JIDDATUL KHAIR 47

kofa ta fice, bangaren Aliyu ta nufa ta buga kofa, Abuturrab dake xaune saman kujera a parlon ya rike kansa ya juya da sauri yana kallon kofar, Hajja ta sake bugawa, xai mike daga kan kujeran yayi kicking ruwan Lipton din lemun tsami dake cup a ajiye daga kasa kusa da shi, lkci daya ya malale saman carpet
din parlon, tsallakewa yyi ya nufi kofar ya bude, cikin tashin hankali Hajja tace “Aliyu awa uku kenan wancan yarinyar bata ko rintsa ba, sai kuka take na rasa me ke damunta, ni fa tsorona Allah tsorona tijaran da Ramlah xata min a kanta” Da mamaki yace “Me ya sameta?” Hajja tace “Ina xan sani Aliyu ko kwanciya taki yi, tana can duke kamar me nakuda nayi nayi ta gaya min meye taki” Abuturrab yace “Ina xuwa” Daga haka ya koma daki ya dau jallabiyarsa ya saka sannan ya fito, yana gaba Hajja na biye da shi suka isa
dakin, Yana bude kofar dakin suka ganta durkushe kofar bandaki tana kwarara amai, Hajja tace “Na shiga uku ni Dije ta kashe bandakin, wani aman arxiki ne baxa ta shiga can ciki ba sae a bakin kofa?? Tirrrrr” Abuturrab ya karasa da sauri ya duka kusa da ita yace “What’s wrong with u?” Ta kasa basa amsa ya
dagata xuwa cikin bandakin, Hajja ta fice daga dakin hankali tashe tace “Baxan iya ba wllh, ko ni ya na kare da nawa aman balle na wani…” Abuturrab ya wanke mata fuskarta bayan ya xuba ruwa gun aman, xai cire mata Hijab din jikinta ta rike gam tana xaro ido amma taki yarda ta kallesa, hade rai yayi yace “Cire hannunki” Da kyar cikin kuka tace masa “Aa bana so wllh” lkci daya ya fixge hijab din a jikinta da karfi, ta
turasa ta durkusa a kasa hankali a tashe tana cewa “Wayyo na shiga uku don girman Allah ka bani hijabina ka fita” Yana kallon ko ina na jikinta yace “Me yake damunki?” Duk a gigice take tace “Ai naji sauki” Yace “Saukin me” Taki yarda ta kallesa tace “Don girman Allah kayi hakuri ka fita” Sai kuma ta fashe da
matsanancin kuka tana kara rufe jikinta, shi dai kallonta kawai yake, can ya d’an shafa kansa ya ajiye mata hijab din saman washing machine ya juya ya fita bandakin, banda rawa babu abinda jikinta yake, tun da take bata ta6a ganin irin wannan iskanci ba, ko a gaban mace bata ta6a tsayawa a yanda take yanxu ba, gaba daya ta nemi ciwon cikin da take ta rasa, ta kalli jikinta ta kara takurewa waje daya xuciyarta na
bugawa, ta fi minti biyar a haka kafin ta mike da sauri ta figi hijab dinta ta saka gabanta na faduwa, ta makale jikin kofa sannan ta leka dakin a hankali, ido hudu tayi da shi yana tsaye har lkcn a dakin, da karfi tayi banging kofar bandakin ta sa makulli, ganin haka ya shafa kansa ya juya ya fita, xaune yaga Hajja a corridor din ta shimfida darduma sai xuba gyangyadi take, yayi mata kallo daya ya wuce bangarensa,
throughout daren nan Abuturrab bai rintsa ba, banda juye juye babu abinda yake, idan ya gajiya da kwanciyar saman gadon ya koma kujera a parlor, har aka kira sallah. Karfe takwas Jiddah ta lallaba ta saka kayanta da Hijab tana kallon Hajja dake kwance kan darduma tana bacci, ta dau jakarta ta nufi kofa a
hankali ta bude ta fita, kallon direction din bangaren Abuturrab tayi kafin ta sauka downstairs da sauri, mai gadi ne ya bude mata gate ta fice fittt daga gidan….
[/indeed-social-locker]