UKUBAR KISHIYATA 1-END

UKUBAR KISHIYATA Page 31 to 40

Ameera suna shiga d’akin,d’an k’aramin fridge dake gefen gadon ta nufa ta bud’e ta d’auki fresh milk mai sanyi ta kafa kai bata d’aga ba sai da ta shanye shi tas.Al’ameen da yake zaune a kan kujera yana kallonta yace…”ke dai yanzu kina son wannan abin dayawa”.

Sai da ta sauke empty roban a bakinta sanna ta amsa mishi da…”wallahi yayana in bansha ba jina nake ba dai-dai nake ba kuma sai in rinka jina… “Turo k’ofan da akayi tare da sallama shiya dakatar da maganan da take.

Altine ce ta shigo d’akin d’auke da katon tray da warmers akwai ta ajiye a kan rug dake tsakiyan d’akin tare da gaishe su,amsa mata sukayi fuska a sake.

Fita ta k’arayi ta dawo da wani madaidaicin tray mai d’auke da tea flasks da plates da cups ta ajiye ta fice tare da rufo musu k’ofa.

Kama hannunta yayi suka sauka k’asa inda Altine ta jera musu kayan breakfast.

Al’ameen shi ya fara bubbud’e warmers d’in yana dubanta yace…” Me zaki ci in zuba miki?”

“Zuba min pepper soup d’in saboda bakina yafi son Abu mai yaji”.

Zuba mata yayi a plate ta fara ci,shi kuma chips ya zuba suna ci suna hiransu.

Al’ameen yace…” Babyna wai kin fad’awa su Umma rashin lafiyarki kuwa?”

“Um-um ” tace tana tura katon tsoka bakinta.

“mesa baki fad’a ba?” Ya bukata.

“Zan k’ira wayan Fateema anjima in fad’a mata sai ta gayawa Umma”.

” Fateema kenan sarkin rawan kai bansan meya hanata zuwa gidanmu ba”yace yana murmushi.

Bata fuska tayi tace…” Hmmm tana son zuwa amma Abba ya hana dan ba abinda ya tsana kaman fita anguwa daga makaranta sai gida”.

Gyad’a kai yayi yana ajiye tea cup dake hannun shi yace…” Abba yana da gaskiya cos ‘ya mace sai da kula”.

Bayan sun k’are cin abincin,k’wanciya yayi a cinyarta suka bud’e sabon shafin love.

Ameera tana wasa da gashin kanshi tace…”yayana ka manta maganan Alhaji ne?”

“Wanne magana kenan?” Ya tambaya yana b’ata fuska kaman mai tunani.

Dariya tayi tana ture kanshi akan cinyarta tace…”kasan abinda nufi tashi ka tafi office “.

Tashi yayi ya zauna suna facing juna ya rik’o fuskanta da hannayen shi yace…” Kora ta kike ko Babyna?”

Zaro ido tayi tana kallon shi tace…” Na isa in kore ka…..”bata samu daman k’arasa maganan ba sakamakon had’a bakinshi da nata da yayi.

Sun jima a haka har yana k’okarin zarcewa Ameera ta k’wace kanta da k’yar tace…” Ka manta a gidanku muke?in Hajiya ta shigo ta same mu a haka fa?”

Yana gyara riganshi yace…” Ni nasan ba wanda zai shigo nan koda k’wana zamuyi a cikin d’akin nan”.

Rau-rau tayi da ido cikin shagwab’a tace…” Yayana ka manta meya kawo mu nan ko sai kasa Hajiya ta koremu”.

” hmmm wai ke wayo ko?gashi daga zuwa gidan Hajiya kin warke”.

Ajiyan zuciya tayi tana kallon gefe tace…” Yayana ina su Aunty dash Fa’iza?”

Had’a rai yayi kaman wanda aka gayawa sak’on mutuwa yace…” Muna zaune lafiya shine kike son b’ata min rai ko?”

Matsowa tayi ta d’ora kanta akan kafad’an shi tace…”ba haka nake nufi ba kayi hak’uri dan Allah”.

Rungomota yayi ta gefe ya fara magana…”ki yafe min Ameera akan abubuwa da suke faruwa a gida bansan me yake faruwa dani ba musamman in a gaban Lateefa ne sai in rasa ina kaina yake ga kuma wani shakkarta da nake ji ko kallonki bazan iya yi aganta ba,wannan abu yana matuk’ar damuna.ina son in kika k’ira Umma tazo ki fad’a mata su taya mu da addu’a nima zan fad’awa su Hajiya”.

Hawaye na sauka a kan fuskarta tace…”abu d’aya muke fuskanta yayana Umma tana zuwa zan fad’a mata ta gayawa Abba ya taimaka mana da addu’oi”.

Suna cikin magana Ya Sa’ad ya shigo yana yiwa Al’ameen tsiya wai Baban twins.

Shiko sai dariya yake yana amsawa da Allah yasa ya fad’a a bakin mala’iku.

Bai jima ba ya duba Ameera tare kad’a kan Al’ameen suka fita tare.

Bayan tafiyansu ne Ameera tayi dialling number Fateema,bai dad’e yana ringing ba ta d’aga tare da tambayan waye 

“Ke dallah Teema nice fa” Ameera ta amsa mata a d’ayan b’angaren.

Ihu Fateema tayi cikin murna tace…” Sisto kece wayyo I missed u ina wayar ki take kika kirani da wannan?”.

Dariya Ameera tayi tace..” Ke kar ki cika min kunne,wayar Al’ameen ce. meya hanaki zuwa in kinyi missing d’ina da gaske?kuma ko a waya in ban kira ki ba,ba kya kirana”.

Marairaice murya Fateema tayi tana… ” ya kike magana kaman baki san halin Abba ba?yanzu abin nashi ya kara gaba dan cewa yayi in muna yawan zuwa gidanki mutane zasu ce mun zuba k’afa a gidanki sabida k’wad’ayi munga mijiki mai kud’i,shiyasa baki ganni ba “.

” toh shikenan ki bawa Umma wayan ” .

Fita tayi zuwa tsakar gida inda Umma take zaune tana gyara gyad’an miya,mik’a mata wayan tayi tace Ameera ce ta k’ira.

Karb’a Umma tayi bayan sun gaisa Ameera take fad’a mata abinda ya faru, nan tayi mata Allah ya sauwake tare da alkawarin zasu zo gobe su dubata ita da Fateema.

Cikin tsanin farincikin zata ga Ummarta ta tashi ta fito parlour wajan Hajiya kuma har tana aiyanawa a ranta matsalarta ya kusa karewa dan tasan Abba yana ji zaiyi wani abu akai.

*part thirty one*

A parlour ta iske Hajiya da wata bak’uwarta suna hira,durkusawa tayi har k’asa ta gaida bak’uwar sannan ta samu waje a kasa ta zauna.

Hajiya ta b’ata fuska tana dubanta tace…”ya zaki zauna a k’asa ki hau kan kujera ki zauna”.

Batayi gardama ba ta hau ta zauna, ganin yanda Hajiya ta b’ata fuska.

Bak’uwar tana murmushi tace…” Hajiya bak’uwa kikayi ne bangane ta ba”.

” asama’u kenan amaryar d’an auta nane baki gane ba?”Hajiya tace itama tana murmushin.

Wacce aka k’ira da Asma’un ta k’ara fad’ad’a fara’ar fuskanta tace…”Allah sarki itace wacce mukayi bikin k’wanakin baya ko?”

Kamin Hajiya ta bata amsa ta cigaba…” Ke yanzu kinga laifina ya za’ayi in gane ta tunda shi Al’ameen d’in kanshi rabon shida gidana sai ince yafi shekara goma bare matansa”.

” kada ki damu zai kai miki su ku yini insha Allah ” Hajiya tayi assurance d’inta.

Ameera dai tana jinsu bata ce komai ba saida Hajiya ta gabatar mata da matan a matsayin k’awarta ce tun suna secondary school.

Kasa sakewa tayi tare dasu dan haka bata dad’e da zama ba ta tashi ta koma d’akinta ta k’wanta.

Sai bayan shiganta ne Hajiya takewa Asma’u bayani game da Ameera,nan ta taya su murna tare da addu’an Allah ya raba lafiya.

Bayan sallahn azahar misalin biyu da rabi saiga Al’ameen ya kasa zaman office ya dawo gida.

Koda Hajiya ta fara mishi fad’an meyasa ya dawo lokacin tashi baiyi ba,marairaice fuska yayi yace zazzabine yake son rufe shi shiyasa ya dawo.

Sannu ta shiga jera mishi tace…” Ya sha paracetamol ya k’wanta ya huta.

Karb’an maganin yayi yana Jan k’afa shi a dole ga mara lafiya ya wuce d’akin Ameera.

Dariya Hajiya tayi tana girgiza kai tace…” Wai ni zaiyiwa dabara”.

Sallama yayi ya tura k’ofan ya shiga,baki bud’e Ameera take kallon shi har ya maida k’ofan ya rufe.

Ajiye brief case d’inshi akan kujera yayi ya juyo yana kallon yanda ta sake baki tana kallon shi ga abinci a gabanta ta bud’e da niyan zubawa amma ta kasa.

Gabanta yazo ya tsuguna yasa hannun shi ya rufe mata bakin yace…” Rufe bakin mana ‘yan matana”.

D’an had’a rai tayi tare da kawar da kanta gefe tace…” Haba Yayana yaushe ka bar gidan nan da zaka k’ara dawowa,na lura so kake Hajiya ta kore mu a gidanta mu huta”.

Rungumota yayi ta baya tare da kissing d’in wuyanta yace…”haka ake taran miji Babyna tunda baki saba gani a gida by dis time ba ai kamata yayi ki tambaye ni ko lafiya,ko kin manta tare muka fara laulayin ne in tuna miki?”

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button