KANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA COMPLETE NOVELS
Saida biki yarage sati uku aka sanarda kuluwa, aiko ranar ansha bala’inta agidan, takuma rantse baza taima Rakkiya ko cokaliba na kayan d’aki, su mariya na zugata.
Ahaka biki yaxo akasha biki, kuluwa bataima Rakkiya komaiba sai babanta ya kukkula yaymata iya karfinsa.
Ankai amarya d’akinta agarin KUSADA, inda angonta yake, itama k’awarta anyi bikinta da malam Ashiru.
Sun sami ciki kusan lokaci d’aya itada karima, karima tafara haihuwar mace akasa mata Safare.
Bayan sati biyu Rakkiya tafara nak’uda, saidai tana shan wahala, ahaka tahaifi d’iyarta mace, akasa mata ZUWAIRA.
Tunda Rakkiya ta haihu batada lafiya, yau fari gobe tsumma, ganin haka aka kawo Asabe, dan tarink’a taimaka mata, dayake yanzu suna d’anyi da’ita.
Bawani dad’in Asabe Rakkiya takejiba, dan bata mata aikin komai, ahaka dai Rakkiya takai wata biyu tana jinya, wata Juma’a tace ga garinku nan.
Malam Usman yaji wannan mutuwa, shida mahaifiyarsa wadda itama bayan sati biyu tarasu, yashiga rud’u mai yawa garashi mahaifiya gana mata ga jaririya anbarmasa.
“””Itama karima taji mutuwar k’awarta sosai, amma bayanda xatayi saidai hakuri.
Bayan Rakkiya tayi arba’in sai dangin malam Usman suka yanke shawarar ya auri Asabe, tamaye gurbin Rakkiya kodan ta raini Zuwaira, tunda d’iyar ‘yar uwarta ce, duk da kullum ana kaita wajan karima tana shayar da ita, itada Safare.
Kowa yaji dad’in auren malam Usman da Asabe, bakamar kuluwa datake ganin yanzu malam Usman d’in yaxama shahararre…………✍????
????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I ???? U MY FAN’s
[10/25, 11:11 AM] +234 809 777 0370: 19~ july~2016
????????????????
????6⃣????
????????
????
????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA❓????
????NA BILLKISA IBRAHIM????
»« Aranar wata talata yaje kasuwar D’an zabuwa, shida malam Ashiru, malam Ashiru yagayyaci malam Usman xuwa gidan gwaggonsa, sunje sun gaida gwaggon malam Ashiru sunfito, sai suka gamu da ‘yammata biyu zasu shiga gidan, d’aya acikinsu tace lah yaya Ashiru yaushe kaxo ??.
"Yace yanxu badad'ewa kinsan yau kasuwa;
Tace hakane yasu inna duk sunanan lafiya??
Lafiya lau tunda kink’i zuwa gaisheta.
“Tace karka damu zanzo sai dai inajin kunya ne””
Malam Ashiru yay dariya tare dafad’in karima kenan, tohaka zamuyi auren kinajin kunyarsu innar ??
Tasa hannu tarufe fuska tana dariya
“Yace baki fad’a mana sunan k’awar takiba??
“Tace sunanta RAKIYA, kaifa yasunan abokinka??
Yace ai yafad’a miki dakansa kawai.
Malam Usman yay murmushi, ni sunana Usman, koxaki bani wannan k’awar taki nima na aura ??
Rakkiya dake gefe kanta ak’asa, tunda ta gaidasu, tad’ago da sauri tana kallonsu????.
Karima tace indai tana sonka, zan baka.
“”Yace to ki tanbaye ta indai tana sona, ni dagaske nakeyi.
Ahaka soyayya mai k’arfi tashiga tsakanin RAKKIYA da Malam Usman, sai dai matsala d’aya suke fuskanta, itace mahaifiyar Rakiya, domin kuwa macece mai shegen kwad’ayi.
Tana son ‘ya’yanta su auri mai kud’i dukda ita talakace dangin tama talakawane.
++++++++++++++
Malam zubairu shine mahaifin RAKIYA, KULUWA kuma mamarsu, su hud’u suka haifa, Mariya, ce babba sai kamilu, sai Rakkiya, Asabe itace auta.
Mariya tana auren kansilan garin D’an zabuwa, dan sunada k’au ba laifi, yanxu kima ana zancen auren Rakkiya……..✍????
????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I ???? U MY FAN’s
[10/25, 11:12 AM] +234 809 777 0370: 20~ july~2016
????????????????
????8⃣????
????????
????
????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA❓????
????NA BILLKISA IBRAHIM????
»« sai dai gaskiya malam Usman baya son asabe, dan yasan batada tarbiyya, amma bayanda xaiyi tunda iyayensa ne suka kawo shawarar hakan.
“Dafarko asabe nasan Zuwaira, amma tunda ta haihu tasami mace Atika, taga yanda malam Usman yakeson Zuwaira, baya son Atika haka, wannan yasa tad’au karan tsana ta d’orama Zuwaira.”
Tazo tasake haihuwar mace, akasa mata Huwaila, sannan Zuwaira nada shekara biyar, amma idan kaga aikin datakeyi saika tausaya mata.
Ahaka Zuwaira takai shekara tara Atika nada takwas, Huwaila nada shida, sai auta kabiru wanda Inna Asabe tasake haihuwa nada hud’u.
Alokacinne inna Asabe tafara kokon saidawa, da hantsi tayi AWARA, kuma zuwaira ce mai tallah, dafarko m.Usman yace bai yardaba, amma da inna Asabe tashiga tafita ta asirce shi saiya daina magana gaba d’aya.
“”Zuwaira nashan wahala sosai wajan inna Asabe, duk sana’ara da inna asabe taima Zuwaira indai bata sayarba, saita zaneta, balle kuma ta b’atar, ai ranar ta bani.
Saita girka abinci tahana Zuwaira, Zuwaira ke wanke wanke, shara, wankinsu Atika, gasu Atika sun rainata, saisuyi ta dukanta, m. USMAN baya iya cewa komai, duk da abin yana damunsa, amma bayadda zaiyi.
“”Idan wuya taima Zuwaira yawa saita gudu gidan karima, dan haka suka shak’u da Safare sosai, tare suke zuwa talla, dan Inna karima tanama Safare taliyan hausa, duk da malam Ashiru bayaso, to amma dayake fatauci yake zuwa saitake samun damar yimata daya dawo saita daina.
Duk sanda inna Asabe taji labarin Zuwaira taje wurin inna karima to saita xaneta, dan takance taje sunyi gulmarta.
Ahaka Zuwaira tatashi cikin wahala, da azabtuwar aikn inna Asabe, abun nadamun malam Usman amma badamar yin magana.
“Dahaka Zuwaira takai shekara goma sha biyu, kullum tana wahar yima inna Asabe talla, duk da bata amfanuwa da sisin kwabo acikin kud’in tallan, ko silifas saidai baban ta ya saya mata……….✍????
????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I????U MY FAN’s
[10/25, 11:14 AM] +234 809 777 0370: 20~ july~1016
????????????????
????9⃣????
????????
????
????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA❓????
????NA BILLKISA IBRAHIM????
»« MUNDAWO LABARI :- Zuwaira kwance akan tabarmar datake kwanciya tanata mirgina2, saboda azabar yunwar datake ji, rabonta da cin abinci tun jiya da daddare, dasafe da yunwa tatafi tallan koko, dama ita tuwone aboncinta, kuma tacinye tun da daddare.
“”Inna Asabe ta danno cikin d’akin batare da tayi koda sallama ba.
Ta kalli Zuwaira dake kwance tana juyi, tace dan ubanki dama kinaji ina kiranki kikai banza dani, saboda ke shahararriyar ‘yar iskace, waima dan uwarki Rakkiya miki ke yi akwance, ga wanke2 nacan awaje k’uda nabi.
“”Dan ALLAH inna kiyi hak’uri wlhy inajin yunwa ne, kuma naduba a tukunya babu tuwo, dama dasafe ban karyaba natafi tallah””
Inna Asabe taja tsaki kekika sani, aibani nace ki bud’e ciki kicinye tuwon jiyaba ko ??
Niki tashi na aikeki gidan hajiya fatsima k’awata.
Cikin k’arfin hali tace inna dan ALLAH kiyi hak’uri, ALLAH baxan iya tafiyaba, dan ALLAH in kun rage abinci ko k’anxo ne ki taimaka mini da shi karna mutu.
Nanfa inna Asabe tafara zazzaga jaraba, dan uwarki kin manta nafad’a miki, bakida kaaon abincin rana a gidannan, ko kin manta ??
“”Inna kiji tsoron ALLAH, nifa d’iyar ‘yar uwarkice””
Dan ubanki da tsoronki nakeji, bana ALLAH ba;har xakice bana tsoron ALLAH, tasamo icce taahiga jibgar Zuwaira, tana fad’in bari nanuna miki raahon tsoron ALLAH.
Tun Zuwaira na iya kuka tana neman agaji, har tai ahiru sai nishin wahala……….✍????
????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I????U MY FAN’s
[10/25, 11:21 AM] +234 809 777 0370: 22~ july~2016
????1⃣1⃣????
????????????
????????
????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA❓????
????NA BILLKISA IBRAHIM????
»«yau kwana biyu da rasuwar malam Usman, yaune aka sallami Zuwaira daga asibiti, bawanda yagaya mata, inna jamilace agurinta, kanwar malam Usman ce, tunda tafarka gabanta ke fad’uwa, harga shi yau an sallamesu, tunda suka nufo gida fad’uwar gabanta ya k’aru.
Kallon mutane kawai takeyi, tun waje har suka shigo gida,kowa na kallonta cikin tausayawa, inna Ai, tadafa mata ruwan wanka, tai wanka aka bata abinci, amma takasa ci, nan sukaita lallab’ata tad’anci, bayan tagama tace wai dan ALLAH miya farune?? Kowa yay shiru, tace ina inna asabe ??
“Sukace tana d’akinta”
Tatashi tanufi d’akin inna asabe, tashiga inna asabe na zaune tare da danginta dasuka xo dakuma k’awayenta, ta gaishe su, ganinta yasa wasu cikin dangin kuka, saboda tsananin tausayinta da sukeyi, shike nan yanxu tazama marainiya gaba d’aya, ba uwa ba uba.
Inna asabe saita mik’e tafita tana matsar ido, dan ba kukan tajeyiba, sukace asabe ai saidai hak’uri, su sun zata kukan tausayin Zuwaira takeyi.
“”Itama Zuwaira saita saka kuka, tace dan ALLAH inna mariya maiya faru??
Mariya tace kiyi hak’uri zuwaira baban kine yarasu !!;
“Anan Zuwaira ta sume”
Inna binta”tace haba mariya aiba haka akeba, yazaki gaya mata.
Aka yayyafama Zuwaira ruwa ta far fad’o, azuciyarta tace yanzu xan k’ara gane inna asabe K’ANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA.