Uncategorized

SAMEEHA I


_????SÂMÊÊHÂ????_*

              (I)

“”Haɗuwa sukayi gaba ɗaya su haɗun a fallon Alhaji bukar bayan ya buƙaci hakan,zaman daya haɗa har da Zee da farin cikin ta yaƙi ɓoyuwa duk da Momy ta ja mata kunne a kan karta kuskura ta nuna jin daɗin abin tayi a bisa cika umarnin Alhaji bukar,Alhaji bukar ya dubi Zee da kanta ke ƙasa bakin  yaƙi rufuwa dan daɗi ya ce.

      “Zainabu ina son ki tsaya kiyi tunani da kyau, ki kauda kunya da kawaici akan tambayar da zan miki,kar ki amsa abinda kika san daga baya zaki zo kiyi nadama ko dana sanin aikatawa,Ni har ga Allah bazan ji wani abu na rashin jin daɗi idan kika faɗi abinda zuciyarki ta zaɓa miki ba,bazan miki dole ba dan bana fatan  muyi tufka daga baya tazo ta warwari,kina jina.


Gyaɗa kai kawai zee tayi ta sake duƙa kanta ƙasa kamar me kunyar gaske,shi kuwa Sameer gaba ɗaya hankalin ya koma kan zee da wani abu ke masa yawo kamar yaje ya haɗiyeta kowa ma ya huta zuciyar sa ta samu sassauci,ya ƙosa Alhaji bukar yabawa zee damar magana yaji me zata furta,momy na kallon yadda Sameer ya zauce a ranta sai murna take tana farin ciki,afili kuwa fuskar gaba ɗaya ta haɗe kamar bata taɓa farin ciki a doran ƙasa ba Alhaji bukar ya ɗora da….

             

     “”Zainabu dukkan nin mu da kika ga mun taru anan saboda ke kaɗai muka taru,amsarki kaɗai ce buƙatarmu,shin zaki auri Sameer da zuciya ɗaya a matsayin matar sa ta biyu,ko ko kina da wanda kike so azuciyarki………….dum zuciyar sameer ta buga tsoro da fargabar abinda Zee zata furta shi ya ɗaga masa hankali gaba ɗaya,daka kalleshi kasan da kwai matsala atattare dashi,zee taja wasu ƴan daƙiƙe tukun ta numfasa ta ce.


“”Abba na amince da duk abinda kuka zartar a kai na……daga inda Sameer yake ya daka uban ihu da tafi a tare yana furta.


“”Alhamdulillah,Allah na gode maka ta amsa, kamar wanda akayi wa albishir da wani abu me daɗi shi kansa Alhaji bukar tsayawa yayi yana duban sameer da mamaki fall a ransa kamar me shirin auran fari,gyaran murya yayi yace.


“Zainabu Babu wani da kukayi alƙawarin aure dashi musamman danaga ba anan ƙasar kikayi karatu ba,idan da akwai karki cu ci kanki ki faɗa min kai tsaye babu dole acikin wannan safga.


Abba bani da kowa,kuma zaɓin da kukayi mun shi ne nawa zaɓin nasan bazan taɓa biyanka da irin ɗawainiyar dakayi a kaina ba sai dai Addu’a da fata na gari,me zai saka naƙi jininka,koda ace ina da wani masoyin,Abba kafi ƙarfin ka nemi abu a guna na bula maka ƙasa a ido bare kuma babu wanda muka ƙulla maganar aure dashi,da murmushi Alhaji bukar ya sake cewa.


“Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya me ɗorewa dukka ku biyun ƴaƴa nane babu wanda yafi wani a guna,ƙulluwar aure a tsakaninku wani siri ne da ba wanda yasanshi sai Allah,ina muku fatan zaman lfy da kwanciyar hankali Allah kuma yabaku zuriya masu Albarka masu yi muku biyayya dai dai gwargwado,ya juyo ya dubi momy yace””


        Momy Sameer ina Sameeh…………layar dake ƙasan hannun momy ta danne ta da ƙarfin tsiya Alhaji bukar ya ɗan dabar barce chan kuma yace,”””ku tashi ku bamu waje ni da Sameer zamu tattauna yanda bikin zai tsaru a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci,momy da zee suka miƙe suka fito daga ɗakin,ɗakin momy suka wuce kai tsaye kowace zuciyar ta na ayyana mata abubuwa da dama.


Koda suka shiga ɗakin rawa Zee ta fara har da baiti momy na mata amshi daga ƙarshe suka saka shewa atare suka tafa layar hannun momy ta faɗo ƙasa,da sauri momy ta dafe ta ta na nunawa Zee tana magana””


“””””Shegiyar gayya mai sa ayi dolle ko an shirya ko ba ashirya ba,ita ce mai juya uba da ɗa ƙurungu ga aiki ga ban tsoro,momy ta dafa Zee da ɗaya hannun ta cigaba.


Ki saki jikin ki ki wala yarinya mu kwashi abinda mukazo nema yanzu tambarin mu ya buga ko wane shege a tafin hannuna yake,Allah yasa da an ɗaura rabo ya ratsa muci karan mu babu babbaka duk wanda yasa mana ido yasawa rayuwarsa Ɗiya ta,Zee ta jefawa momy tambya””


Ni ko momy naji Abba ya ambaci wachan sha taran,by sakan kuma naji ya kauce me yasa?.


,Aikin wannan kenan manta kanka da duk abinda kakeyi,ke idan kin matseta ko kashe mutum zakiyi ba zai taba sani ba har ki gama abinda zakiyi,kema taki nan a ajiye da an ɗaura zan ɗauko na danƙa miki amma da sharaɗi.


Wallahi zan bi indai zanyi abinda raina ke so na juya Sameer kamar waina a cikin tanda.


Kisha kurumin ki,kamar kinyi kin gama,maza jeki dubo mana matacciyar chan na san yanzu ta ƙarasa  ana gama kukan ta mu kuma mu ɗora da dariyar mu.


Wo wo Momy wani time ɗin sheɗan haka ya ganki ya barki..


*”Wa’iyazibllah,ya Allah ka kiyashemu da faɗawa halaka.*


Zee na fitowa daga ɗakin momy tayi ɓangaran su Sameeha,koda zee ta fita daga ɗakin duƙawa ƙasa momy tayi ta zaro wani abu a ƙasan gadon shi ba horo ba ba kuma dodo ba,babu kyan gani ta tura layar a bakinsa da ƙarfi ya haɗiye ta mai dashi inda ta ɗauko ta rufe..




_*WAI WAYE ADON TAFIYA*_



Alhaji bukar shahararran ɗan kasuwa ne ta ɓangaran fata ya kan ƙetara ƙasashe da dama……………








*Anan zan ɗan dakata idan naga Comments na cigaba????*





_*By*_

_*Maman Dr*_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button