Labaran Kannywood

Kamaye ya yi tir da masu yaɗa ƙarya game da ‘yan Kannywood, ya ce ‘Ina nan ban mutu ba’

JARUMI kuma babban furodusa Malam Ɗan’azimi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa (wanda aka fi sani da Kamaye) ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa wai ya rasu.

 

Tun a safiyar jiya Laraba dai aka tashi da yaɗuwar labarin, aka shafe tsawon wuni ana baza shi a soshiyal midiya, har ta kai wasu su ka ɗauka gaskiya ne, su na buga fosta da rubutun Allah ya jiƙan shi.

 

Amma jarumin na cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ ya yi magana da mujallar Fim kan labarin, ya ce: “To, ni dai haka na ga labarin a soshiyal midiya, kuma daga baya ake ta bugo mini waya ana cewa na mutu.

 

“Ni dai a yanzu ina nan da rai na, ban mutu ba. Kuma lafiya na ke, ina ci gaba da harkokin da na ke yi.”

 

Jarumin ya yi Allah-wadai da masu yaɗa labarin ƙanzon kurege game da ‘yan fim a soshital midiya. Ya ce: “Ban san abin da ya sa wasu su ka mayar da irin wannan labarin na ƙarya a matsayin labarin da za su ɗora a shafin su ba, wai don su na son a rinƙa bibiyar su. Wannan ba aikin jarida ba ne, shirme ne kawai da ɓata sunan mutum da kuma tayar da hankalin jama’a, don a yanzu duk masoya da masu ƙauna ta da su ka ga wannan labarin hankalin su ya tashi.”

 

Malam Ɗan’azimi ya yi kira ga masoyan sa da su kwantar da hankalin su. Ya ce: “Ina kira ga masoya na su kwantar da hankalin su. Ina nan da rai na cikin ƙoshin lafiya, ban mutu ba.

 

“Kuma ina yi wa kowa fatan alheri saboda ƙaunar da aka nuna mini.”

 

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ba wannan ba ne karo na farko da aka yaɗa labarin ƙarya game da jaruman Kannywood, musamman mutuwa. Wannan labarin ya na daga cikin waɗanda su ka fi ɗaukar hankalin mutane sosai.

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button