum Ni zanyi tayi Ni kadai,
Kuma haj umman ce take daga hankali akaina?….

Cikin raba Kai da wahala Haj umman itama tace”

Daman Kam bazan iya daga hankali akankiba na na Hana kaina bacci a banza,
Su dai dazasu iya suyita fama…

Amma Kam maganar rashin ji da kema kike sane kike gashinan kina cewa zakici gaba dayi,
Yana Tara qananun Yara Dole Zaki dawo hankalinki…..

Shigowarsa batasa Inayah fasa maganaba tace”

To ai Ni nayi Rigimar nawa ‘yayanma idan sunzo suyi tasu,
Mune zamuyita Masa rigima Yana rarrashinmu…..

Dangwale bakinta umma yaganah tayi tana hanata karasa fadar sauran maganar.

Yallaban kuwa yi yayi tamkar baiji abinda suke fadarba sbd zancen nasune dan ya lura Haj umma ita kesa Inayahn fadan wasu maganganun batareda taji nauyin fadarsuba.

Kallonsa Inayah tayi daga kwancen datake tareda sakar Masa murmushi tana cewa”

Abbi sannu da shigowa.

Kallonta yayi tareda amsawa cikin kulawa.

Su Haj umma ya gaidar shima tareda zaunawa a 2 seater Yana amsa gaisuwar Dr farhat batareda ya kalletaba sbd idanuwan Inayah dake kansa kaman ta taso ta rufe Masa Ido Dan kada ya kalla Dr farhat din Kuma yanajin idanuwan nata akansa.

Kasa Haj umma ce ta kallesa cikin kulawa da murmushi kan fuskarta tace”

Kaman gobe ne naji kace zakai tafiya Abuja right?
Dr farhat ma goben Abuja Zata acan gidan juwairiyyah Zata zauna munyi magana da juwairiyyahn kafin jibi tabi flight dinta na wucewa gaba daya…

Tunda kaima can din kayi inaga zaifi sauki ku wuce taren ka gaisa sosai da ‘yan uwanka daga can..

Washe Baki Dr farhat tayi cikin Jin dadin maganar tana kallon MAJEED din a natse.

Dan gyara murya yayi kadan kafin ya kalli Haj umman Kai tsaye yace”

Flight din yamma zanbi ba buqatan ta tsaya jiran tafiya Dani.

Miqewa yayi zai wuce ciki Umma yaganah tace”

Angama shirya dining bazaka tsaya kaciba kafin ka shige??

Sai alokacin ya juyo Yana kallon Inayah yace”

Ok.

Inayah yake kalla ta hade fuskarta sosai idanuwanta ma kokarin cikowa da hawaye suke.

INAYAH….”ya Kira sunanta a natse Wanda hakan yasa su Haj umma kallonta
Umma yaganah Kuma miqewa tayi ta nufi dining Dan qarasa duba abinda aka jera kafin kowa yazo.

Kasa dagowa tayi Saida yakuma Kiran sunanta cikin kulawa sbd yasan Zata iya rikicewa da rigima yanzu..

Dagowa tayi tareda miqewa tsaye batareda ta kalli kowaba ta nufi gurinsa ta tsaya gabansa ta dago ta kallesa da idanuwanta dasuke yagar zuciyarsa da dafinsu tace”

Abbi Nima zanje abujan kaga bantaba zuwaba.

Kallon Zaki kasheni yayi Mata ahankali kafin ya girgiza Mata Kai ahankali Yana cewa”

No,
Muje dinner is ready.

Wucewa yayi gaba ta tsaya zuciyarta na shiga damuwa da rigima saidai wlh batajin Zata yarda yaje ba da itama saidai yafasa tunda Dr farhat bazata iya hanata tafiyarba suje can su qarata a gidan anty juwairiyyah din Amma Abbinta tunda Zata iya hanasa tafiya Koda rigimarta bazata Bari yajeba saidai yaje da ita.

Haj umma ce ta kalleta tace”

Karki yarda naji kin tada rigima akan tafiyar Nan ki dagawa bawan Allah hankali a banza ko tausayinsa bakyaji sai anyi magana kice Abbinki ne ke Babynsa ce…..ba baby ba wlh ‘yar tsana.

Kallon Dr farhat tayi tace muje kici abinci kafin ki tafi farhat kinji.

Ajiyar zuciya Dr farhat ta ajiye kafin tace”

Haj umma inaga Bari kawai na tafi basai na tsaya cin abincinba zanje na qarasa shirina kafin kigama magana dashi akan tafiyar idan ya amince.

Ok shikenan Saida safen Inshallah Zan sake Masa magana yanzu.

Kallon Inayah Dr farhat tayi tace”

Bye Inayah.

Batareda ta nuna bacin Rai ko wani abunba itama ta juyo bayan tafara tafiya tace”

Allah ya tsare hanya Dr farhat.

Tana fadar hakan ta juya ta nufi dining room Haj umma na bayanta tana kallon kayan jikinta cikin takaici.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107
[11/10, 10:03 PM] +234 703 623 7917: 57
Arewabooks@Mamuhgee
Suna shigowa ya Dan dago ya kallesu
Ya tsaida kallonsa kan kayan jikinta da masuda wani kauri leggings ne black Daya kwanta a siraran cinyoyinta sai vest me Dan Fadi Bata kwanta ajikinta ba..

Dauke kansa yayi tareda maidawa kan abincin da umma yaganah tagama zuba Masa ya dauki spoon a natse yafara ci.

Itama gefensa ta qaraso ta zauna ta kallesa zatai magana ya dan lumshe fararen idanuwansa ya bude tareda girgiza Mata Kai yana cewa”

Kici abinci tukuna kafin magana daga baya.

Shiru tayi tareda gyara Zama tana zuba abincin.

Ganin yakusa Gama cin abincinsa ya tashi yasa Haj umma kallonsa tace”

MAJEED inason magana dakai zuwa anjima kafin kashige.

Ok Inshallah” yace Yana daukan lemon juice Mara sanyi sosai yasha kadan ya ajiye tareda daukan tissue ya goge bakinsa tareda miqewa Yana cewa alhmdllh.

Yana barin dining din ya fice daga gidan gabaki daya sbd akwai Inda zaije.

Yana barin gurin Haj umma tafara gamawa itama ta tashi tabar Inayah da umma yaganah.

Kallon umma yaganah Inayah tayi tana Dan Bata fuska tace”

Umma bin Abbi zanyi abujan nidai bazan iya zaunawaba tunda Haj umma tafara maganan zaije tareda Dr farhat nasan takurasa zatayi Kuma Ni bazan yardaba.

Numfashi umma ta sauke tana dagowa ta kalli Inayah tareda hango kishi me zafi dake cinta Kuma ita kanta tasan manufar Haj umma tayin hakan Dan haka bazata Hana Inayah binsaba indai shine yace zaije da ita Amma yanzu rigima kawai zasuyi tayi itada Haj umman su sakasa a damuwa sbd sun kasa gane sune mutum biyu dayafi so da kauna a rayuwarsa Kuma sunqi jituwa koyaushe rigimarsu neman sakasa damuwa take.

Inayah kiyi hakuri karkice Zaki bisa tunda kinga wani aikin ne ze kaisa.

Shiru tayi batareda zuciyarta tayi na’am da hakanba sedan Bata saba dogon musu da ummanba.

Suna gamawa ta nufi dakinta tayi sallar ishai ta miqe kan sofa tana chatting da Neesah dake sake zugata akan tabi Abbin Kuma Dama itama batada niyar fasa binsa tana Nan tana jiran yadawo suyi magana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button