INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 56-60

Lafiyansu kalau,
Ya Dr Abdulsamad?
Oh sorry kaman a asibiti zai kwana jiya right?

Eh a can ya kwana gashi Zaki Kuma tulawa ‘dan bawan Allahn yarona aiki ki gudu da Abbinki sbd gata ko tausayin ‘dana bakwayi Yana aiki asibitinku.

Dariya Inayah tayi tana cewa”

Bazan dadeba Zan dawo
Kuma ai namasa waya na sanar dashi tunda ai sune manya a asibitin.

Wane time zaku wuce inason kawo sakon Anty iklimat ki wuce Mata dashi sbd idan kinje idan abbin naki ze Bari saiki Kai Mata ku gaisa tanata son ganinki kinji?

Shiru ta Dan kafin tace”

Sai Abbina idan ya yarda zanje.

Ok ganinan zuwa gidan Banda mintuna Zan kiraki saiki fito.

Ok Tom.

Suna aje wayar umma yaganah tace”

Idan ta iso tashigo Mana tunda dai ba cewa yayi kada ta Kuma shigowa gidanba,
Koba komai ai anzama Daya Dole ko baa so tunda ita sirikarsa ce itama Kuma sirikinta ne uwa uba su biyun kaman sune asalinki.

Acan Hadiza kuwa wasu kayan dataiwa Inayah siyayya tun kwanaki da Anty Hafsat tafada Mata aurenda ake tunanin Haj umma Zata saka MAJEED yaqara takeson Bata Amma tana dakatawa sbd batason batawa AA MAJEED din kokuma yaga tanason Bata Masa ‘ya yasa Bata bawa Inayar ba Amma yanzu Kam Bata zatayi suje can su qarata ko zaa samu ya rage wannan kame kamen fuskar ya dawo mutum kaman kowa.

Mintuna masu Dan yawa dauka kafin ta iso gidan sbd sunada Yar tazara
Tana parking takira wayar Inayah saiga zubbi ta fito tashigo da ita har dakin umma yaganah.

Zaunawa tayi suka gaisa a sake sbd zuwa yanzu sun saba sosai Musamman kullum sai Hadizan takira umma yaganah.

Kallon Inayah dake kwance tana faman chatting take bayan sun sake gaisawa tace”

Ga sakon Anty iklimat” wata qaramar envelope ce da takarda aciki.

Karba tayi tana cewa”

Iya sakon kenan?
Na dauka Babba ne¿

No wannan dinma Babbane sbd yanada mahimmanci sosai agunta takardan Daya shafa aikinta ne.

Fira suke sama sama ita Kuma tana chatting a waya sosai suke fira Neesah akan tafiyan nata da Abbi.

Umma yaganah ce tace”

Inayah tashi ki raka ummanki taje ta gaida Haj umma Basu gaisaba
Dagacan kuje dakinki ta tayaki hada kayan tafiyar sbd idan aka biyeki sai abbin yadawo Baki hada komaiba.

Tashi tayi suka fito tareda Hadizan tana cewa”

Yanzu muna zuwa zanyi lefi agurin Haj umma.

Suna shiga kuwa dakin ta zaune kan kujera Salimat na gasa Mata qafafunta ta kallesu da mamaki bayyane kan fuskarta tace”

Baqi akai gidan kenan?

Zaunawa Hadiza tayi tana gaidata cikin girmamawa da Yar sakewa…

Inayah Kuma gadonta ta nufa Zata zauna sbd sun cike kujerun biyu dake sakin
Cikin babban sauti tace”

Maza karki haumun gado ki yamutsa kaman yanda kike mulke gadon yaganah sbd Bata Miki fada,
Zo zauna gefen mamarki karki yamutsan gado.

Kai Haj umma daga Zan Dan hau?
Baga Salimat nanba saita gyara Miki.

Banaso jeki kiyita yamutsa Wanda kika Saba na yaganah.

Miqewa Hadiza tayi suka fito tare tana dariyar Rigimar Haj umman da Inayah.

Suna Isa dakin Inayah
Hadiza tafara kallon koina dakin cikin nutsuwa da kulawa tareda mamakin zuciya irinta MAJEED,

Dakin Inayah yafi kowanne daki girma da tsaruwa tareda Jin dukiya a gidan bayan dakinsa Wanda Batasan Yaya yakeba,

Komai na Inayah a gidan da rayuwarsa is different,
Komai nata na Musamman ne sbd ya banbantata da kowa a rayuwarsa,

Meyesa yake tsananin so da kaunarta irin haka Bayan qyamatarta yakamata yayi sbd rayuwarsa data lalace sanadinta Dana uwarta.

Zama tayi kan sofa tana ajiye qaramar paper bag din hannunta me tambarin Alex Mill.

Cikin kokarin sakewa da ‘yarta tace”

Ina luggage dinki?

Zubbi ta qwalawa Kira a waya tazo tace ta dauko akwati Daya acikin akwatinanta dake sama jere kan closet dinta.

Rimowa suitcase din da zubbi ta dauko Hadiza ta kalla tana kiyasta kudinsa a ranta sbd MJ Muhammed yanada irin set din cikin luggages dinsa.

Da kanta tanufi closet din Inayah din tana zaban Mata kayan dazata saka Mata a akwatin..

Kaya kalilan ta daukan Mata marasa nauyi da wahala sai tsadaddun designer kayan baccin data siyo Mata tazo dasu.
Undies de tasa Mata da yawa sbd lurada Inayahn nada tsafta sosai Dan ko undies dinta dake jere basa iya kirgiwa tun daga kan wainda aka fasa da wainda Bata taba amfani dasuba.

Tana Gama hada Mata kayan ta tsayar da akwatin gefe ta dawo ta zauna gefenta tareda karban wayar hannunta ta ajiye gefe tana cewa”

Inayah kin taba tafiya kuwa dagake se Abbinki?

Girgiza Kai tayi tana kallonta tace”

Baya zuwa damu koina koyaushe muna gida nida umma yaganah.

Numfashi umma Hadizan ta sake tareda riqo hannunta tana Mata Yan maganganu irin na uwa da ‘ya.

Sun jima a dakin kafin suka fito taje tayi bankwana da Haj umma suka fito itada umma yaganah da Inayah har harabar gidan ta Shiga mota ta wuce suna shigewa Abbi na dawowa gidan.

Bai Bata lokaci ba kawai dakinsa ya nufa Kai tsaye ya shiryo yafito janyeda qaramar givenchy luggage Mai shegiyar tsada da kyau
Kai tsaye yacewa Inayah ta samesa mota sbd sun Dan Yi latti zuwa airport din.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR

INAYAH
MamuhGee

GURBIN IDO
Safiya Huguma

SANADIN LABARINA
Hafsat Rano

FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)

BABU SO
Billyn Abdul

Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k

ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

Shedar biya????
07040727902

MTN card????
09134848107[11/11, 9:11 PM] Ummulkhairi: 59
Arewabooks@Mamuhgee
Haj umma Dole rasa bakin magana tayi sbd mamakin Daya Gama cikata ganin da Inayah zaayi tafiyar,,

Tana kallo Inayah ta fito jayeda akwati ta wuce ta gabansu tana masu bye bye harda hawayen kewan umma yaganah da Basu taba tafiya Kota kwana daya bace ba tareba sai wainda tayi da abokan karatunta da suna Australia.

Haj umma yau takaicin da mamakinta har akan umma yaganah datakega tamafi kowa Zama mutuniyar banza.

Inayah na fita driver ya karba akwatinta yasa bayan boot ta bude baya Inda Abbinta yake zaune Yana waya tashiga driver yaja motar sai airport.

Suna Isa kaman hadin Baki saiga Dr farhat qaninta ya kawota airport din.

Cikin mamaki take kallon Inayah duk da tana tunanin ko kawosa airport kawai tayi dan ya wuce fuska a sake tace”

Babyn Abbinta ce takawosa airport din da kanta yau.

Murmushi itama tasake tana kallon ashraf qanin Dr farhat din tace”

Yaya ashraf barka da yau.
Gun Dr farhat ta dawo da kallonta har lokacin da murmushi kan fuskarta tace”

Ba rakosa nayiba Dani zaije hankalina be kwantaba da tafiyan Abbina shi Daya.

Dan waro Ido Dr farhat tayi cikin mamaki da dariyar rainin hankalin Inayah tace”

Waini yaushe duk kika Zama hakane Inayah?
Maganar Haj umma Gaskia ce gata na neman maidaki wata abin dabam,
Abbin nakine kike cewa Zaki raka sbd hankalinki be kwantaba?
Shima AA MAJEED Gaskia yakamata yarage Miki wannan gatan ya fara Zama wani iri.

Dariya Inayah kawai tayi tareda wucewa gaba tabi Bayan Abbinta da Bai wani tsayaba tun fitowarsa mota ganin Dr farhat.

Jirgi Daya suka Shiga Kuma dukansu a first class suke Dan haka Inayah ganin Yana tareda CM da wani babban mutum abokinsu Daya yasata zaunawa gurin Dr farhat tana Dan biyewa zancenta sama sama Danma umman Dr Abdul tasata Dena nunawa Dr farhat din shariya da wani abin shiyasa take daurewa tana basarwa a gabanta Kuma hakan yasata Jin dama Dama da yanzu rigima Zata fara.

Shi kansa Abbin zaune yake dasu CM din Amma zuciyarsa na kan Inayah dake tareda Dr farhat Sam bayason ta dauki damuwar ganin farhat din suje ta daga hankalinta kawai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button