KANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA COMPLETE NOVELS

KANWAR UWACE KO KISHIYAR UWA COMPLETE NOVELS

Gidan ummy yanufa bayan sun gaisa damai gadi yay masa alkairi kamar yanda yasaba yanufi cikin gidan ummy na zaune dawata dattijuwa suna kama da ummy sosai, sunata hira abinsu, yay sallama suka amsa, ummy tace ango kasha k’amshi yay d’an murmushi yana sosa gefen kansa da key d’in mota.
“Ya kalli dattijuwar nan yace” wlhy gwaggo dama kinyi zamanki anan kyaringa d’ebema ummy kewa tunda acand’imma babu abinda kikeyi.
Ummy tace wlhy nima auta haka nace tunjiya nake rok’onta amma tak’i, yace ” kai gwaggo dan ALLAH ki zauna damu mana, gwaggo tai dariya to shikenan karkai kuka xan zauna, cikin farinciki yaje ya rungume gwaggo, suna masa dariya.
“””Bayan sun lafa da dariyar yace ” ummy gobe idan ALLAH yakaimu xan koma wajen aiki, gashi inada fasinja zuwa GERMANY, bansan yanda zanyi fa Juwairiyya ba”””
Ummy tace”nima tuni wannan tunanin yana raina, dole sai dai anemo wata tsohuwa daxasu xauna dan ta rink’a d’ebe mata kewa.
” ummy asamo mai d’an k’arfi wadda zata taimaka da koya mata wasu abubuwan.
“Gwaggo tace”wannan kuma aikinane akwai wata hajja Rabi a saudiyya suka zauna da mijinta to bayan rasuwarsa saita dawo gida, to nakula xaman k’auyen bata jindad’insa tunda bata sababa, ita kawai yakamata ad’akko nasan zaku k’aru da ita sosai”
Ai gwaggo duk yanda kikace dai dai ne kinga kawai saiki shirya yanxu muje mu d’akkota kema ki had’o kayanki.
ummy tace wannan shawara tayi, saikuje d’in Salamatu, to shike nan yaya bari naje na shirya.

Sun isa garin matazu, garinda gwaggo take kenan, kuma sun sami nasar d’akko hajja Rabi, ana kiran magriba suka shigo cikin garin katsina, gidansu ummy suka nufa, ummy tayi farincikin ganinsu da hajja Rabi, anan yabarta yatafi gida sai gobe in ALLAH yakaimu xa’a kaita gidan Sultan.
“Yashiga palon da sallama, Zuwaira na xaune tsakanin kujeru ta mak’ure guri d’aya, jikinta sai rawa yakeyi, da sauri Sultan yak’arasa gareta yana fad’in Juwairiyya lafiya?? Yasa hannu ya d’ago fuskarta duk ta b’aci da hawaye, miya sameki ?? Yasake tambaya akaro na biyu, cikin sark’ewar murya tace tsoro nakeji.”
Ya d’agota ya zaunar saman kujera shima ya zauna kusa da ita, Juwairiyya kinga wani abin tsorone??, ta girgixa kai, kawaidai inajin tsorone, yasa hankacif yana goge mata hawayen to ya isa haka kukan yi hak’uri kiji, naje samomiki wadda zaku zaunane, in sha ALLAH daga yau baxaki sake jin tsoroba kinji, ta d’aga kai cikin sanyinta.
“Kinyi SALLAH dai ko?? Ta girgixa kai alamar A’a, ya mik’ar da ita to tashi muje kiyi SALLAH ko”
Har d’akinta yarakata tashiga bayi tayo alwala tafito yana zaune abakin gado yana kallonta, yanda tayi sallar ya birgeshi dankuwa gyara kad’an za aimata aciki, insha ALLAH zai nemamata school tafara zuwa, kwananan.

Bayan ta idar, yace”Juwairiyya?? cikin sanyinta tace na’am, ya gyara zama, gobe idan ALLAH yakaimu wadda zaku xauna xataxo sunanta hajja Rabi, saboda yanayin aikina, yau inacan gobe inacan, gakuma binda ban tab’a sanar dakeba shine inada mata, sunanta ikeeram, yanxu bata k’asarnan tana Egypt jiyyar kakarta dabata da lfy, tokinga wataran ina gidan ta dan ba gidanku d’ayaba, kinga bazai yuwwuba nabarki ke kad’ai nasan ke yarinya ce tagari mai hak’uri, dankuwa tun aranar dana kusan tureki damota, harkikai asarar Awararki nakuma baki kud’i kika k’i karb’a sai iyana awarar shima dan bak’yaso ran innarki ya b’aci, ba k’aramin burgeni kikaiba gsky, wannan ya k’ara k’arfafamini son aurenki, gashi kuma ALLAH yabani yafad’a yana murmuhi.
“”Yanzu nayanke sha warar nema miki makaranta dankema kisami ilmi na addini dana zamani, cikin tsananin farinciki ta dubeshi dan ALLAH dagaske ?? Yaune rana tafarko daya fara ganin fara’arta, ranar daya fara ganinta bata cikin natsuwarta, tunda kuma aka kawota gidansa tana cikin damuwa, cikin murmushi yace in sha ALLAH my Juwairiyy.
Gabansa taxo ta tsugunna tana masa godiya, yace”miyasa kike murna haka ?? Tace” inason karatu amma ban samuba dama inna karima tace in ALLAH yayar da wataran sainayi karatu, gashi kuwa ALLAH ya yarda, nagode ALLAH yajik’an mahaifa, ALLAH yak’ara bud’i.
Yaji dad’in addu”arta, dakuma mamakinta gata k’aramar yarinya sai wayo………………✍????

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I????U MY FAN’s
[10/25, 2:57 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 29~ july~2016
????3⃣0⃣????
????????????
????????

????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA❓????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« washe gari dawuri yatashi yay shirin tafiya wajan aiki, yanufi d’akin Zuwaira tana bayi tana wankewa yay sallama yashiga, jin motsinta abayi yasa shi xaman jiran fitowarta, bayan kamar minti uku tafito, ta tsugunna ta gaidashi, ya amsa cikin sakin fuska, kiyi hak’uri ‘yar aikinki tana nan zuwa munyi magana da ummy xa’a samomiki mai aiki, kanta ak’asa tace ai dama anbarsa zan iya, A’a ai aikin gidannan yay miki yawa, yafad’a yana mik’ewa bari natafi dan dawuri zamu tafi, sai gobe in sha ALLAH xan dawo.
To ALLAH ya tsare ya kiyaye hanya, amin Juwairiyya yashafi gefen fuskarta, bari naje su gwaggo su na nan zuwa inagama harda ummy, ya mik’a mata kwalin waya mai k’yau ga wannan in hajja tazo xata koya miki yanda akeyi, zan Runga kira muna gaisawa kinji, ta d’aga kai ido taf da hawaye, shima yakula da hawayen amma saiya basar dan baya son sata kuka, yabata key d’in d’akinsa gashinan idan kina buk’atar kud’i kije d’akina ki d’auka kinji, yay gaba batare dayajira ce wartaba, ta Window ta rink’a lek’ensa har yaja mota yabar gidan.
“Tadawo ta xauna tana hawaye, lallai rayuwa mai sauyi, idan ta tuna rayuwarta ada saitayita kuka, inda wani yace xata tsinci kanta awannan halin saita k’aryatashi, tabud’e kwalin wayar tana kallo, wayace mai kyau da tsada, ALLAH nagodemaka tafad’a tana hawaye, yanzu k’awarta Safare tanacan da innarta lallai tayi missing d’insu sosai, har inna Asabe datake bata wahala da k’annanta tayi kewarsu, jitake kamar tayi tsuntsuwa taje garesu, tanuna musu irin cigaban data samu.

Sai wajan k’afe 11:15AM su gwaggo sukaxo, amma ba ummy, taji dad’in zuwansu dan harta fara jin tsoro, takawo musu ruwa da lemo, ta tsugunna har k’asa ta gaishesu, bayan sun gama gaisawa gwaggo tai mata bayanin hajja Rabi, sannan tatafi tabar hajja Rabi anan.

++++++++++++++++++
Shikam Sultan yana filin jirgi, inda abokansa sukaita masa murnanar auren nasa, bayan sun koma gefe da Nazir, Nazir yace kai mutumina angwancin ya karb’eka kaganka kuwa har wani sharyning kakeyi saboda hutu.
Sultan ya hararesa kai dai wlhy d’an iskane Nazir, toni wlhy yarinyar nan ko d’aki d’aya bamu tab’a kwanaba bare gado d’aya.
“”Nazir yasaki baki yana kallonsa kai wai dagaske kake??
Oh tunda muke dakai natab’a maka k’arya, aii da tausayi yarinyace k’arama yanxufa tashiga 15years.
Hummm kai dai kabarta ne kawai nikam in nine wlhy bawani d’aga k’afa.
Sultan yay dariya to kai dama aii sai dai addu’a ba tausayi kacikaba, kaga muje masinja sun gama shiga…………….✍????

????Bily????
????Mrs Abdus’salam????
I????U MY FAN’s
[10/25, 3:00 PM] ‪+234 809 777 0370‬: 2~August~2016
????3⃣1⃣????
????????????
????????

????K’ANWAR UWACE????
ko
????KISHIYAR UWA????

????NA BILLKISA IBRAHIM????

»« Hummm Zuwaira ansamu abokiyar hira,, yau daka ganta zakasan tana cikin walwala,, hajja Rabi tsohuwar macece wadda tasan duniya,, dakuma saurin fahimtar matsalar mutane,, ko a saudiyya tana koyama mata yanda xasu zauna da miji,, dan tanada ilimin addini sosai,, yau d’aya data rayu da Zuwaira ta fuskanci abubuwa dayawa atare da ita,, yarinyar k’yak’yk’yawa ce,, lafiyayya rashin gatane kawai ya dakushe rayuwarta,, amma in sha ALLAH zata taimaka mata dan ganin taci ribar zaman aure.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Back to top button