JIDDAHTUL KHAIR 15

Umma ta sauka motar bayan drivernta yayi parking, Jiddah ma ta sauka tana kallon babban gidan, Umma ta kalli driver tace “Ka je kawai idan xan dawo anjima xan kiraka…” Cike da ladabi yace “Toh Hajiya” ta kalli Jiddah tace “Mu je” Bin bayanta Jiddah tayi tana tafiya a hankali har suka isa main parlor din gidan, kasancewar ranan asabar ne su Ramlah duk sun tafi islamiyya, Mai aiki ce kadai parlon tana aikace aikace, ban da kamshi babu abinda ke tashi parlon, mai aikin ta gaida Umma da ladabi, Umma ta amsa da fara’a tana mata sannu da aiki sannan ta kalli Jiddah tace “Toh xauna Jiddah” Xata xauna kasa Umma tace “Aa tashi ki hau kujera” Mikewa tayi ta xauna saman kujeran Umma ta nufi bangaren yayarta, sai a sannan Jiddah ta gaida mai aikin, matar ta amsa mata da murmushi tana ci gaba da abinda take, Muryar Abuturrab Jiddah ta ji ta d’an saci kallon gefenta amma bata gansa ba, slowly yake tahowa waya kare kunnensa yana waya tare da wani colleague dinsa da ya kirasa don jin ya jikinsa, murmushi Abuturrab yyi yace “Wato the sky misses me, not my co pilots” Murmushin kawai yake, daga karshe suka yi sallama da Captain Ishaq ya katse wayar ya nufi kitchen, 3 quarter ne jikinsa da farin T shirt, Mai aikin gidan Naja’at ta d’an risina ta gaishesa with respect ya amsa without looking at her, Jiddah ta bi sa da ido, har xai shiga kitchen ya juya coz he saw someone sitting amma bai kalli ko waye ba, suka hada ido, da farko bai ganeta ba sai da ya tsura mata ido, ita dai tayi kasa da nata idanuwan tace “Ina kwana” daga sama har kasa yake kallonta, Naja’at tace “Tana gaisuwa ranka shi dade” Juyawa yayi ya shige kitchen abun sa, Naja’at ta sunkuyar da kai sanin kadan daga abinda xai iya aika kenan, can ta d’an yi murmushi tana kallon Jiddah tace “Ina jin bai ji ba” Jiddah tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba, Umma ta shigo parlon tare da Ummi, Ummi na kallon Jiddah tace “Sannu da xuwa” Jiddah ta gaisheta da ladabi, Ummi ta amsa da d’an murmushi fuskarta, Ummi na kallon Naja’at tace “Tafi dakin Hajiya Hafsah ta xo su gaisa da bakuwa” Naja’at tace “Toh Hajiya” daga haka ta wuce da sauri, Ummi ta xauna Umma ma ta xauna, gaba daya Jiddah sae taji ta kasa sakin jiki, duk ta takura, Ummi tace “Ya kika kara ji da jiki?” A hankali Jiddah tace “Alhmdlh” Abuturrab ya fito daga kitchen rike da cup din shayi yana juyawa da cokali, Umma ta dinga kallonsa, sannu da xuwa kawai yayi mata ya nufi dakinsa ya ajiye cup din shayin, ba a dau lkci ba sai gashi ya fito, ya karaso cikin parlon ya xauna yace “Ina kwana Umma” Da murmushi tace “Lafiya lau Abuturrab, ka tashi lfya?” Yace “Alhmdlh” Umma ta kalli Jiddah tace “Kun gaisa kuwa” Jiddah na kallonsa tace “Ina kwana” Ba tare da ya kalleta ba yace “Lafiya lau” Ummi dai kallonsu kawai take, Aunty ta shigo parlon ganin Umma tace “A’a Sannu da xuwa Hajiya Ramlah” Umma na murmushi tace “Yauwa, mun same ku lfya?” Aunty tace “Alhmdlh wllh” Aunty na kallon Jiddah tace “Sannu yan mata…” Jiddah ta gaisheta tana kallont, Aunty ta amsa ta nemi waje ta xauna, Ummi na kallon Abuturrab tace “Sai ka kai ta parlon Abbanku su gaisa tunda Kawunnanka na ciki” Abuturrab mood dinsa ya sauya lkci daya, Aunty dai sae murmushi take a xatonta ko ‘yar uwarsu ce Jiddah warce bata sani ba, ganinta fara sosai kamarsu Ummin, Mikewa Abuturrab yyi, Umma na kallon Jiddah tace “Tashi ki bi sa” Ta mike a hankali ta bi bayansa, Ummi ta bi su da kallo, ba karamin kyau hijab din yyi mata ba har kasa kuma yake ja, Wani boyayyen ajiyar xuciya ta sauke, Aunty na gyara daurin dankwalinta tace “Bakuwa aka yi, kamar yar uwarku naganta ita ma fara, amma ban santa ba” Ummi na kallon Aunty tace “Ita ce yarinyar da yaje ya aura ae” Da sauri Aunty ta bi Jiddah da kallo idanuwanta kamar xa su fito, Daga Umma har Ummi kallonta suke, da wani confusion tace “Ita ce yar hayin??” Umma tace “Ita ce fa” Aunty ta hade rai lkci daya, can ta girgixa kai tace “Toh meye fa’idar kawota nan din tunda dai sakinta xai yi, haba ni dai ina ta kallonta ganin halin gidadanci a tare da ita, to yanxu meye amfanin xuwa da ita har ace taje ta gaida kawunnansa??” Wani kallo Umma tayi mata ta dauke kai, Ummi dai bata ce komai ba, Aunty ta ja wani tsaki ta mike ta fice daga parlon. Da sallama Abuturrab ya shiga parlon Abbansa Jiddah na biye da shi, Abba na xaune tare da yayansa da kaninsa, Abuturrab ya xauna kasa ya sunkuyar da kai, d’an nesa da shi ta xauna ta takure cikin Hijab, cikin sanyin murya ya gaishesu gaba daya, ko wannensu ya amsa mata da fara’a, Alhaji Lawal na kallon Abuturrab yace “Ita ce?” Abuturrab yyi karfin halin cewa “Ehh” Duk suka amsa da maa sha Allah, Ita dai Jiddah kanta na kasa, Abba yace “And there is nothing wrong with her, Allah ubangiji ya baku xaman lafiya” Sae a sannan Jiddah ta dago tana kallon Abba, Abuturrab dae ya kasa dago kansa, nasiha dattijan suka shiga yi masu a tare, Jiddah dai sae bin su take da kallon don gaba daya bata gane inda suka dosa ba, a xatonta wanda aka ma aure ake yi ma irin wannan maganganun da suke mata, ya xa ayi ta bi shi kamar yanda suke cewa, tayi masa biyayya sannan tayi hakuri, Abuturrab dai ya ki dago kansa, Sun fi minti talatin suna abu daya daga karshe suka masu addu’a da fatan Allah ya kade shaidan a xamansu, A hankali Abuturrab ya dago yace “Ameen nagode Abba” Kudi ko wannensu ya ciro ya mika mata ta ki amsa tana kallonsu duk kana ganinta kasan she is confused, Abuturrab ya daga kai ya kalleta, can ya karasa ya amsa kudaden, Uncles din nasa suka ce ya siya mata duk abinda take so, ya amsa masu da in sha Allah, Abba yace “Yau din xa ku wuce can gidan naka, amma kafin nan ka kira mai martaba” Kai kawai Abuturrab ya gyada masa a hankali, sannan ya mike yana kallon jiddah, k’in tashi tayi, Alhaji Ibrahim ya mata murmushi yace “Tashi ku je, Allah yayi maki albarka” Mikewa tayi, Alhaji Lawal yace “Ya sunan nata?” Ta sunkuyar da kanta Abuturrab ya d’an fara kame kame yace “Ummi ce…” Abba ya d’an yi murmushi yace “Hauwa sunanta” Duk suka amsa da maa sha Allah, Alhaji Lawal yace “Baki da matsala a rayuwa idan kika yi halin me wannan sunan ta gidan nan, A very simple life” murmushi kawai Abba yayi, Abuturrab ya nufi kofa Jiddah ta juya ta bi bayansa, sai da suka fita ya kulle kofar yana mata wani irin kallo yace “Ke wace irin dakikiya ce ana maki magana kiyi ta kallon mutane kamar wawuya kiyi shiru…” Kallonsa kawai take da manyan idanuwanta ko kiftawa babu, ya nuna mata parlon fuska daure yace “Koma kiyi masu godiya ko ajiya kika basu kudin da suka baki?” Ba musu ta juya ta bude kofar ta shiga parlon, duk kallonta su Abba suka tsaya yi, ta tsugunna hawaye har ya kawo idonta cikin sanyin murya tace “Abba nagode Allah ya saka da alkhairi” Duk suka amsa mata da Ameen, suka kara sa mata albarka sannan Alhaji Lawal ya umarceta da ta tashi ta wuce, mikewa tayi ta nufi kofa ta bude ta fita ta rufe masu kofar, tsaye ta tadda Abuturrab bakin kofar yana jiranta, ta sunkuyar da kanta, ya fara tafiya, bin bayansa tayi tana tafiya a hankali, babu kowa parlon, ganin xai hau sama ta nemi waje parlon ta xauna, kamar ance ya juya ya ganta ta xauna a parlor, hade rai yayi sosai yana kallonta, ta mike tsaye ita ma tana kallonsa, yace “Xo ki wuce” Ta nufesa gabanta na faduwa, sai da yaga ta kusa iso shi sannan ya fara tafiya, tana biye da shi har suka isa dakin Aunty, Kulle kofar yayi bayan Jiddah ta shigo, Aunty ta tamke fuska ganinta, ya xauna kan stool din gaban mirror yana kallon Aunty a hankali yace “The lady…” Aunty ta wani ta6e baki hade da tafe hannu tana