JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDAHTUL KHAIR 16

Ta gyada masa kai, juyawa yayi ya bar bakin kofar, ta mike tana gyara hijab din jikinta ta bi bayansa, xaune ta samesa a parlon ta karasa ta rakube kasa jikin kujera ta xauna yana kallonta daga sama har kasa yace “Babu wani Hijab din ne a jakar?” Tace “Akwai” Yace “To bana son maimaita kaya… Koma ki canxa hijab din” Mikewa tayi ta wuce sama a sanyaye, ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da wani Hijab din navy blue colour, shi ma har kasa, sosai Hijab din ya haskata kasancewarta fara, ta koma inda take ta xauna ba tare da ta kallesa ba, bayan few minutes yana kallonta yace “A gidanku idan an tashi da safe ba a gaisuwa?” Ta d’an buda ido tace “Ina kwana” Bai tanka ta ba yana kallonta jin voice dinta da ya canxa yace “AC din dakin kika kunna?” Da sauri tace “Aa ai ban iya kunnawa ba” Yace “Da ruwan sanyi kika yi wanka?” Ta girgixa kai tace “Aa na xafi na tara” Yace “Kin bude windows din dakin ne?” Nan ma ta girgixa kai tace “Ban san ma ya ake budewa ba” She looks so Afraid, don with authority yake mata tambayar, bayan ya gama kallonta da kyau yace “A ina kika kwanta?” Tana jan fingers dinta a hankali tace “A kasa” Da mamaki yake kallonta, can dai yace “Saboda me?” Innocently tace “Ai baka ce in hau saman gadon ba” Dauke idonsa yayi daga kallonta, bai ma san wani reaction xai yi ba, she sounds very funny, can dai ya sake kallonta yace “To daga yau nace ki dinga hawa saman gadon, anjima da daddare xan baki bargo da xaki dinga rufa” Cikin sanyin murya tace “Toh nagode” ya nuna mata basket me dauke da breakfast da Umma ta aiko masu da shi, yace “Ga ya can ki je ki karya” Ba musu ta mike ta isa wajen, babu abinda babu wajen har cup da spoon da plate, ganin yanda take ta kallon basket din bayan ta duka a wajen yace “Ki bude dukka ki xuba abinda kike so” A hankali ta shiga bude warmers din, wainar shinkafa da lafiyayyen miyarsa na naman rago, sai fried Irish da kwai, ga kuma bread da pepper soup din hanta xalla, kallonta kawai yake, ta dau plate ta debi waina biyu xata kara daya suka hada ido, mayarwa tayi, yace “Juye dukka” Da sauri ta kallesa tace “Ya min yawa ai” Ya hade rai yace “Juye nace” Ta kalli wainar da xai kai sha uku tace “Wllh tllh baxan iya cinyewa ba” Hade rai yayi sosai yana kallonta can on a serious note yace “Bana son rantsuwa a gidana, kada ki sake” Sauke kanta tayi ta xuba wainar guda biyar sannan ta debi miya, xata mike yace “Hada shayin” Ta hada shayin ta koma can jikin kujera ta xauna, lkci lkci take satan kallonsa tana cin abincin gabanta, daga karshe ya mike ya wuce sama ganin she isn’t comfortable, ta bi sa da kallo. Bayan kusan awa daya Abuturrab ya sakko rike da makullin motarsa, kananun kaya ne jikinsa as usual, Jiddah na ta xaune bayan ta gama wanke plate da cup din da ta karya a kitchen, kashe tv dake aiki yayi ya kashe fitilan parlon ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa yace “Ki sameni waje” Mikewa tayi ta bi bayansa, takalmanta ta gani bakin kofar fita ta saka sannan ta fita, yana tsaye waje yana jiran fitowarta, tana fitowa kuma ya kulle kofar da makulli ya nufi can gate, ya bude gate din sannan ya karasa parking lot ya bude motarsa ya shiga, slowly take tafiya har ta iso parking space din, ya gama warming motar sannan ya kalleta yace “In roke ki kafin ki shiga motar?” Bude back seat tayi ta shiga, bai dai ce mata komai ba ya fara driving ya fitar da motar kofar gida, sannan ya sauka ya kulle gidan ya koma cikin motar, Driving Abuturrab yake yana tunanin shopping mall da xa su, daga karshe ya dau hanyar ASD city mall, suna isa yayi parking ya bude motar ya sauka, Jiddah ta sauka ita ma, don yanxu kam ta iya bude mota, ganin inda ya nufa ta bi bayansa, shopping cart ya dauka tana biye da shi, wajajen turarruka ya fara nufa ya tsaya ya rungume hannu yana kallonta babu yabo babu fallasa yace “Debi turaren” tace “Ai a jakar kayan nan akwai turare hudu” Wani shegen kallo yayi mata yace “Debi turare nace my frnd” Diban turaren ta fara yi wanda wasu body sprays ne a wajen tana xubawa a cart din, takaici ya sa ya ma kasa ce mata komai, she’s not even making any effort to check for the ones with better scent diba kawai take, cikin husky voice dinsa yace “koma gefe” A hankali ta ja ta tsaya a gefen tana kallonsa, gun sealed tsadaddun turarurruka ya karasa ya xabi hudu ya xuba a cart din, a takaice dai turaren da suka diba a wajen xai kai kala sha uku kamar abinda kadai ya kawosa mall din kenan, dubu dari biyu Abbansa yayi masa transfer a yau da safe yace ya siya mata duk wani abinda take so, ga wanda uncles dinsa suka bata a jiyan, gun mayyuka ya nufa next tana biye da shi tana tura cart din da ya sakar mata, wayarsa ya ciro aljihu yayi dialing number Aneesah warce har yau bata san abinda ke faruwa ba, yasab Aunty ma baxata yi gigin sanar mata ba, shi ma kuma bashi da intention din sanar mata, tana dagawa cikin cool voice dinsa yace “Aneesah wani cream kike shafawa pls?” Daga daya bangaren tace “Ohh body cream?” Yace “Yeah” fada masa tayi, ya d’an yi shiru har sai da tace “Are u there?” Yace “Yeah, amma ba na lightening bane ko?” Daga daya bangaren tayi dariya tace “To ka mance ni fara ce, lightening din me kuma my captain?” Kallon Jiddah dake tsaye ta rakube waje daya yayi, yace “ohk, haka ne” Tace “Ba na bleaching bane kamar yanda kake tunani, amma kuma me kyau ne, yana fito da ainahin complexion din mutum, sannan yana sa jiki yayi glowing, me tsada ne sosai” Abuturrab ya d’an yi murmushi yace “Ohk, text me the name now ina jira, and sorry…. Har da sabulu, infact da duk wani abinda kike amfani da shi na gyaran jiki ki turo min ta text ynxu” Tace “Uhmm my Captain lefe ka fara hadawa ne?” Bai san lkcn da ya fara murmushi ba yace “Yea, with perfumes da kike amfani da” Farin ciki ne sosai a voice dinta, tace “Alright my captain, i will now” daga haka ta katse wayar, jan cart din yayi suka tafi bangaren undies kafin Aneesah ta turo masa text din, gefe ya ja ya tsaya ya rungume hannunsa yana kallonta yace “Ko shi ma ni xan xabar maki?” Kasa kallonsa tayi wai duk kunya, ta sunkuyar da kanta inda take tsaye, yace “Heyy kina bata min lkci” A hankali ta karasa ta fara daukan panties din tana ajiyewa a cart din, ya hade rai yace “Idan kika dauki wanda suka fi karfin ki kina da wanda xaki ba ma ne?” Kasa kallonsa tayi kamar xata yi kuka, yace “Madam kina bata min lkci fa, baxa ki dinga dubawa ba….” kamar xata yi kuka tace “Ni baxan iya ba” that sounds so funny, amma ya dake yace “Baxa ki iya me ba?” Juya masa baya tayi, bai san lkcn da ya d’an yi murmushi ba, karasawa yayi ya gun undies din, daga sama har kasa ya kalleta doing survey with his eyes, ita dai ta ki juyowa, da kansa ya xabar mata undies din ko wanne dozen dozen, ya tura cart din ya bar ta wajen a tsaye, satan kallonsa tayi, sai kuma ta fara bin sa a hankali, gun nighties ya tsaya nan ma ya xabi sha biyu…. Kananun wears ma ya xabar mata isassu, ganin she is already tall, flat shoes iri iri masu kyau ya xabar mata shi ma dai kusan sha biyu, da handbags, a mall din nan atamfofi ne kawai Abuturrab bai siya mata ba, komai da mace xata bukata sai da ya siya ma Jiddah enough a lkcn, sai dai idan cart din ya cika ya ajiyesa sa can gun da xa abiya kudi ya dau wani shopping cart din, Creams da sabula da turarrukan da Aneesah ta turo masa ne karshen abinda ya duba a mall din, kala uku ya dau mata cream din da sabulu da shower gel, turarruka kuwa kala biyar kawai ya kara mata har da miski a ciki, a mall din Abuturrab yayi azahar, Jiddah dai iya gajiya ta gaji, bayan ya biya duk kudin kayan an kai masa mota ya nufi bangaren cin abinci dake cikin mall din, Jiddah dai na biye da shi, xaunawa yayi ya nuna mata table din dake opposite din wanda ya xauna yace “Can xa ki xauna” Karasawa tayi ta xauna wajen tana kallonsa, fried rice yayi ordering da kaza sai Chivita da bottle water, bayan an kawo masa abincin a gabansa ya juya ya kalleta, da sauri ta sunkuyar da kanta, yace “Me xa ki ci” Ta girgixa masa kai tace “Aa na koshi” Wani shegen kallo ya jefa mata yace “Me xa ki ci nace?” Kasa cewa komai tayi, ya kalli waitress din ya umarceta da ta kawo mata exactly abinda ta kawo masa amma takeaway xata yi, waitress din na wucewa ya soma cin abincinsa, lkci lkci Jiddah ke satan kallonsa, cikin rashin sa’a suka hada ido, da sauri ta kauda kanta, shi dai ya ci gaba da cin abincinsa, Waitress din ta kawo abincin ya amsa ya ajiye kan table dinsa, sai da ya gama cin abincin sannan ya mike ya saka sauran drink din da bottle water a ledan abincin dake kan table din, cash ya ba waitress din har xai fara tafiya ganin jiddah bata taso ba yace “In xo in daga ki ne malama” Mikewa tayi xata wuce ya nuna mata ledan yace “ohk bar masu abincin xa ki yi” bata ce komai ba ta dauki ledan ta bi bayansa, suna isa gida da kansa ya dinga kwasan kayan yana kai wa parlor har ya gama, tana tsaye kamar wawuya bakin kofa sai dai ta basa hanya, har ya gama shigar da kayan yayi xamansa a parlor yyi powering Tv, jin bai ce ta shigo ba taki shigowa parlon, bayan kusan minti sha biyar ya mike ya isa bakin kofar yace “Ke wai baki da hankali ne dama ban sani ba? Meyasa kike behaving kamar yar kauye?? Yanxu me kike yi a nan a tsaye” Kamar xata yi kuka tace “Ai baka ce in shigo ba” Ya mata wani shegen kallo yace “Get out my frnd, sai nace ki shigo, idan kina son xaman lafiyar ki a gidan nan ki daina behaving kamar wawuya” Har hawaye ya kawo idonta ta bi ta gefensa ta shiga parlon, bata san dama kayan da ta bar sa da shi yake ta kwasa tana kallonsa ba ya basa haushi, tsaye tayi parlon tana tunanin ta wuce sama ko ta tsaya, ganin kallon da yake mata ta juya da sauri ta nufi sama, yace “Dawo nan” Dawowa tayi yace “Kwashi duk kayan nan ki wuce da su sama dakin ki” Daukan ledojin ta dinga yi daya bayan daya tana kai wa dakin nata har ta gama, ta dau na karshen xata wuce ya dawo da ita ya nuna mata ledan abincin durkusawa tayi ta dauka sannan ta wuce sama yace “Idan kin je saura ki ajiye abincin ki jirani in xo ince ki ci” Bata ce komai ba a sanyaye ta wuce sama ta shiga dakin ta kulle.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button