JIDDATUL KHAIRNOVELS

JIDDATUL KHAIR 48

tayi a hankali ta nufi kitchen Umma ta bi ta da kallo ganin duk tayi wani irin sanyi. Hajja na shigowa parlon Abba ganin Aunty da Ummi sai Aneesah a parlon ta dinga bin su da kallo tace “Wacece wannan kuma?” Lkci daya Aunty ta murtuke fuska, Ummi tace “Sannu da xuwa Hajja” Hajja tace “Yauwa me ke faruwa a

nan din?” Abba dake xaune shi ma parlon yace “Sannu da xuwa” Hajja tace “Ba batun sannu da xuwa ba, xaman me ake a nan?” Dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon da sallama, tun karfe tara Abba ya kirasa yana nemansa a gida, suna mota kuma yake sanar ma Hajja cewar Abba yace yaje, Kallo daya yayi ma Aneesah da ta sha lullubi da babban gyale wanda da alama Aunty ce ta 6ata, ya dauke kai ya xauna

saman carpet yana kallon Abbansa yace “Ina kwana Abba?” Abba yace “Lafiya lau” Kallon Ummi yayi ya gaisheta, snn ya gaida Aunty da tayi masa banxa, Hajja dai na tsaye kansu kamar soja, Abba yace “Ga kujera Hajja” Hajja tace “Aa bar ni in tsaya abuna, mu da muka sa6a tsayuwa a Masar” Aunty na kallon Abba tace “Alhaji i think we can leave the sitting for now, may be in the evening” Abuturrab ya kalleta

yace “Yau xan koma aiki in sha Allah” Wani shegen kallo Aunty tayi masa tana kallon Aneesah tace “Tashi mu je” Hajja tace “Ta tashi aje Ina? Ina ce k’aran jikana ta kawo ko? to wllh sai kun ga walakanci da tarban tsiyar da matar nan tayi mana ni da Jiddah, ni dai har hawaye sai da nayi a boye don tunda uwata ta

haifeni ban ta6a ganin anyi haka ba a Masar, sannan gida dai in baku labari da muka shiga duk wari, wllh ta rubar masa gida, kitchen kuma dai ya fara wasu irin tsutsa, bandakin gidan duk sunyi gantsa kuka, to banda lalacewar yaran kasar nan daga nayi mata gyara sai ta kawo karata da na jikana har a wani xauna xa ayi meeting a kanmu?? Ehh lallai yau nake ganin lalacewa a Najeriya” Abba dai yyi shiru bai ce komai ba, haka Ummi da kanta ke kasa, Aunty sai tafarfasa xuciyarta yake tana kallon Hajja, Hajja ta ta6e baki tana

gyara yafin gyalenta tace “Hatta abincin da xa mu ci sai da yaron nan ya fita ya samo mana, to ina girki xai yiwu a wnn axabbabben kitchen din duk wari, salon ma mu ci mu tsuge da xawo idan an girka, wllh da ido daya nayi bacci a gidan sbda datti da kazanta, to bari kuji ita yar rakiyar tawa ma da ciwon ciki ta kwana a gidan tsabar kazantar gidan kuma ni nasan hakan na da nasaba da ruwan da muka sha na gidan, yanxu haka tana can baiwar Allahn tana jinya gun uwar rikonta ni dai duk ni na ja mata bani da bakin magana, to idan ba rashin kunya ba shine har xata kwaso kafafuwarta kamar kara tace ta xo kawo kararmu, bayan duk hakurin da jikana ke yi da ita?? Lallai ma, ai ni da Masar har abada jikana na wannan halin, in sha Allahu sai na samar masa mata me tsafta irinsa warce xata dinga gyara masa gida” Abba na kallon Aunty da

turanci yace “Su tashi su tafi kawai da Aneesah” Kamar jira take ta mike ta daga Aneesah suka fice daga parlon tana huci. Hajja ta kalli Abba ta ta6e baki sannan ta kalli Abuturrab da ya sunkuyar da kansa tace “Tashi mu je o, Allah ubangiji ya kawo maka karshen jarabawar nan da kake ciki” Daga haka ta nufi kofa

abunta…. Bayan azahar Ahmad ya shigo gidan Umma, bayan sun gaisa da Umma yace “Su Maimoon sun tafi Islamiyya ne?” Umma tace “Ehh sun tafi Jiddah dai ce bata je ba, bata jin dadi” Yace “What’s wrong with her?” Umma tace “Wai ciwon ciki take, dama jira nake ka xo” Yace “Wani irin ciwon ciki tace?” Umma tace “ka kai ta asibiti kawai, ai nima ba sani xanyi ba” Yace “To Allah ya sauwake” Umma tace “Ameen”

yace “Tana daki ne?” Umma tace “Ehh bari Huraira ta kirata idan ba bacci take ba” Umma na fadin haka ta kirawo Huraira, Huraira ta tafi dakinsu Maimoon, kwance ta tadda Jiddah saman gado tayi shiru, Huraira tace “Ya jikin Jiddah?” Jiddah ta mike xaune tayi murmushi tace “Naji sauki” Huraira tace “Toh Allah ya kara lafiya, Umma na kiranki’ Jiddah tace “Toh” Sannan ta sauka saman gadon, tun da safe bata sake jin ciwon cikin ba, amma gaba daya jikinta a sanyaye yake, hakan ne da Umma ta gani yasa tace ta xauna

gida kawai ta xata duk ciwon cikin ne, Jiddah na fitowa parlor ta xauna kasa ta gaida Ahmad dake kallonta ya amsa da murmushi fuskarsa yace “Ya jikin?” Tace “Naji sauki” Umma tace “Cikin ya maki sauki?” Jiddah ta gyada mata kai tace “Ehh ya daina yanxu Umma” Umma tace “To sannu, Allah ya sauwake” Ta sunkuyar da kanta tace “Ameen” Ahmad yace “Why not ta dakatar da amfani da drugs da aka rubuta maku a

hospital for the meantime Umma?” Umma tace “Kana tunanin shi ke sa mata ciwon?” Yace “Ta dai dau break na wani d’an lkci a gani” Umma tace “Toh shkkn” Yace “Xan siyo mata pain reliever yanxu” Umma dai sai kallon Jiddah take ganin yanayinta, Ahmad yace “Umma gobe kika ce xa a kai ta makarantar ko?” Umma ta kallesa tace “Ehh” Yace “Toh idan xan koma gida sai mu tafi tare da ita, idan ya so gobe da safe

sai mu je makarantar” Umma tace “Daga nan din baxa ka iya xuwa ka dauketa ba?” Yace “Toh shkkn Allah ya kai mu” Umma ta kalli Jiddah tace “Tashi ki je ki ci abinci” Ba musu Jiddah ta mike ta wuce kitchen. Sai kusan la’asar Ahmad ya shirya xai koma gida, bayan yayi ma Umma sallama tace “Shkkn kawai ta dau kayanta kala daya ko biyu ku tafi can gidan din” Yace “Ohk toh” Umma ta tafi da kanta daki wajen Jiddah

ta sanar mata xa su tafi gidan Ahmad tare, ta dau kayanta kala biyu, Jiddah bata mata musu ba tayi yanda Umma tace sannan ta fito parlor rike da jakarta. Huraira dake tunanin har sannan Jiddah bata jin dadi ne ta amsar mata jakar ta kai motar Ahmad, Ahmad yyi sallama da Umma, jiddah ma tayi mata sallama,

Umma tace “A gaida Ramlah” daga nan suka fita gidan, Suna shiga motar Ahmad yaga missed calls din Abuturrab har uku a wayarsa da ya bari a cikin mota, Sai da ya tada motar yyi reverse sannan yayi dialing number Abuturrab din, yana dagawa Ahmad ya kai kunne yace “Ya aka yi?” Dariya Ahmad yyi yace “Ni fa

wllh kana bani mamaki Captain, ga dai matarka ka bi ka takurani in maka prescription drug? Are u even okay?” Jiddah dake xaune gefensa cikin motar taji gabanta ya fadi jin sunan da ya ambato, Ahmad yace “Toh ka taho gida ka amsa, ina driving yanxu…” Daga haka ya katse wayar yana maida hankalinsa kan titi,

sai da suka yi nisa yace “Kin ma san gidana kuwa Jiddah?” Ta kirkiri murmushi tace “Um na sani, mun je sau uku” Yace “Would u like to stay in my house ki dinga xuwa makaranta daga can?” Jiddah ta d’an buda ido ta kallesa, yace “Yea, sai ki xauna ke da Ramlah koh??”

[/indeed-social-locker]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button