INAYAH COMPLETE HAUSA NOVELINAYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

INAYAH 56-60

Kai tsaye gidan Dr iklimat suka nufa Batada wani nisa sosai Dan itama a maitama take.

Umman Dr Abdul tun acan Daman tabawa Inayah address dinta Dan haka drivern Kai tsaye yakaisu har kofar gidan.

Suna Isa Dr iklimat da kanta ta fito ta tarbesu cikin wayewa da farin cikin ganin Ayshatouh me tsanani tamkar itace ta haifeta sbd kusan atare suka Sha wuyar rashin ganinta itada Hadiza wancan lokacin gashi itama batada ‘ya mace ko daya ‘yayanta biyu duka maza ne sun girma tuni basama qasar dukansu.

Babu wani damuwa ko kame kame tasaki jiki ta gaisa da MAJEED shima ba laifi ya Dan sake Mata sbd Inayah dayaga hankalinta yafi kwanciya anan din da Bata saba ko taba zuwaba Akan gidan juwairiyyah ko safiyyah.

Bai shiga gidanba ya juya da nufin dawowa anjima daukanta ya wuce.

Suna Shiga gidan Dr iklimat ta ringa dawainiya da Inayah din tana nuna Mata farin cikinta sosai da ganinta da zuwanta gidan,

Ko masu aikin gidan kusan duk sunsan Anty Hadiza nada ‘yar data Bata ganin Inayah yasasu Mata hidima cikin kulawa da girmamawa sbd kowa Kam yasan yanda anty Hadiza ke tsananin Jin Ayshatouh a zuciyarta.

Dr iklimat mace ce Mai sakewa da faran faran tareda kulawa Musamman tana gane gatan dayayiwa Inayah yawa ta ringa wani lallabata tana janta ajiki
Inayah Kuma dayake dama gata tasaba dashi da tattali take ta saki jikinta ta sake da Dr iklimat din ganin sai wani gata da lallabata takeyi.

Hadiza tayi waya da antyn tata Dr iklimat taqara Mata bayanin komai akan abinda ake ciki na dalilin tafiyar Inayahn Abuja ta biyo Abbinta.

Fada Dr ta ringa Yi sosai tana ganin lefin Hadiza da bazata sake ta cusa ‘yarta da gyarataba su qwaci yancinsu agun uwar MAJEED din,

Ita kanta Inayah Saida Dr din Tai Mata fadan uban me take jira da Bata dauki cikiba kowa ya huta masu mutuwa su mutu masu bin duniya subi can su suka jiyo.

Dayake dama Hadiza nada niyar zuwa Abujan yau tun jiya ta yanki ticket Koda suke waya tana airport daman Dan haka ba zato Inayah taganta driver yaje ya daukota da mamaki take kallonta tace”

Umman Dr dazu Koda muke waya kina hanya kenan?

Da farin ciki kan fuskarta tace”

Eh ba Dole nazoba sbd inason na kwana Ina zantawa da ‘yata tunda haryanzu Abbinki yaqi yafemun yaban cikakkiyar dama.

Dan murmushi kawai Inayah tayi tana cewa”

To ai ko yanzu ba anan Zan kwanaba anjima zai dawo tafiya zamuyi.

Dariya Dr iklimat tayi tana cewa”

To ai yau de Dole ku hakura anan Zaki kwana.

Kallonta tayi zatai magana Hadiza ta hanata ta hanyar dafa hannunta cikin kulawa tace”

Inayah,
Ba kowace magana ake bada amsartaba,
Ni mahaifiyarki ce
wannan Kuma da kike gani yayatace dukanmu bazamu cutar dakeba
Bakyason kema ki ringa bugun gaban kinada Yan uwan nunawa
koyaushe daga Abbinki sai Abbinki kawai,
Shima yanzu Yan uwansa sun dawo rayuwarsa muma ki bamu Dama mu dawo rayuwarki.

Shiru tayi tana sauraronsu sunata Mata maganganun hikima da lurarwa,

Dr iklimat Bata bartaba Saida tasa Mata ra’ayin son kwana gidan tagani yau abbin zai iya bacci kaman jiya batareda itaba.

Murmushi tasake zancen na Mata Dadi da Dr tace”

Daqyar yau zaiga safiyar gobe.

Ba kunya ta nuna farin cikinta tana tunanin yanda zaiyi.

Hadiza wanka tayi tai sallah kafin taci abinci ta zauna tana shiga firar Dr da Inayah.

A cikin wunin suka fahimci yanda rayuwar Inayah take sosai ba kwabar magana gata yayi Mata yawa sosai hakama soyayyar abbinta tariga ta ginu cikin ranta sosai ta yanda Babu abinda zai girgiza hakan sai ubangijin Daya dasa Mata wannan so da kaunar,

Ta bangare Daya sosai suka jinjinawa MAJEED da ganin girmasa Mai tsanani ya qaru a idonsu sbd yanda Inayah take fada musu yanda take rayuwarta dasuke qiyasta gata da girman son dayake Mata.

Sanyi jikin Hadiza yakuma Yi sbd tasan Koda a hannunta Inayah ta taso bazata Bata irin girman gata da tarbiyar da MAJEED ya bataba.

Dr iklimat kuwa cewa tayi to ai bamuga zamaba tunda ‘yar Tamu tagama mutuwa a sonsa koina fada takeyi gaban kowa Dan haka Dole wannan kurman abbin naki ya magantu Dan Naga alaman bazaiga girmanmuba sai ‘yarmu tagama da bude Masa Ido.

Ba Bata lokaci suka fara dirka Mata wasu Hadi na natural Kaya na Musamman.

Da farko bataso Amma haka Dr ta bude Mata Ido tasakata Shan abubuwan kala kala.

Hadiza Kam farin ciki take ciki yau ta wuni Zata Kuma kwana da ‘yarta ga MAJEED datasukeson saukewa duk wata kamewa ya samu farin ciki da Jin Dadi kaman kowa.

Sai bayan sallar ishai har sunci abinci abbin yazo daukanta.

Da farko marairaice fuska tayi tanajin son binsa Amma su Dr ta bude Mata Ido ta hanata Dan haka ta fasa tareda Dan Kama kanta.

Shigowa dashi akai har Lafiyayyan palon gidan yana shigowa akanta idonsa ya sauka tana fitowa daga hanyar bedroom din Dr iklimat sanyeda wasu kayan dabam.

Da kulawa yake kallonta da kayan data sauya na wata doguwar Riga Mara albarka Dan kuwa rigar robace doguwa har qasa ta lafe jikinta tun daga sama har qasa ta fidda duk wata albarkar shape din jikinta Musamman shafaffen cikinta dayasa kirjinta dake cikin padded push-up bra.

Dan gyara muryarsa kadan yayi tateda dauke Ido daga kanta Yana sake gaisawa da Dr iklimat Dake rokonsa ya tsaya yaci abinci yace aa yariga yayi dinner tareda baqinsa.

Hadiza ce itama ta fito fuskarta a Dan sake jiki ba kwari ta gaishesa.

Yayi mamakin ganinta Amma Bai nunaba ya kalli Inayah dashi take kallo ya amsa gaisuwar Yana Dan kallonta da cewa”

Ashe kina garin?
Allah ya taimaka.

Amin suka amsa ta juya ta shige tabarsu.

Miqewa yayi Yana kallon Inayah yace”

Kije ki shiryo mu tafi time na tafiya.

Kallonsa tayi cikin marairaicewa tace”

Abbi Zan kwana anan tunda gobe zamu koma please..

Kallonta ya juyo yayi da kyau Yana mamakinta sanin Bata iya kwana baqon gurinda batasan kowaba.

Cikin kulawa Yana kallonta yace”

Zaki iya kwana anan?

Gyada Kai tayi tana kallonsa.

Kin tabbata?

Sake gyada Kai tayi tana kallon yanayinsa dayake sake nanata tambayar.

Hannu ya miqa yace”

Zo Nan.

tahowa tayi ahankali tana kallonsa a shagwabe maimakon ta Kama hannunsa saita shige jikinsa ta Dan kwanta tana cewa”

Abbi Zan iya kwana anan Ina sone.

Dago kanta yayi ya kalli fuskarta cikeda kulawa yakuma cewa”

Are you sure?

Yes Abbi” tace ahankali tana kallon fuskarsa cikeda kauna da shagwaba.

Numfashi ya sauke ahankali kafin yace”

Ok shikenan Zan barki anan din Amma idan kin kwanta kinji bazaki iyaba ki kirani Zan dawo na daukeni ok??

Okay, I will miss you my Abbi.

Lumshe fararen idanuwansa yayi tareda sakinta Yana cewa”

Shikenan kije ki saka Kaya masu nauyi ki kwanta akwai sanyi.

Gyada Masa Kai tayi tana sakin hannunsa.

Sallama yayi da Dr iklimat Dake tsaye tana kallonsu cikeda shaawa da burgewa batareda ta damuwaba sbd tanada wayewarta sosai ba komai bane agurinta.

Yana ficewa Inayah ta sauke ajiyan zuciya tana juyawa ciki itama.

Shima Yana fita bayan ya shiga mota numfashi ya sauke me zafi tareda Dan rufe Ido ya bude Yana sake danne zuciyarsa kafin ahankali ya bude Baki yacewa driver sutafi kawai.

MAMUH

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button