BABU SO HAUSA NOVEL

BABU SO 17

17

……..Kasancewar Abie a wajen ya sashi ƙin cewa komai ya ɗauketa gaba ɗayanta ya haura sama aunty Mimi biye da shi. Ɗakin Mamie suka nufa kamar yanda Aunty mimi tace.
     Wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfin gaske lokacin da yake ajiyeta akan gado, dan tunda ya ɗakkota ta ɗauke numfashinta da rumtse idanu zuciyarta na bugawa da sauri-sauri. Shi ɗimma dake ƙoƙarin dannewar tashi zuciyar bugu take da gudu a ƙirjinsa har numfashinsa na seizing. Ajiyar zuciyar ya sauke tamkar ita, sai dai tasa ta fitane a ɓoye. Sallamar Mamie ta sashi haɗiye abinda ke masa kaikawo, tray ɗin hanunta ya amsa yana ɗan murmushi da faɗin, “Mamie da kanki”.
      Murmushin itama tayi batare da tace komai ba, ta harari Anam dake kwance lamo tana sauke ajiyar zuciya. “Mai rakin tsiya yanzu waye yaji daɗin? Nikam zanga yanda zaki ƙare lokacin rainon ciki balle ranar haihuwa, mijinki dai yaga takansa ai”.
     Dariya aunty Mimi ta sanya, yayinda Anam ke tura baki gaba, taɗan saci kallon Shareff sai ko idonta cikin nashi. Sosai ya sarƙeta da su, sai da ƙyar ta samu damar fisgewa tari mai alamar sarƙewar yawu na kufce mata. Wani irin yanayi data kasa bama fassara ta karanto a cikin ƙwayoyin idanunsa, hatta da tsigar jikinta yamutsawa ta shigayi, ga tarin yaƙi tsayawa har sai da Aunty Mimi ta tadata zaune tana bubbuga bayanta. Kamar ba shine sanadin komaiba cike da basarwa ya miƙama Aunty Mimi ruwan, a baki ta saka mata, sai da tasha sosai kafin tarin ya lafa idanunta har sunyi jajir. Sannu Mamie tai mata tana ƙoƙarin ficewa domin nuna kara garesu tunda dai duk suna ƙoƙarin nuna kulawa gareta bai kamata ita saita tsaya ba.
     Yana daga tsaye har Aunty Mimi ta bata umarnin fara cin abinci bayan ta ɗaura mata tray ɗin akan cinyarta. A hankali ta fara cin abinci, sai ƙunƙuni take a zuciyarta na zamansa ɗakin. Oho bai san tanayi ba, dan babu alamar zai fita ɗin. Aunty Mimi ta miƙe ta fita saboda kiran mijinta daya shigo mata a waya.
       Shiru ɗakin bakajin motsin komai sai na ƙarar spoon da take juyawa a plate, dan gaba ɗaya tama kasa cin abincin yanda ya kamata, tarasa mike damunta, kunyarsa ko haushinsa, dan abinda ya faru a gidanta ɗazun ya gagara barin zuciyarta. Jin shiru kamar baya ɗakin ya sata ɗan ɗagowa da nufin satar kallonsa sai suka sake haɗa ido. Kanta ta maida ga abincinta tana sake tsuke fuska.
     (Sai kallon tsiya) ta faɗa a ranta. Kamar yaji mitake faɗa ya zura wayarsa a aljihu yana ɗan jan siririn tsaki. “Baki iya komai ba sai kallon mutane laziness”.
     Kasa daurewa tai sai da ta ɗago ta kallesa idanunta cike da tsiwa. “Toni da baka kalleniba zaka san ina kallonka ne…..”
       “What!”.
  Ya faɗa cikin ɗan kausasa murya da waro idanunsa kanta sosai. “K! Wai yaushe na zama abokin wasanki ne a gidan nan?”.
       Ƙin cewa komai tai, sai dai bakinta a sama kamar zai taɓo silin. A ranta ko addu’a take aunty Mimi ta dawo kafin ya fara zazzabga mata maruka. Ganin yana matsota tai saurin faɗin, “Amma matarka ɗazun datai iskanci agaban mutane baka hukuntata ba sai ni, kuma jinina da aka zubar sai na rama”. Ta ƙare maganar wasu zafafan hawaye dake nuna tabbacin abun na ranta kamar zanen dutse har yanzu suka shiga rige-rigen sakkowa. Cak ya tsaya yana kallonta, kuka take sosai kamar wadda aka doka, kusan tsahon minti guda da wasu sakanni ta gagara tsaidasu. A hankali ya rumtse idanunsa, tare da furzar da ƙaramin huci daga bakinsa. Shiru bashi da alamar cewa komai balle lallashinta, itako sai ƙara matso hawayen take wani baƙin ciki da takaicinsa na sake hasalata, tabbas da ace lafiyar ƙafarta ƙalau ɗakin zata bar masa….
       “K sau nawa ina hanaki tarayya da wannan yaron amma kika maidani sauna? Bayan shi ba muharraminki ba itako Matata ce!”.
     Karan farko da tunda ta fara kukan ta ɗago jajayen idanunta tana kallonsa cikin tsakkiyar ido. Shima kallon nata yake a tsakkiyar idon……
       Ita ta fara janyewa cikin ƙunƙuni tana faɗin, “Ni dai baza’a rabani da masoyina ba”.
Sosai kalaman nata suka daki ƙirjinsa. Sai dai kafin yay wani yunƙuri aka dakatar da shi.
“Mike faruwa anan?”.
   Aunty Mimi dake shigowa ta faɗa cikin dariya. Ita ta fara janye nata idanun, batare da tace komai ba ta zame ta kwanta. Shima numfashi ya ɗan fisga, cikin yanayi kamar mai borin kunya ya ɗaga kafaɗarsa. “Nothing Aunty. Zan wuce gidane goodnight”. Kafin ta samu damar cewa wani abu yayi ficewarsa. Da kallo ta bisa har ya fice, kafin ta juyo ga Anam dake faman sauke ajiyar zuciya.
     Komai batace mataba, sai da ta tadata zaune ta bata abincin da kanta tare da magungunanta sannan ta fiskanceta da ƙyau. Kai tsaye tace, “Mamana kina son Shareff ko??!…”
        “God for bid Ummie”.
  Ta faɗa cikin tarar numfashin Aunty Mimi da saurai.
    “Sure?”.
“Yes Ummie”.
Yanda ta bada amsar da ƙwarin gwiwa yasa Aunty Mimin haɗe fuska tana mata kallon sama da ƙasa. Cikin rashin wasa tace, “To _BABU SO MIYA KAWO KISHI?!”.
        “Kishi kuma Aunty? A dalilin mi zanyi kishinsa?”.
     Ko amsa ɗaya Aunty mimi bata amsa mata ba, sai dai ta kafeta da ido ganin hawaye na ciko mata ido. cikin ɗan ɗage kafaɗa tace, “Okay fine kwanta kiyi barci”.
    Kwanciyar tayi, tana ta faman ALLAH ya kiyaye ta so wannan mutumin a zuciyarta, a fili dai bakinne kawai ke motsawa babu sautin fitar magana……

    ★★

   A hankali yake driving ɗin tamkar baya so ko kuma shi kaɗaine a titin, motoci da yawa sai sun masa horn yake ɗan kaucewa ya basu hanya su wuce, ga kiran Fadwa dake faman shigo masa waya babu ƙaƙƙautawa. Sai da tai wajen bakwai baida alamar ɗauka, ana takwas ɗinne ya fisgi wayar a fusace daga change daya sata yakai kunne. Sai dai baiyi magana ba dan inhar ransa ya ɓaci baya son ya ringa cewa komai….
      “My son!”.
Muryar aunty Mimi tazo masa a bazata. Da sauri ya cire wayar a kunensa ya kalla. Tabbas Aunty Mimi ɗince ba Fadwa ba. Yawu ya haɗiye da ƙoƙarin saisaita kansa. “Yes small Mom ko nayi mantuwa ne?”.
      “Da alama tunda ka tambaya ƙila kayo ɗin”.
  Ƴar dariya yayi yana shafa kansa da lanƙwasa kan motar ya shiga layin gidansa. “Aunty kenan, da alama magana kike nema dai kawai”.
         “Kusan hakan, sai dai kai tsaye zan yita, kamar yanda nayi a ɗayan ɓangaren”.
      A hankali ya tsaida motar a ƙofar gate, sai dai baiyi horn ba. “To ina saurarenki mamana!”.
        “Babana kana son Anam ko?!”.
    Da ace ruwa yake sha ko cin abinci babu shakka sai ya ƙware dan abinda Small mom ɗin nasa ta faɗa yazo masa a baza. Ya haɗiyi yawu da sauri jin maƙoshinsa na ƙafewar danshi. Yay ƙoƙarin saisaita kansa kai tsaye yace ni da nai aure sati guda kuma”.
     “Ba labarin aurenka nake tambaya ba, dan nima ban manta lissafin ba. Ka bani amsata kawai”.
          Steering ya ɗan daka yana cije lips, cikin son kauda mata dukkan wani tunani babu ko gargadar murya ya bata amsa.
     “Aunty ni matata kawai nake so, bayan ita babu wata a raina”.
        Shiru Aunty Mimi tai, sai kuma ta saki murmushi mai sautin da har yaji, cikin dakewa tace “Sure?”.
     “Babu kokwanto a maganata Mom”.
“Okay fine. To amma _BABU SO MIYA KAWO KISHI?!”.
        “Kishi kuma?! Sai dai na zuminci”.
     Ƴar dariya aunty Mimi tai da faɗin, “Lallai kam”. Tana yanke wayar.
      Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka yay baya luuu jikin sit ya kwanta, idanunsa da suka canja launi ya lumshe, tsahon mintuna ya kasa horn balle yunƙurin shiga gidan. Ga kiran dake shigo masa waya da baya raba ɗayan biyu Fadwa ce amma ya kasa yin komai. Sai da ya sake shafe kusan mintuna goma sha biyu har mai gadi ya gaji da leƙowa ransa fal mamakin lafiya sannan yay masa horn.
       Da ɗan gudunta ta fito, duk da ranta a ɓace yake saboda kiran da take jera masa yaƙi dagawa sai ta danne saboda shawarar su Sima da take hange mafita a gareta basai ta cigaba da tada jijiyar wuya a wajensa ba. Ta ɗanesa tare da maƙalƙalesa, ko kulada yanayinsa batai ba ta haɗe bakinsu. Ƙoƙarin janyeta yay yana kauda kansa kodan maigadi da yake da tabbacin zai iya hangosu amma ta hanashi damar hakan. Dole yay ta maza ya tura murfin motar da kafarsa ya ɗauketa gaba ɗayanta yay sasheta bayan ya raba bakinsu da ƙyar. A kujera ya zube da ita jikinsa, babu wani ɗaga kafa ta sake maida bakinta kan nasa. Baya buƙatar komai a halin yanzun, sai dai bazai iya ƙin bata hakkintaba koda ace faɗan doke-doke sukai indai ta nema zai biya mata, balle ma baya buƙatar haɗa wata matsala tasa ta waje da cisgunawa iyalinsa  wannan alƙawarine ya daukama kansa insha ALLAH, laifinta kuma zai mata hukunci a lokacin daya shirya. Duk da babu wani karsashi tare da shi ita ke kiɗanta tana rawarta bata damuba, sai da ta tabbatar ta isar da saƙon da take bukata sannan ta barsa tana mai kallonsa cikin ido cike da so da kaunarsa.
    “I love you my Soulmate”.
Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe akanta. Batare da yace komai ba ya lakaci hancinta da yatsansa. Sai kuma ya ɗanbi falon da kallo. Ganin komai tsaf yaji haushinta ya ragu a ransa. Ya ɗan rungumota jikinsa da sumbatar hancinta. “Haka nake so na dinga ganinki k da gidan nan a koda yaushe”.
     Kai ta jinjina masa tana murmushi da faɗin, “Zaka sameni mai aikatawa”.
         “ALLAH yay miki albarka bari naje na ɗan watsa ruwa”.
     “Kodai ka fara cin abinci”.
Ɗan kallonta yayi na wasu ƴan mintuna, “Sure baiyi ƙauri ba na yau?”.
         “ALLAH bai yiba”.
   “Okay muje”.
Duk da ba son cin abinci yake ba haka ya dinga turawa, dan babu makusa a girkin sai abinda ba’a rasa ba. Dan kawai ya bata ƙwarin gwiwar cigaba dayi kamar hakan ya yaba tare da saka mata albarka..

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button