JIDDATUL KHAIR 59
wannan babban gidan Ummi, shikenan saboda bata da iyaye ita marainiya ce sai aka ce bata da gata? Aa wllh tana da gata don yanda na dau su Maimoon haka na dauketa, Hajja taje can ta samar ba Bashir wata matar amma ba Jiddah da ko secondary din ma bata kare ba” Ummi tace “Toh ina ga xai fi ki tashi
kije ki samu Hajja kiyi mata duk bayanin nan, ke wani lkcn kina magana kamar baki san Hajja ba, kin gan ni nan duk fa abinda xai dameni ko ya bata min rai bana so yanxu, ta kaina kawai nake babu ruwana, In dai Bashir din da bakinsa yayi admitting yana son Jiddah kuma xai xauna da ita i see nothing wrong with
that, domin kuwa shi din ba wani xama yake a kasar ba, bini bini ya fita, to ba sai ya tafi da matarsa ba, ina Jiddah xata ga uwarsa idan ba dawowa kasar suka yi ba, kinga wllh yanda kike hakikancewa a batun nan tsaf Hajja xata ce Hassada kike tunda ba er ki bace, don haka ina baki shawara ki bi komai saisa saisa
babu ruwanki…” Umma tace “Aa kiyi hakuri yaya a gaskiya da ruwana, Hajja kuma ba tun yau na saba da tijararta ba, kuma ni kema kin san raga mata nake kawai sabida ke, banda haka ni baxan yi tolerating
haka ba, kuma a gaskiya idan haka abubuwa xa su ci gaba da faruwa gwara ki tafi da Jiddah can gidan don ma kada taga kamar ban tsaya mata ba tunda ni ba uwarta bace.. ki tafi da ita kawai ku yi yanda ku ka ga ya dace da ita, dama ai Hajjar ta sha fada min ba don Aliyu ba a ina xa a santa, don haka ki tafi da ita ku yi mata bayani a can amma ba a nan ba” Ummi dai kallonta kawai take, Umma ta mike tace “Haka
kawai ga gaskiya a dinga takesa kiri kiri, ita Hajjar Allah ce da dole sai an bi abinda tace mata gigin tsufa duk ya rikitata kuma ayi ta bin ta a haka, ba ga jikokinta sa’annin jiddar ba, tayi masu auren mana idan haka ne, kiyi hakuri fa kar kice rashin kunya nake maki Yaya, aa gaskiyata nake fadi, kawai don Jiddah bata da gata a duniya sai a tauyeta?? To dauketa ku tafi kuyi yanda ya dace da ita, babu ruwana”
Mikewa Ummi tayi ta fita daga dakin tayi wucewarta… Bayan tafiyar Ummi da kusan awa daya su Maimoon suka dawo Islamiyya, bayan sun gaida Umma dake xaune parlor xa su wuce dakinsu Umma tace “Da wani number kike waya da Aliyu Maimuna?” Maimoon ta dawo, Jiddah ta d’an saci kallon
Umma sannan ta wuce ciki, Maimoon tace “Da numbersa ne yana shiga” Umma tace “Toh” daga haka ta mike ta wuce dakinta ta hau kiran Abuturrab wayar bai yi connecting ba hakan yasa ta ajiye ta fito… Sai can da daddare Umma ta sake kiransa sai ya shiga, yana dagawa bayan sun gaisa tace “Kana ji na Aliyu?”
Yace “Ina ji Umma” Tace “Ka dai ji abinda iyayenka ke shirin aikatawa ai ko?” Ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Na me fa?” Tace “Ohh duk baka sani ba, to Hajja ta dage ita dole sai tayi ma Jiddah aure da Bashir,
na kiraka ne kuma saboda naga kamar tana jin maganarka, i want u to put a stop to that, ko secondary bana fatan Jiddah ta gama ace xa a aurar da ita, don haka talk sense into Hajja” Abuturrab dai yyi shiru, ta hade rai tace “Ko baka ji na ne?” Yace “Ina ji Umma, xan kirata in sha Allah, nobody told me about it, tace to wa xai gaya maka dama tunda cutar yarinyar ake son yi” a hankali Abuturrab yace “Shkkn, i will
call her in sha Allah” Tace “Do so immediately” Daga haka ta katse wayar ta ajiye lamarin na kara kona mata rai, wai aure kamar xa a aurar da wata mara makabuli, to su yi ta gani. Hajja ta gama sauraron Abuturrab tsaff sannan tace “Toh ko ubanka Usman wanda shine lallai dole ne bai isa yace xai dakatar da ni kan abinda nayi niyya ba, kai kuma a wa Allah na tuba? Kai da ka walakanta yarinya ka cuceta ka
mayar da ita baxawarar karfi da yaji sannan ka saketa? Kai fa ba wani abu ke damunka ba banda kishi, kuma sai dai ka hadiyesa don tayi maka nisa wllh, idan ma sa ka aka yi ka kirana ka koma ka fada ma wanda ya sa ka ai ba Hajjar da bace yanxu, bana nufin er yarinyar nan da sharri banda alkhairi, yanda ta
taso cikin bakar talauci da rashin ga ta so nake ita ma ta ci arxiki ta bar sa a inda ta gansa, so nake ita ma ta shiga babban gida a dama da ita, to na meye kowa sai bakin ciki abinda ni Allah bai daura min ba kenan, to kowa dai ya ci kansa ya kurkure da bakin ruwa, kai kuma ina baka shawaran ka kauda idonka a
kan duk wani abu da ya shafi yarinyar kayi mana me wuyar tunda ka kawota cikinmu” Tana kai wa nan ta katse wayar, Abuturrab murmushi kawai yake yi… Kawai bayan sati daya sai ga shi Aunty ta kira Umma wai an kawo kudin Jiddah daga masarautan bauchi… Ummi ta fi minti talatin rike da wayarta
bayan aunty ta katse, Allah kadai yasan yanda take ji a xuciyarta a lkcn…. Sai yamma ta shirya ta tafi gidan don bata son xuwa ta tadda mutane, ai ko duk yan kawo kudin sun watse, parlon Abba ta shiga direct, yana xaune shi da duk brothers dinsa, Umma ta xauna bayan sun gaisa gaba daya tace “Alhaji Usman dama wajenka na xo” Abba na kallonta ya dau wayarsa yace “Toh Allah ya sa lafiya, in taso ne?”
Tace “Ehh” tana fadin haka ta tashi ta fita, Abba ya mike ya bi bayanta, can kofar gida suka fita tana kallonsa tace “Yanxu Alhaji an xaunar da ita yarinyar an tambayeta ko tana son auren nan da ake shirin kulla mata? Domin bata da kowa ba yana nufin bata da gata Alhaji, this is wrong wllh” Abba yace “Domin
bata da kowa mu ma ba yana nufin xa mu cutar da ita bane, did you know this is a great privilege to her also? Ki duba fa wanda ake son hadata aure da? Wa kike tunanin Hajja xata yi ma hakan banda ita din??” Umma tayi wani murmushi tace “Wato privilege? But she never begged for that privilege Alhaji, idan
kuma xa ayi adalci kamata yyi a ji ta bakinta don a fita hakkinta, an ta6a yi ma mutum dole a aure? Shkkn sai aka ce ita bata da choice da dream dinta?” Abba ya duba wayarsa jin shigowar message yana dubawa yaga message din Abuturrab, and the content goes as thus “Kada ya kasance ana neman Aure ne a kan Aure Abba, that is highly prohibited in islam…. We plan but Allah plans best in sha Allah” Abba ya
karanta text din ya fi sau uku, can ya mika ma Umma dake kallonsa, Umma ta amsa tana dubawa ita ma dai sau ukun ta karanta tana sake duba sender din, a ranta tace Aliyu?? A fili kuwa tana kallon Abba tace “Shashasha, to me yake nufi da text din? Wa ake nema ma aure a kan aure?” Abba yace “I am still trying to understand that too” Umma tace “Ka kirasa” Ba shiri Abba ya hau kiransa amma ya ji layin a kashe, ya
kira sau uku duk a kashe, Umma tace “Wai wa yake nufi ne?? Wa ake nema ma aure kan aure?” Abba yace “Tare mu ka karanta text din nan yanxu Hajiya Ramlah” Umma tace “Toh ina jin shaye shaye ya fara a can din ko” Abba dai bai ce komai ba, Umma tace “Ni dai na gama magana, idan xa ayi mata adalci ayi
mata, a tunaninku gata xa ayi mata tunda xa a aura mata d’an sarki, to amma kwanciyar hankalin xaman gidan auren fa, tunda naji ance uwar tasa ma ba so take ba, kuyi ma Allah a duba lamarin nan idan kuma shakkar yi ma Hajja magana ake ni sai inyi mata wllh” daga haka tayi ma Abba sai anjima ko gidan bata sake shiga ba ta bude motarta ta shiga, driving take amma tunanin solution da xata samar ma Jiddah
take don in dai kuwa aka yi auren nan kilan bata doron kasa ne, samm baxata ta amince da auren ba, baxata ta6a bari a shiga hakkin yarinya ba. Abba na komawa cikin compound ya sa a kira masa Ummi, tana fitowa ya mika mata wayarsa yace “Ko xaki iya fahimtar wani abu a message din nan kiyi min