JIDDATUL KHAIR 47
Abuturrab yayi mata ya ki daina dawo mata, ganin abun yake kamar afresh, Cike da damuwa Hajja tace “To ko dai wani mugun abun ta maki naga duk a firgice kike wllh, ki gaya min gaskiyar me ta maki Jiddah” Jiddah ta lumshe ido ta bude a karo na farko ta bude baki a hankali tace “Bata min komai ba” Hajja tace “Oho dai ita da Allah ni dai na gaya mata duk abinda ya kamata ta sani” Tana fadin haka ta sake fita daga dakin, Jiddah ta ji hawaye ya kawo idonta ta kai hannu bakinta da take jin kamar bai cire nasa ba har
sannan, ita idan ba a tv ba bata ta6a sanin ana haka a reality ba ma, hancinta ta kai kayanta jin kamshin turarensa ya cikata, ta wani turo baki ta mike ta fara cire kayan, sai da ta cire tas sannan ta saka hijab ta kwanta tayi lamo saman gadon, scene din da bata so na sake dawo mata kamar a lkcn yake faruwa. Aneesah na xaune parlon kawarta Chef Salma, Salma tace “Kan bala’i!!! to ai ni duk a xancen ki babu
abinda ya tsaya min irin yarinyar da kika ce ta biyo kakar tasa… Ita yar kauyen da ya saka ce ake miki sintirin xuwa gidan ki da ita? Sannan kuma ta bi ki da sharri haka? To me hakan ke nufi?” Aneesah ta fyace majina da handki din hannunta tace “Ai shine nake jiran kiran stepmom din tasa, wllh ni rabona da su gaba daya tun xuwansu da rana da nayi shigewata parlonsa, ban ganta ba balle har wani abu ya hadani da ita, amma ban san me taje ta gaya ma makirar tsohuwar ba ta shigo har bangaren mijina tayi min wankin
babban bargo ta ci min mutunci” Salma tace “To kuma ai kinyi wauta barin gidan da kika yi, bar masu gidan fa kika yi kenan” Aneesah ta fashe da kuka tace “Captain din fa ce min yayi in tafi sai da safe” Salma tace “Toh ai dadi kakar da ita tsinanniyar yarinyar xa su ji, ke dai wani lkcn idan kinyi wani abun kamar er fari, ke da gidanki kawai ki hado kaya ki bar masu, wato sun ma ci nasara a kanki, sannan karyar da ita yarinyar tayi ma kakar Captain din ya xama gaskiya kenan tunda har kika bar gidan” Aneesah tayi wani
murmushi tana girgixa kafa, Salma ta ta6e baki tace “Wllh sakwa sakwan da kike ma wnn pilot din yayi yawa, sai kace shine autan maza? Shi yasa har ya iya budan baki ya maki maganar banxa, banda kilan suna da wani kudurin a ransu meye na xuwa da yarinyar da ya saka gidan tun tale tale? Me ya kawota bayan ga kanninsa da cousins dinsa da xasu iya rako tsohuwar, to wllh ki farka daga wnn slumber din naki kina da aiki ja a gaba, da kyar idan ba sake cusa masa me dankali da doyan xa su yi ba” Aneesah ta sakko da
kafarta daga saman kujera da sauri alamar xancen ya gigitata tana kallon Salma, er dariya tayi tace “Ka ji ki da wani xance, to babu wani aure tsakaninsu sai in ta sake wani auren, ya mata saki sau uku kenan, daya a lkcn auren na farko farko, sannan suna tare ma ya saketa, sai na karshen da Abbansa ya umarcesa da ya saketa kuma ya saketa din” Salma tace “Ke wa ya gaya maki haka?” Ta gyara xama tace “Aunty, kuma
Aunty Safara’u ma taje wani waje haka aka ce mata babu aure tsakaninsu har abada, don haka mu kwantar da hankalinmu, balle ma captain ba class dinta bane shi ma ya sha fada, me xai ci da ita?? yar hayin rigasa ce fa bama birnin hayi ba kauyen hayi, ko numfashinta baxai so ya shakka ba balle wani abu ya hadasu” Salma tace “To har naji hankalina ya kwanta maki, da kika ce babu auren, amma duk da haka sai kin taka burki a daina taho maki da ita gida gaskiya, ba fa dangin iya ba na baba” Aneesah tace “Ita
kanta tsohuwar xuwanta na farko da na karshe kenan tayi idan anyi duniya don manzon Allah, wllh ko da kudi aka hadota ta taho gidan Aliyu baxata sake xuwa ba” Salma tace “Yauwa, haka nake son ji dama, ki tashi xaune daga kwancen da kike wllh… Yanxu kowa ta kansa yake duk inda kika ji ance aiki na kyau ki cire kyashin kudi kije” Aneesah ta jawo wayarta ta daga ganin Aunty ke kiranta ta kai kunne da sauri, kuka ta sakar mata, nan kuma ta bata labarin duk abinda ya faru, Aunty da ta kakance idonta tace “Kina nufin
tare da shegiyar taje maki gida?” Aneesah tace “Wllh kuwa” Aunty tace “Toh ke banda shashanci meye na barin gidan, wato Hajjar taji dadi kenan ma kin bar masu gidan” Aneesah tace “Aa wllh Aunty ni baxan iya xama ba suna ci mun mutunci kuma babu abinda Aliyun yace, sannan da kansa yace in tafi” Aunty tace
“Toh abinda xai faru yanxu ki dauko jakar taki ki taho nan gida, Abbansa na gari ai, maza ki taho yanzu, kuma wajen maida magana duk ki san abubuwan da xaki kara a xancen, ai in sun san wata basu san wata ba” Aneesah tace “Toh” Aunty tace “Wai ya ma baki wannan kudin kuwa?” Aneesah ta tabe baki tace “Ina fa, ce min yayi sai sabon wata da xa a shiga…” Aunty tace “Anya Aneesah kinyi amfani da maganin karshen da na baki a daren ku na farko kuwa?” Aneesah tace “Aunty sai dai na xo gidan, yanxu xan fito dama gidan Salmah na taho” Aunty tace “To na gane, taho gidan maxa yanxu” Driver Salmah ta saka ya kai Aneesah can gidansu Abuturrab. Har wajen karfe sha daya Abuturrab na xaune downstairs tare da Hajja da babu irin labarin Masar da bata masa ba, with much interest yake sauraronta yake biyeta duk da labarin ba dadi yake masa ba, ya gyara xama yana kallon agogo yace “To ai nan ma akwai turarruka masu kamshi ba can kadai ba” Hajja tace “Inaaa har yau banji turare me kamshi irin ta Masar ba, akwai wani
turare da Usman ya bani wai dubu hamsin ya siya ni dai yana can na jefa cikin kwambodi…. to ba kamshi” Yace “Toh bari in dauko maki wani turarena yanxu ki ji kamshinsa ko ya kai na Masar din” Mikewa yayi
yace “Ki jirani yanxu in dauko maki” Hajja tace “Toh yi maza, kaga idan kamshin ya min sai ka bar min kawai” Yace “Ba damuwa” Daga haka ya haura sama, gently ya murda kofar dakin ya bude, kwance take saman gadon ta rufe duk jikinta da hijab dinta idonta a lumshe, ya karasa cikin dakin ya kulle kofar, kallon switch din dakin yayi kafin ya nufeta walking slowly ya tsaya kusa da gadon yana kallonta, ya kalli kayanta da ta linke ta ajiye sannan ya kara kallonta, daga hijab din da ta lullube jikinta yyi yaga babu abinda ke
jikinta sai undies, lkci daya ya sake hijab din ya juya ya fita dakin ya tafi bangarensa yana shiga bedroom dinsa ya kashe wutan dakin ya fada saman gado yayi rub da ciki. Hajja ta gaji da xama, ta sha gyangyadinta har ta gode Allah sannan ta mike wajen karfe daya ta wuce sama tana cewa “Gantalallen ba sai yace min bacci yake ji ba sai da safe, me hali dai baya fasa halinsa kawai…” Tana bude kofar daki taga Jiddah durkushe kusa da gado ta hade kanta da gadon, Hajja tace “Meye haka?” Ta dago da kyar tana
kallonta ta girgixa mata kai, a fusace Hajja tace “To meye kika wani rungume gado kamar me nakuda?” Jiddah dai ta kasa ce mata komai, Hajja tace “A gaskiya da na sani baki biyoni ba, daga abun arxiki? Me ya sameki?” Jiddah ta kara girgixa mata kai kawai, Tabe baki Hajja tayi ta Kashe wutan dakin tace “Baxan iya da wahalanki ba bacci xanyi wllh, babu wanda xai shiga hakkin bacci na” Tana fadin haka ta kwanta daga
kwanciya kuma sai minshari, Jiddah tayi ta juye juye… tun tana daurewa har ta kasa ta dinga hawaye tana yarfe hannu, rabonta da irin ciwon nan da take ji yanxu tun tana gun Babaarta, har karfe biyu Jiddah na durkushe yanda take, da ya lafa mata sai ya fara kuma… Shesshekarta ya farkar da Hajja, Hajja ta mike xaune sai kuma ta tashi ta kunna wutan dakin, xaro ido tayi ta kalli agogo ta kalli Jiddah sannan ta bude