KANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA COMPLETE NOVELS

KANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA COMPLETE NOVELS

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I????U MY FAN’s
[10/25, 2:55 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 28~ july~2016
????2⃣6⃣????
????????????
????????

????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA❓????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« ALLAH sarki Zuwaira tunda ‘yan kusada suka tafi take kuka, ga fargabar wannan auren da bataso, ga tunanin inna asabe dabata san halin datake cikiba, tunda har suka taho jiya bata farfad’oba, anty Abida tashigo d’akin da sallama, ta zauna kusada Zuwaira abakin gadon haba k’anwata kukanne har yanzu, yaka mata abari haka, wannan shine yak’in namu mu mata, muma duk haka akai mana.
“”Ummy tashigo d’akin tana fad’in ‘yannan yanxu nan baki bar kukannan ba ??
Wlhy kuwa ummy nima yanzu nagama lallashinta, karma kanta yazo yana ciwo.
Ummy “”tace kiyi hak’uri d’iyata kinji, kukan ya isa haka, nan dai sukaita lallashinta hartai shiru, ummy ta mik’e tana fad’in Abida kisata tayi wanka kinga da anyi sallar isha’i sai mijinta yazo su tafi, tunda tak’i cin abincin.
“To ummy ai insunje can yasata taci shi,, anty Abida tashiryata cikin atanfa mai k’yau, tayi k’yau sosai, tayi SALLAH tazauna jiran Sultan, duk da ita tafison gidan ummy, bata so akaita wani gida daban, gashi ance tanada kishiya, wasu ‘yan kwalla suka taru mata a idanu, itakam tana ganin Rayuwa ALLAH ya tak’aita mata, wahalar nan, tunda tagirma tai wayau batasan miye jindad’iba.

Cikin sassanyar muryar sa yay sallama, ta amsa batare data d’agoba, ya k’araso cikin d’akin idonsa na kanta, ta daure tace ina yini ??
“Lafiya lao, mai kuka, haryanxu kukanne ??
Ta share hawayenta tana girgixa kai alamar A’a.
Yay murmushi to taso mutafi gida ko, kinga dare yafara yi, ga garin da hadari, tad’ago kai ta kalleshi, yana cikin k’ananun kaya yayi k’yau tamkar matashin saurayi, dan ALLAH kabarni anan ??
“”Ya fitar da huci tabaki haba Juwairiyya, keda kike amarya yaxa abarki anan, kiyi hak’uri dai zandinga kawoki akai akai kina gaisheta kinji, yafad’a yana rik’o hannunta”
Dole tamik’e badan tasoba, yace “ina gyalenki ??
Ta d’auka ta yafa, tana hawaye, ahaka suka fito falo, Sultan yace ummy bari muwuce kar ruwannan ya sakko, ina abincin ??.
“”Ummy tace” Abida takai mota, saida safenku, d’iyata aita hak’uri kinji.
Har mota anty Abida tarakasu, tasake lallashin Zuwaira, sannan yaja mota suka tafi.

Tunda suka tafi baice da ita komaiba, aikin tuk’insa kawai yakeyi, itakuma ta takure ajikin murfin mota tana kuka, baya son yaga ana kuka, dan haka tausayinta ya d’arsu aransa, amma yasan idan yaci gaba da lallashinta baxata daina kukanba, sai ya daka mata tsawa wadda tasa hantar cikinta yamutsawa, kinga kimin shiru wannan kukan ya isheni kona tsaya na bubbugeki, tunda safe ake lallashinki amma kink’i kiyi hakuri, koxamu yanka namanki mucine ?? To naji tsit anan.
“”Aiko mutuni yarku saitayi tsit ko shashshekar kukan babu, kuma asanna tagano waye Sultan danta tuna ganinta dashi a kusada………………..✍????

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I????U MY FAN’s
[10/25, 2:56 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 28~ july~2016
????2⃣7⃣????
????????????
????????

????K’ANWAR UWACE????
ko
???? KISHIYAR UWA❓????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« Har suka isa gidan bata k’ara ko k’wak’wk’waran motsiba, shikuma baisake cewa komaiba, wani gida suka isa madaidaici, amma bagidan da ikeeram take bane, shima wannan yanada k’yau, mai gadi yabud’e masa get, yadanna hancin motarsa cikin gidan, bayan yay faking ya kashe motar, yakai dubansa ga Zuwaira data takure jikinta, yay d’an murmushi, sai dai tabasa tausayi baiso ya aikata haka garetaba, bayaso ta d’aukeshi masifaffe, ya bud’e mata murfin motar to fita muje ko.
Cikin sanyin jiki tafita lokacin har anfara yayyafi, yad’auki d’an kwandon da kulolin abincin suke ciki da wata leda, ganin ta tsaya kallonsa sai kawai yaja hannunta, batare da yayi maganaba, yabud’e kofar palon suka shiga, kai jama’a palonnan fa ya had’u aradu kuwa.

Ya zauna ad’aya daga cikin kujerun yana fad’in wash ALLAH, itakam Zuwaira k’asa ta zauna ad’arare, da sauri yace haba Juwairiyya keda gidanki ki zauna k’asa maxa tashi ki hau kujera, dayake atsorace take dashi saita tashi da sauri ta hau kujerar dake kusada k’ofa.
“”Ya kalleta ya girgiza kai lallai yanada aiki agabnsa, dankuwa ya lura saiyayi Raino, saiya tuna ikeeram adarensu na farko itace ma ta taimaka burinsa ya cika, amma daga baya saita gujeshi alokacin dayafi buk’atar taima konta, harta jashi dayin aure biyu, abinda baya cikin tsarinsa, lallai yayi dana sanin d’aukar Zuciyarsa yabama Ikeeram.
Wata tsawa da akayi tadawo dashi hayyacinsa, ya mik’e ya nufi kichin, itadai Zuwaira batasan wainar dayake toyawaba ma, dan tuna ninta yana kusada.
“Ya fito hannunsa rik’e da filed da kofuna, ya zauna ya zuba abincin da abinsha, zuwa yay yakamo hannunta batare dayayi mata maganaba, ya zaunar da ita, abinci yad’ebo acokali ya nufi bakinta dashi da sauri ta matsa baya.
Yace” yaya dai ??
Cikin rawar murya tace inna karima tace mana kar mu yarda namiji yabamu abu abaki, iskanci ne.
“”Tofa Sultan yafad’a yana gyad’a kai, lallai da sauran aiki, a fili sai yace to d’auka kici da kanki, amma banda wasa, inba hakaba kuma toh ya cije leb’ensa na k’asa.
Ta d’anci abincin saboda tsoronsa datakeji, jama’a bafa tsoro da amare sukeyiba, dan ita Zuwaira bama tasan wannanba.
Shima yaci yace ” to tashi narakaki d’akinki ki kwanta ko ??
Tamik’e yarakata wani d’aki dayaji kayan gado na alfarma, to kinga ga d’akinki nan, ni bari naje nakwanta saida safe, tace “ALLAH ya kaimu.
Har ya fita yadawo kinga na manta na nuna miki bayi, ya nunnuna mata duk abinda ya kamata, yace bak’ya jin dai tsoro ko?? Tace”eh.
“”To shikenan saida safe yafad’a yana fita.
Bayan fitarsa ta sake ganin ko ina, wai yau itace awannan d’aki wai kuma nata, ta tuna gidansu akan wata tsohuwar karaunin tabarma take kwana, ko abin lullub’a babu, ita kam ba abinda xatace da ALLAH sai godiya, saidai abinda yake bata mamaki ance tanada kishiya amma har yanxu tunda aka kawota bataga kishiyarba, kotana ina ?? Haka dai ta kwanta batare data cire kayan jikintaba, barci yay awon gaba da’Ita.

Shikam Sultan yana d’akinsa ya kasa barcin sai sak’a da warwar yakeyi, yasan dolene yay hak’uri da yarinyar nan sai xuwa wani lokaci, ga matsalar ikeeram, dan yasan bala’inta da k’in da takema kishiya, tunkan suyi aure ko hira suke yay maganar kishiya to saitayi sati bata fito wajansaba koda yaje gidansu, to bare yanxu ace ammata, kuma bata saniba lallai da cakwakiya kam………………..✍????

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I????U MY FAN’s
[10/25, 2:57 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 29~ july~2016
????2⃣8⃣????
????????????
????????
????2⃣9⃣????
????????????
????????

????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« KUSADA :- inna Asabe antashi, sai dai saboda bak’in cikin da zuciyarta take ciki takasa magana, wannan yasa bikin Atika baiyi wani arbashiba sosai, bayan ‘yankai Zuwaira sun koma gida labari yacika gari akan gidan Zuwaira da mijin data aura, wannan lamari yak’ara gigitar da inna Asabe, takuma d’au alk’awarin tar watsa auren Zuwaira, tofa ashe dasauran cakwakiya kudai biyoni.

????????????????????????????????
Katsina kuwa yau kwanan Zuwaira hud’u da angon nata, sai dai tak’i sakin jiki dashi ko kad’an, hasalima tsoronsa takeji, idan yana palo tana d’aki sai dai shi yashiga d’akin yasata taci abincin da ummy ta aiko musu, to gashi hutun da akabasa a office gobe zai k’are, yashafa sumar kansa yana mai fidda huci, yakamata yanemo hanyar dazata ringa kusantashi da yarin yarnan, dan bayaso taci gaba dajin tsoronsa, ya kalli wayarsa datake ta faman ruri yaja tsaki, ikeeram ce keta faman kiransa amma yak’i ya d’aga, dan yasan matsalarta bata wuce ta atura mata kud’iba, mai makon yad’auki wayar sai kawai yaxari mukullin mota da wayar yafice abinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Back to top button