INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 56-60

Maganar Dr farhat damunta takeyi Musamman muryarta jinta take tana toshe maqoshinta da kishi sbd har maganar Abbinta takeyi cikin nuna kulawarta da kaunarta garesa,.

Rufe idanuwanta kawai tayi tareda yin baccin qarya sbd kawai tai Mata shiru da fadan sunan Abbinta a bakinta sbd hakurinta da juriyarta sun fara qarewa.

Dayake tafiyar yamma sukai ana Isha suka sauka.

Motoci biyune daga gidan Wanda suke tare sukazo daukansu
CM dashi Alhj falalun suka shiga mota Daya suka wuce dayan motar kuwa shida Inayah da Dr farhat suka Shiga.

Shine a gaba tareda driver sai ita da Dr farhat a baya.

Kai tsaye gidan anty juwairiyyah suka nufa Dr farhat itace me bada address din da alama harsun Saba koma har ta taba zuwa gidan.

Suna parking shine ya daga wayarsa yakira anty juwairiyyah din..

Tana dauka Kai tsaye yace mata”

Gamu a gaban gidanku.

Da Murna anty juwairiyyan ta tashi daga zaunen datake cikin babban palonta tareda ‘yayanta da Anty safiyyah ma tana gidan tana jiran isowarsu taga MAJEED dataketa gani a hoto yazama babban mutum masu fada aji.

Fitowa sukayi harabar gidan anty juwairiyyah tasa megadi ya bude musu gate suka shigo da motar.

Ana parking Dr farhat ta fito cikin farin cikin ganinsu suka rungume itada anty juwairiyyah dasuka Saba sosai a waya.

Inayah kuwa qin fitowa motar tayi ta kalli Abbinta dashima ita yake kalla ta mirror yace”

Ya ya?

Marairaice fuska tayi tareda ciko hawaye a idonta na kishin Dr farhat dake cinta sosai tana dannewa tun a Abuja zatai magana ya bude motar ya fito a natse kwarjininsa ya cikawa su Anty juwairiyyah da ‘yayansu dasuka fito gaida uncle din nasu da Basu saniba sedai labari Ido,

Anty safiyyah Neman daburcewa takeyi da zallar haiba da kamalar da Allah yacikasa da ita ga uwa uba dala data Kama ta zauna….

Gefen da Inayah take ya bude ahankali tareda kallonta cikin kulawa yace”

Rigiman me zakiyi ba kince Zaki zauna anan ba kafin nagama mukoma?

Fitowa motar tayi ahankali tareda tsayawa gefensa ta riqe hannunsa cikin shagwaba a hankali tace”

Aa bazan iya zaunaba anan Kuma.

Numfashi ya sauke tareda juyowa suka nufo gurinsu anty juwairiyyah dasuka ja poster duk su dukan suna kallon ikon Allah Baki sake.

Anty juwairiyyah data ‘dan San kadan daga halin Inayah da rayuwarta murmushi tasake tana kallon MAJEED din batareda ta damu da halin Inayah ba a sake cikin kulawa tace”

MAJEED barka da isowa,
bazaka shigo ko abinci kaciba anyi maka dinner Musamman domin zuwanka Naga ka tsaya daga Nan.

Agogon Omega dake daure hannunsa ya kalla kafin ya dago kyakkyawar fuskarsa ya kallesu Yana Dan kokarin wadata fuskar da murmushi Mai nutsuwa yace”

Inada baqin dazan gani 9 Dan haka ba time din tsayawa cin abinci
May be next Inshallah.

Anty safiyyah ya kalla fuskarsa har lokacin da sauran kyakkyawan murmushinsa yace”

Barr Ina wuni?
Ya family?

A daburce tace”

Lafiya kalau alhmdllh,
MAJEED zance kokuwa AA MAJEED?

Wani murmushi yasake Yana amsa gaisuwar ‘yayansu dake gaidasa cikeda girmamawa da farin cikin ganinsa.

Farin cikin ganin yaran yasashi kallon tasa babyn datake riqeda hannunsa daya har lokacin Kuma a hakan ta gaisar dasu duka itama ba laifi fuskarta asake.

Cikin kulawa yace”

Ok I have to go Inayah time na tafiya kije ku shiga ciki zandawo gobe sai a kaiki Inda kikace din gidan Dr waye???

Qin sakinsa tayi tana kallonsa a Dan marairaice tace”

Abbi Zan bika please.
Ni bazan iya bacci ba anan muje goben se nadawo Nan.

Ganin yaransu anty juwairiyyah na kallon zuqeqiyar budurwa na Dan shagwaba yasashi yanke Rigimar da cewa shikenan.

Da kulawa Anty juwairiyyah tace”

Haba Inayah kiyi hakuri ki kwanar Mana zakiji dadin Nan dinma
Zaki Saba dasu rumanah gasunan manyan Yan Mata kamarki.

Dan murmushin yaqe ta saki ahankali tana gefensa tace”

Gobe Zan dawo saimu Saba.

Baki anty safiyyah ta bude zatai magana anty juwairiyyah datasan a banza zatayi ta hanata sbd MAJEED akan Inayah baya Gene zancendaba Wanda takeso ba.

Ita anty safiyyah so tayi MAJEED dinma ya tsaya su zanta sosai na yaushe rabo
Su Kuma fahimci juna tunda dai yanzu dukansu ba quruciya atare dasu bare shi Daya Zama babban mutum duk da sune yannan Amma ai yanzu Kuma shine ubansu.

Hannunta cikin nasa suka juya zuwa Mota bayan driver ya mayar da akwatinta da aka fidda tare dana Dr farhat data shige tuni Batasan Rigimar da aka tsaya Yi a wajenba Dan ta dauka MAJEED din ze shigo cin abinci kaman yanda anty juwairiyyah ta fada.

Suna fita gidan ya juyo ya kalli fuskarta dakeda sauran rigima
Itama ta juyo ta kallesa tana sake Bata fuska tace”

Abbi da gaske nake bazan iya bacci acanba.

Hannunta dake riqeda nasa ya dago ahankali yayi kissing yace”

I Know.

Murmushi tasake tareda sake matsowa jikinsa tana lafewa.

Transcorp Hilton dake maitama suka driver yakaisu sbd acan akai Masa reserving Lafiyayyan daki.

Tunda suka fito motar hannunta na cikin nasa driver na janyeda akwatinansu a bayansu kafin ma’aikatan hotel din suka karba Kai tsaye suka nufi lift suka shige zuwa dakinsu.

Suna Shiga dakin ta saki hannunsa tana nufar tsadaddun kujerun Dake dakin ta zauna tana ajiye handbag dinta da wayarta Dake hannunta.

Kai tsaye toilet ya wuce yayo wanka yafito daureda sabon towel fil da aka jera masu a dakin.

Bai tsaya Bata lokaciba ya shirya tareda zuwa zura jallabiya fara Sol yayi sayi sallolinsa Yana idarwa ya kalli agogon Daya sauya na Patel Philippe yaga time yaja Dan haka ya tashi ya shirya cikin ash luxury filtex Mai tsananin taushi da shegiyar tsada ya juyo ya kalleta tayi zuru tana kallonsa kaman Zata rusa kuka ganin yanda yake zuba qamshi da wani cika Ido da kyansa da kwarjininsa.

Ahankali ya shafa fuskarta yace”

Zanje nadawo kiyi ordern abincin da kike buqatan ci ok?

Dafa hannunsa tayi Tana gyada Kai.

Juyawa yayi ya fice.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda tashi na nufi toilet tayo alwala.

Sallolin dake kanta tafara Yi kafin ta tube ta koma toilet tayo wanka tareda gaso jikinta da ruwan zafi ta fito daureda towel itama.

Mai tashafa sama sama tareda turare kadan ta bude kayanta ta dauko kayan baccin dazata saka taga duka Babu masu wando sai Yan dogaye da umman Abdul ta siyo mata,

Tafison kayan bacci masu wando sbd sunfi dadin bacci agurinta Amma haka ta saka Daya daga cikin na umman Abdul din batareda ta damu da fingilewar rigarba.

Tea da snacks sai kebabs tayi order aka kawo suka jere kan dining dake qatoton dakin suka fice kafin tazo ta zauna ta Sha tea sosai taci snacks da kebabs din kadan ta tashi sbd bacci takeji.

Brush takuma Yi tadawo ta zauna kan kujera tana jiran dawowar Abbin Amma har bacci ya dauketa Bai dawoba.

Sai guraren 11:30 ya dawo…

Gabaki daya qamshin turarenta ya Gama gauraya sanyin ACn dakin..

Qarasowa yayi a hankali cikin nutsuwa ya tsaya akanta Yana kallonta wayarta na rungume a kirjinta da alama kiransa taketayi har baccin ya dauketa.

Hannu yakai ya zare wayar zai ajiye gefe hotonsa Dake wallpaper na lock screen ya fito baro baro,

kallonta yayi yana sake kallon wayar,

Shafa fuskarta yayi ahankali tareda Kai fuskarsa yayi kissing lips dinta ahankali Yana kallon cinyoyinta Dake bayyane afili suna sheqin lafiya da hutu,

Rigar jikinta yabi da kallo tun daga saman har Inda ta tsaya daidai ko Rabin cinyarta Bata kaiba
Tabi ta lafe kan jikinta tagama bayyanarta ni’iman da Allah yayi Mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button