HAUSA NOVELMUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

MUSADDAM NE ZABINA Complete Hausa Novel

1️⃣

 

 

______Saukar wayar wutar da na ji saman jikina ne ya dawo da hankalina cikin jikina. Baki na rawa na fara roƙonsa, “Abba dan ALLAH kayi haƙuri wallàhi bazan kara ba, Umma ki zo ki cece ni waiyo Umma zan mutu…”

Duk magiyar da nake hakan sam bai sa Abba jin koda ɗigon tausayi na ba. Sai da ya min jina-jina sannan ya wurgar da bulalar hannunsa yana huci da sauke ajiyar zuciya cikin bacin rai.

Ɗago kai na nayi dakyar wanda nake jinsa kamar an dora min dutsen dala saboda nauyin da yayi min nace, “Abba kayi haƙuri wallàhi nima ban san yadda aka yi na fara sonsa ba…”
“…Abba addu’a kawai zaku min amma wallahi ina ji a raina cewa idan ban samu *MUSADDAM* a matsayin miji ba wallàhi mutuwa zan yi…”

Sake yunkoruwa Abba yayi a matukar fusace da niyar rufe ni da wani dukan cikin sauri Umma ta riƙe masa hannu tana girgiza masa kai hawaye na zuba akan fuskarta.
Gabaki ɗaya Abba ji yayi jikinsa yayi sanyi kasancewar Umma mace mai matukar hakuri da kawar da kai akan batun ‘ya’yan ta.

Zame hannunsa yayi kawai ya fice daga gidan gabaki ɗaya saboda tabbas idan ya cigaba da zama cikin gidan wallàhi tsaf zai illata yarinyar nan.

Yana fita ta fashe da kuka tana mai rungume Umma. Sai dai dukda yadda tausayin ta yake bin duk wata jijiya ta jikinta hakan bai hana ta ture ta daga jikinta ba cikin nuna ko in kula ta ce,” yanzu irin rayuwar da kika zaɓawa kanki kenan *Ummi*?

Kallon umma tayi tace, “umma kin san duk yadda aka yi na faɗa cikin wannan halin, umma ban tsammaci wannan tambayar daga gare ki ba…”
“Umma ina matukar son sa, *MUSADDAM* ne zaɓina Umma wallàhi duk wani fitar numfashina da so da kaunarsa yake fita..”
“Umma tabbas zan mutu, zan mutu umma idan har ban auri *MUSADDAM* ba. Umma, *MUSA…DDAM…” lokaci ɗaya numfashinta ya ɗauke jiri ya kwashe ta.

Wata irin razananniyar kara umma ta sake tare da rungumeta tana mai kiran sunanta.

Ƙwantar da ita umma tayi ta fita waje neman agaji, cikin gaggawa aka dauke ta sai asibiti banda kuka babu abinda Umma take. Shi kansa Abban kukan zuci yake.

Ko da aka shiga da ita ɗakin, taimakon gaggawa Doctors din suka shiga bata cikin ikon ALLAH kuwa ta farfaɗo. Sosai Umma da Abba suka firgita ganin yanda ƴar su ƙwali ɗaya tal ta rame lokaci ɗaya kuma ta fita haiyacinta.

Kuka Umma take sosai, hakan yasa Abba ya janyo ta jikinsa yana rarrashinta da cewa, “ki daina kuka wannan ba komai ba ne daga cikin jarabtar da ALLAH yake yiwa bayinsa, kawai addu’a zamu cigaba da yi mata kamar yadda ta buƙata”

Nodding da kai kawai Umma ta yi.

*

Buɗe idanuwanta tayi a hankali ta sauke su kan iyayen na ta, murmushi tayi ganin yadda suke rungume juna suna kallonta tare da murmushi, sake rintse idanuwanta tayi yana ganin yadda nasu tsufan zai kasance ita da *MUSADDAM*

Kallonta Umma ta yi ta ga kamar murmushi take, cikin sauri ta ƙarasa gunta tana kiran sunan ta, “Ummi na”.

Buɗe idanuwan ta tayi a hankali fuskarta cike da murmushi tace, “na’am Umma na”.

Da mamaki duk suka kalli juna.

Kallon Abba tayi tace,”Abba har yanzu fushi kake da ni?”

Girgiza mata kai yayi yace, “a’a Ummi na ai komai ya wuce yanzu ya jikin naki?”

“Jiki alhamdullahi sai dai kuma ina jin ciwo a zuciya ta sosai, ciwo irin wanda soyayya take sakawa Abba, ina jin kamar zuciyata zata faso karjina ta fito. Rashin ganin *MUSADDAM* a yau tabbas zai iya zama silar rasa raina Abba”.

Cikin abinda bai fi minti biyu ba hawaye ya gama jiƙa mata gaban riga. Kallon ta kawai suke domin kuwa abin nata ya fara wuce hankali.

Riƙo hannun Umma tayi tana cewa, “umma na kan ji da yawa wadanda suka rasa uwa su na kuka da faɗan abubuwa masu nagarta akan ta, amma ban taɓa jin komai a rai na ba saboda na san kina kusa da ni, Umma ke uwace kuma tabbas na san kina jin raɗaɗin da nake ji, Umma ki taimaka min na ga *MUSADDAM* yau dan ALLAH Umma”.

Bakin gyalanta Umma tasa ta share hawayenta da shi tace,” shike nan daina kuka kin ji *Ummi* na…”

“…ba tare da bata lokaci ba zan kai ki gun *MUSADDAM*”
Kallonta Abba ya yi sai dai bai ce komai ba dan shi kansa yanzu abin ya fara ba shi tsoro sosai.

********

Zaune yake saman sofa, hannun sa riƙe da waya yana dannawa ,fuskarsa a daure gashi sai taunar chum gum yake kamar mace, kafar sa ɗaya tana dore bisa kan ɗaya.

Sallamar da aka yi ne yasa ya ɗago da kansa, tsaki yayi yace,”wane ne a gurin?”

Cike da rawar murya tace,”ni ce yaya *MUSADDAM* mummy ce tace ka sauko tana jiran ka”.

Sosa kansa yayi yace,”ki ce mata ina zuwa’.

“Ok yaya”.

Tashi yayi yana yatsina fuska. Sai da ya shiga ya watsa ruwa sannan ya fesa turare kafin ya fita daga ɗakin zuwa ɓangaren mummy.

Zaune ya sameta ta hakimce saman kushin banda ƙamshi babu abinda ke tashi a falon.

Cike da girmamawa ya rusuna a gaban ta yace,”ina ƙwana mummy”.

Sai da ya maimaita gaisuwar har sau uku sannan ta daka masa tsawa tana mai cewa, “ban kwana ba *MUSADDAM*, nace ban kwana ba”.

Rausayar da kai yayi ya koma kalar tausayi, kamo hanunta yayi ya damke cikin nashi tare da marairaicewa yace, “ki min afuwa mummy wallàhi ban san laifin da nayi miki ba sanyin idaniyata dan ALLAH a faɗa min laifin da nayi gudun kar na ƙara maimaita irinsa a gaba”.

Janye hanunta tayi tana mai sake haɗe fuskarta fiye da lokacin da ya shigo ɗakin tace, ” ya zancen alƙawarin da ka min?”

Sosa kansa yayi yace,”mummy ki yi hakuri wallàhi har yanzu ban samu wacce ta dace ba ne, amma insha ALLAH…”

Tsawar da ta daka masa ce yasa shi saurin dakatawa daga faɗar abinda yake da niyya.

Miƙewa tsaye tayi tace, “to bari ka ji wallàhi, wallàhi ka ji na rantse maka? Nan da ƙarshen wata idan baka zo min da yarinyar da zaka aura ba zan aura maka duk yarinyar da nake ganin ta dace da kai mtsww! Aikin ban za aikin wufi. Haka kawai ni kullum a cikin zagi da cin mutuncin nake ji da gani gurin dangin mahaifin ka saboda kullum gani suke kamar da sa hannuna akan rashin aurenka, wallàhi ka dai ji abinda na faɗa maka.”

Rausayar da kai yayi a sanyaye yace, “ki yi haƙuri, insha ALLAH zan yi kamar yadda kika ce.”
????????????????????
*MUSADDAM NE ZAƁINA*
????????????????????

*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*????

( WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS ????)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

 

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

*Reviewed by Musaddam Idiriss Musa*

_jama’a ku shaida na sadaukar da wannan littafin ga Musaddam Idiriss Musa_

 

*Remember this duniya is like a jail for the believers and those who haven’t been tested in this duniya will wish to send back just to go through hardship because there is so mush reward, so next time you go through any trials and hardship remember this…*

2️⃣

________Koda *MUSADDAM* ya koma ɗaki dafe kan sa yayi saboda wani irin sarawa da ya ji yana yi masa lokaci ɗaya.

Magani ya ɓalla ya sha dukda kuwa shi ba ma’abocin shan magani ba ne ba, amma jin yadda ciwon kan ya matsa hakan yasa ya sha maganin ko zai ɗan samu sauƙi daga raɗaɗin da yake ji, ga shi zancen mummy sai yawo yake masa a kai.

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un kawai yake ta maimaitawa. Sosai yake jin ciwon kai irin wanda bai taɓa jin kamarsa ba tsawon rayuwarsa, toilet ya shiga ya watsa ruwa ko hakan zai sa ya ɗan ji sauki amma ina! Cikin sauri ya saka kayansa don zuwa asibiti. Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci ba ƙaramar dauriya yake ba.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button