JIDDAHTUL KHAIR 16
Jiddah dai na tsaye bakin kofar parlon tana share hawayen da ya ki tsaya mata, saman kujera Abuturrab ya xauna bayan ya ja center table din parlon right in front of him, ya daura takardan a kai ba tare da ya kalleta ba, babu yabo babu fallasa yace “Shigo ciki…” A hankali ta karaso cikin parlon tana share idonta, ta rakube jikin one sitter din parlon ta tsaya tana kallonsa, daga kai yayi ya kalleta ya nuna mata kujeran alamar ta xauna, ta xamo kasa ta xauna, bayan few seconds, speaking calmly yace “Shekaranjiya na gaya maki an daura maki aure, right?” Jin tayi shiru ya ajiye biron hannunsa yace “Tambayarki nake” Ta gyada masa kai tana kallonsa, yace “Kuma baki san da wanda aka daura maki auren ba ai koh” Nan ma ta gyada masa kai, a takaice yace “Ohkk… Da ni aka daura auren” Kallonsa kawai Jiddah take kamar bata gane abinda yake nufi ba, not minding that ya langwabar da kai yace “Shi yasa kika ji a can gida suna maki nasiha” a hankali Jiddah ta sauke idonta kasa, taji xuciyarta na bugawa da sauri da sauri, yace “Na aure ki ne kawai don ceto rayuwarki daga matar mahaifin ki, na aure ki ne saboda naga xa a cuce ki xa a lalata maki rayuwa, na aureki ba don naje da niyyar yin hakan ba, don haka bani da xabi da ya wuce in sakeki, wannan sakin kuma da xan maki tsakanina dake ne kawai….” Da duk idanuwanta take kallonsa jin furucinsa na karshe, cikin sanyin murya tace “Xaka sakeni?” Yace “Ehh xan sake ki” Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, shi ma shirun yyi yana kallon hotonsa dake parlon yana sanye da wear dinsa na pilot, muryarta ya ji tace “Idan ka sakeni sai in koma wajensu Umma kenan?” Ya girgixa kai, cikin nutsuwa yace “Aa a nan gidan xaki xauna, kamar yanda na fada maki sakin nan xai kasance sirri tsakaninmu, babu wani da xai san na sake ki….” Tayi shiru bayan few seconds tace “Toh ae ni ba muharramarka bace da xa mu xauna gida daya bayan ka sakeni….” Kallonta ya dinga yi da mamaki jin furucinta ba don shi ta fada ma ba idan wani yace masa ta fadi hakan baxai ta6a yarda ba, can yace “A ina kika san wannan?” Tana wasa da fingers dinta ba tare da ta kallesa ba tace “Lokacin da nake xuwa islamiyya” Surprisingly yake ta kallonta, can yace “Ohh i see… amma kuma basu koyar dake hukuncin wanda ya kashe kansa ba kuma?” Kallonsa Jiddah tayi amma taki cewa komai, ya jefa mata wani shegen kallon da yasa ta koma baya a hankali, idonta har ya fara kawo ruwa, yace “Ke a tunaninki rashin sakin ki kadai ne xai sa mu xauna gida daya kenan, idan ban sakeki ba shine kike muharramata koh?” Shiru tayi bata ce komai ba yace “Bude baki ki bani amsa malama” A hankali tace “Nima ban sani ba” Wani kallo ya sake jefa mata ta sunkuyar da kanta, yace “Xan sakeki kuma xa mu xauna gidan nan tare, don mun xauna gida daya tare ba yana nufin ganina xaki dinga yi ko ganinki xan dinga yi ba, kinsan matsayinki gidan nan, nima haka, balle ma ni daga ranan lahadi da yamma xuwa juma’ah ina wajen aiki, kina tunanin sati da lahadin ma idan na dawo ganina xa ki dinga yi??” Ita dai bata ce masa komai ba, yace “Don haka ki cire tunanin yan kauye dake ranki yanxu, komai kike bukata xan baki waya da xa ki dinga kirana, sannan idan ba abu me ma’ana ba dama kar ki kuskura ki kirani, nan da wani lkci xaki fa islamiyya da boko….” Sai a sannan ta daga kai ta kallesa cikin sanyin murya tace “Toh nagode Allah ya saka da alkhairi” Bai tanka ta ba ya soma rubutu a takardan gabansa, kallonsa kawai Jiddah take babu ko kiftawa, yayi rubutu wanda iyakarsa layi biyu xuwa uku sannan ya dago kai yana kallonta, da sauri ta sauke idonta kasa, yace “kin iya karatu?” A hankali ta girgixa masa kai, sai kuma ta gyada masa kai alamar xata iya, ya mika mata takardan yana kallonta, ta mike ta karasa ta d’an risina ta amsa takardan tana kallo, bayan few seconds ya mika mata hannu alamar ta basa takardan, ta dago kai, hawaye ya gani makale idonta ta mika masa takardan ya amsa sannan ya linke without looking at her yace “Wannan tsakaninmu ne da ke, har abada bance ki sanar ma kowa ba idan ba haka ba……” Daure fuska yyi yana kallonta bayan ya fadi haka, ta gyada masa kai a hankali hawayen idonta ya silalo, mikewa yayi ya linke takardan tsaf sannan ya shiga bedroom dinsa ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya fito, kofar fita ya nufa yace “Mu je in nuna maki dakin da xaki xauna” Juyawa tayi cikin sanyin jiki ta bi bayansa, bangaren suka bari gaba daya, ya bude wani daki wanda akwai komai a ciki yana kallonta yace “Ga dakin ki nan, kinga can bangaren nawa ko by mistake, kinsan me nake nufi da by mistake?” Ta girgixa masa kai alamar A’a, yace “Ohk, ina nufin ko bisa kuskure kada ki kai kafarki can, iyakar ki nan dakin, ko parlon kasa idan ina gari bana son kina xama, idan bana nan xaki iya xaman ki can, sai kuma kitchen, komai xan ajiye maki a ciki ki girka duk abinda kike so” Ta gyada masa kai kawai, yace “Yanxu ki tafi kasa jakar nan ki kawo dakin ki, gobe da safe xa mu fita xan siya maki duk abinda xaki bukata, sai ki xaba komai da kanki” Nan ma kai kawai ta gyada masa yace “Kin ci abinci ai a can gida?” Ta gyada masa kai nan ma, yace “Good” downstairs ya nuna mata yace “Tafi ki dauko jakanki, kayan da xaki dinga amfani dasu ne a ciki” Ba musu ta fara sauka kasa, ya bi bayanta suna shigowa parlon ya nufi kofa ya sa makulli, ta dau jakar ta koma sama, kashe wutan parlon yayi, sannan shi ma ya wuce saman, tsaye ya ganta bakin kofar dakin da ya nuna mata, a hankali tace “In shiga?” Ya daure fuska yace “Ehh” Bude kofar tayi kafin ta shiga ciki yace “Gobe karfe takwas xa ki sauko kasa” Ta gyada masa kai, sannan ta shiga dakin ta kulle, ya kashe wutan corridor din ya nufi bangarensa. Bin dakin da kallo Jiddah ta dinga yi, sai take ganin abun kamar a mafarki wai yau ita ce xata kwanta saman wannan katon gadon ita kadai, to ko dai bai ce ta kwanta ba? Kar ta kwanta kuma yace mata don me, a hankali ta kai jakar can jikin bango ta ajiye sannan ta dawo ta xauna kasa tana sake bin dakin da kallo, ta fi minti talatin xaune a kasa, can ta tuna abinda Umma tace mata duk dare kafin ta kwanta ta dinga yin wanka, mikewa tayi tana kallon jakar da yace mata kayan da xata dinga amfani da ne a ciki, ta karasa gun jakar ta kwantar sannan ta bude, tawul ta fara cin karo da sabo, ta ajiye gefe, taga sabulu da soso da Toothpaste and toothbrush, su ma ta ajiye a gefe, sannan taga sabbin undies, da turarruka da mayyuka sai kayan kwalliya, kallon kayayyakin ta dinga yi, lkci daya hawaye ya kawo idonta, xaunawa tayi nan kasa ta hade kai da gwiwa tana shessheka, gani take kamar Hansai xata xo ta haureta ko ta watsa mata ruwa sai ta farka taga duk mafarki kawai take, ta fi minti sha biyar tana kukan kafin ta dago kanta har sannan hawayen yaki tsaya mata, ta dinga share idonta daga bisanni ta mike ta cire Hijab din jikinta, kamar yanda Umma tace mata bata ajiye Hijab din haka ba sai da ta linke, sannan ta soma cire kayan jikinta, ta dau tawul din ta daura ta shiga bandaki, tun daga gidan Umma su Huraira da Maimuna sun nuna mata yanda ake amfani da komai na cikin bayi, cikin kankanin lkci kamar ana koranta tayi wanka ta fito bandakin, bayan ta gama goge jikinta ta dau lotion daya ta bude ta fara shafawa, wani doguwar riga mara nauyi duk da ba na bacci bane ta dauka ta saka, sannan ta maida komai cikin jakar ta rufe ta mayar jikin bango, darduman da ta gani ta shimfida don tayi alwala, ta gabatar da sallan isha sannan ta linke darduman da hijab din ta ajiye, komawa tayi ta rakube ta xauna a kasa, tana ta xaune tana tunani iri iri, taji bacci ya fara fixgarta, tsoron hawa saman gadon take yace tayi laifi, hakan yasa ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta kwanta nan kasan tiles ta dukunkune waje daya, nan da nan bacci ya dauketa, sai dai kafin asuba ba karamin wahalar da ita sanyi yayi ba, baccin ma bata yi me dadi ba sbda sanyi da ya isheta, a haka har aka kira sallan asuba, abun ka da wanda ya saba, tun kafin a tada sallah ta tashi ta tafi bandaki ta dauro alwala, da kyar take numfashi sbda hancinta da taji ya toshe, ga ciwo da kanta ke yi, tana xaune saman darduma bayan ta idar da sallah aka bude kofar dakin, da sauri ta juya suka yi ido hudu da shi, sanye yake da jallabiya, ta sunkuyar da kanta, ya rufe kofar ya nufi bangarensa, sai a sannan ta dago kanta jin ya rufe kofar dakin. Har gari ya waye Jiddah na xaune saman darduma sai dai fa babu abinda take, ko d’an azkar din nan babu, kawai sabo da tayi da rashin komawa baccin asuba ne, bakwai saura ta mike ta shiga bandaki ta wanke baki tayi wanka sannan ta fito, wani atamfar ta saka bayan ta shafa mai ta saka turare dai yanda ta ga su Maimuna na yi, tana ta xaune dakin lkci lkci tana duba agogon dake dakin, har taga karfe takwas yayi, mikewa tayi ta dau Hijab ta saka sannan ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, kamar mara gaskiya ta dinga sauka stairs din har ta iso main parlor din, karan Tv ta ji, ta leka parlon ta gansa kwance saman dogon kujera idonsa a lumshe, kasa karasawa tayi cikin parlon, ta fi minti goma a tsaye kamar munafuka, daga karshe ta juya a hankali ta koma saman, xaunawa tayi a kasa ta jinginar da kanta da gado, tana ta xaune a haka har bayan awa kusan daya taji an bude kofar dakinta, da sauri ta juya, suna hada ido ya daure fuska yace “Baki san agogo bane?” Ta kalli agogon dakin dake nuna karfe tara saura mintuna kadan, a hankali tace “Na sauko karfe takwas naga kana bacci shine na koma” da mamaki yake kallonta, can yace “To meye damuwarki da baccina ba ni nace ki sauko lkcn ba?”