JIDDATUL KHAIRJIDDATUL KHAIR COMPLETE HAUSA NOVEL

JIDDATUL KHAIR 59

bayani??” Ummi sai karanta message din take da surprise barin da ta ga cewar Aliyu ne sender din, can ta kalli mai gidan nata tace “What’s the meaning of this?” Yace “Shine nake son ki min bayani” tace “Jiddar matar aure ce da xai ce kar a nemi aure kan aure?” Abba yace “Shine nake son fahimta Hauwa” Ummi tace “Ikon Allah, to ka kirasa” Abba na kokarin sake kiransa yace “A kashe wayar” sai gashi ance

wayar a kashe, Ummi tace “Ji d’an rainin wayo, aurar da ita yayi ne ba a sani ba, ko ko?” Abba dai bai ce
komai ba yayi shigewar sa ciki, Ummi ta bi sa da kallo, gaba daya ta ma rasa wani tunanin xata yi, anya kuwa Abuturrab na da kai? Menene manufar wnn text din wai kar a nemi aure kan aure, to ko aure yake nemar ma Jiddar basu sani ba ne. Abba na komawa gun brothers dinsa su ma ya basu wayar su duba message din, bayan sun duba da daddaya da daddaya, suka dinga kallon Abba, Alhaji Salmanu yace

“Neman aure kan aure kuma? To ko dai bai saketa ba ne dama Alhaji Usman?” Abba yayi dariya yace “Ya fara hauka kenan, ai har yanxu takardan na nan bai je ko ina ba” Abba na fadin haka ya mike ya wuce daki sai gashi ya fito da takardan ya mika ma Alhaji Salmanu ya amsa ya karanta sannan ya ba duk sauran ma suka duba, Alhaji Salmanu yace “Ikon Allah, to me yake nufi da hakan? Is he even in his right

senses?” Abba ya daga kafada yace “I thought as much” naxari duk suka yi shiru suna yi, Alhaji Umar yace “Try his line ko xai yi connecting” Abba ya sake kira yaji a kashe, Alhaji Lawal yace “Toh ko dai komawa yayi aka sake daura masa aure da yarinyar?” Kallonsa Abba yayi da sauri almost with shock, sai

kuma yayi wani dariya yace “Aa he must be joking ashe, har ya isa ya sake yin hakan? Da kuwa nayi disowning dinsa wllh… Allah kuwa da ya ga the other side of me, wato ga yan iska ya ajiye, wllh in har hakan ne ya kasance Aliyu xai yi mamakina ainun” Alhaji Umar yace “Ikon Allah, that just dawn on me

bayan Lawal ya fadi haka, in dai kuwa ba shi ya koma ya aureta ba to wani ya kai ya aureta, don babu yanda xai turo wannan message din idan ba dayan biyun abinda na fada ya kasance ba, but that’s bad…

Who does that, ya maida mutane kananun mutane kenan yake nufi ko me?” Abba dai da alama ransa idan yayi dubu ya baci, daukar wayarsa yayi ya tura ma Abuturrab text kamar haka, “call me immediately after switching on ur phone, i said immediately!!!” Alhaji Lawal yace “Lallai kuwa tunda har ya turo

message din nan Komawa yaron nan yayi aka daura masa aure da yarinyar ba tare da sanin kowa ba, tunda ya san waliyanta sannan tun farko shi dama babu wanda yayi masa waliyyanci a cikinmu, don haka abu ne me sauki garesa” Abba dai baya cewa komai a parlon… Har bayan sati da text din nan wayar

Abuturrab a kashe yake, Jiddah na xaune daki tare da Maimoon da daddare tana son mata magana amma ta kasa, don bata ma san ta ina xata fara maganar ba, tun 3 days ago maganar ke cin ta amma ta kasa yi mata shi, can dai ta dake a hankali tace “Maimoon ya jikin Ya Aliyu?” Maimoon ta kalleta tace

“Wllh I don’t know, I can’t reach him for a week now” Jiddah tace “Both Whatsapp?” Maimoon tace “Baya hawa….” Jiddah bata kuma cewa komai, Maimoon dai sai kallonta take, mikewa tayi ta koma side din da take kwanciya tayi kwanciyarta…. Ranan Friday bayan an sauko sallan Juma’ah, Jiddah na xaune

xaune bakin tap din compound din gidan tana wanke hijabs dinta biyu don Safiyya na wanki a washing machine aka bude gate din gidan, daga kai tayi a tunaninta Ahmad ne don in dai ya shigo kd ya kan fara

xuwa ya gaida Umma kafin ya tafi gidansa, tun da ya shigo take kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta, saukarsa kasar kenan kuma babu inda ya fara nufowa sai gidan Umma……

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button