KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

ƘAGAGEN LABARI NE,BAN YI SHI DAN CIN ZARAFIN KOWA BA HAKA BAN YARDA AJUYA MIN KAYANA BA TA KO WANE SIGA

PAGE 1-2

Ɗan ƙaramin towel na jawo nayi ɗaurin ƙirji wanda ya tsaya min iya ƙugu bai sauka kan gwiwai ba,ƙarami na ɗauka na naɗe kaina da shi ta yadda zai tsane.A hankali na fito kamar mai tsoron taka ƙasa ban zame ko ina ba sai bisa ɗan maidaidaicin bed ɗina, Teddy ɗina na jawo wanda ya ke ƙatoto na rungume tare da lumshe idona ina tunanin abinda ya zame min ibada wato tunanin wanda zai aurena,ina mashi wani irin so wanda ba zan iya ƙiyasta shi ba dan tuni soyayyar shi ta game gangar jikina da ruhina.
Amman tambayar da ni ke yawan yiwa kaina wanene shi?a ina ya ke?dan ni kaina ba zan iya cewa ga shi ko ga kamar shi,abinda na sani kaɗai shi ɗin dogo ne,wankan tarwaɗa,mai saje da yalwatacen gargasar ƙirji.”Hummm!”na sauke wani gwabron numfashi saboda ganin suffar shi da nayi a idona ta na min gizo amman banda ainahin fuskar shi saboda in banda dogon gemun shi da ƙayatacen sajen shi babu abinda ni ke iya ƙiyastawa.

“Mimi lafiyar ki kuwa?”cewar Mami wacce ta shigo ban ma san ta shigo ba, murmurshi nayi nace “Mami yaushe kika shigo?”ba ta ban amsa ba sai tea ta miƙo min ta na cewa “ungo karɓa ki sha wannan in ya so kya sauko ƙasa ki ci abinci yanzu Daddyn ku ya yi min waya ya na kan hanyar dawowa ma”karɓar tean nayi na fara kurɓa dan dama ta wannan fannin na ƙware dan ba ka sau ni ke cin abinci ba sai in su Mami sun matsa min ita da Daddy.

Sai da na shanye tas sannan na miƙa mata cup ɗin ,fita tayi ni kuma na nufi wajen coiffeuse ɗita na jawo lotion na shafe farar fatata da shi sannan na shafa kwalli hakan ya fiddo kyawun fararen idona man leɓe na shafawa baƙaƙen laɓana uwanda a ko da yaushe ni ke muradin sun canza launi zuwa jajaye.

Wata baƙar riga tee-shirt mai shatin love na saka tare da sket ɗin ta wanda ya kasance na jeans ne,tsaf na fito abuna gwanin kyawu dukan shap ɗina ya fito irin coca-cola.

Fita nayi zuwa falo Teddy na riƙe da hannuna,tun kafin na ƙarasa ni ke jin hayaniyar yara sama-sama kuma ina jin murya Daddy alamun abun da suka saba ne rigima shi kuma ya na yi masu shari’a.

Imane ce ta rugo da gudu ta nufo ni ta na mai cewa “anty Mimi rufe idon ki zan gwada maki wani abu”tayi maganar ta na mai kamo hannuna,ina shirin rufe idona Ihsane tayi caraf ta na cewa “anty Mimi sabon Teddyn da Daddy ya sawo maki ta ke son nuna maki dubo shi nan”tayi maganai ta na mai ɗago min wani ƙaton Teddy rose dan har ya fi na hannuna girma.

Ihu Imane tayi tare da saka kuka ta na birgima da ƙasa,duƙawa nayi na tallabota ina rarrashinta tare da kamo hannunta mu ka ƙarasa cikin falon.Sai da na zauna sannan na dubi Daddy nace “ina wuni Daddyna?”da murmurshi ya amsa”lafiya lau Mimi ya jikin naki?”nace “ai na ma ji sauƙi”Teddyn ya miƙo min nayi mashi godiya ina mai ɗaukar shi hoto da wayana sannan na ɗora a statut/status a ƙasa na rubuta thank You my dear Daddy???? ina gama ɗorawa na kashe data saboda Mami da ta kawo mana abinci.

Cikin tray guda duk mu ka kewaya mu na ci har da Daddy dan haka al’adar gidan mu ta ke saboda ƙarin zumunci,kamar wacce aka jefo haka Ameera ta shigo ɗakin babu ko sallama idonta bai zame ko ina ba sai kan Teddy na.

“Kam bala’i wai ba dai wani sabon Teddy aka kawo maki ba? Daddy ni shine ba ka sawo min ba?”Ameera ta faɗa cikin jin haushi tare da nuna tsantsar hassadar ta gare ni.
Wata uwar harara Mami ta watsa mata tace “sannu Hajiya Babba (cewa da mahaifiyar Daddy)da fatan kun shigo lafiya?to barka”sosa ƙeya tayi tace “laaa ashe ban gaishe ku ba? please na tuba dan Allah Mami kiyi haƙuri, Daddy ina wuni Barka da dawowa”ta faɗa ta na wanke hannunta ta saka cikin trayn abinci.

Cike da sakin fuska Daddy ya amsa tare da ɗorawa da “Ameera uwayen kishi,to ke ma yau na kawo maki abinda kike bala’in so shikenan sai kowa ya huta da mitar ki”cike da zumuɗi ta cire hannun ta daga abincin tace “Daddy dan Allah bani tun yanzu”tsawa Mami ta daka mata hakan yasa ta miƙe ta na gunguni,har ta fara tafiya Daddy yace “kin ga fah Ameera dawo ki karɓa ta shi nan cikin leda”da murna ta zo ta ɗauki ledar ta na mai fiddo galleliyar wayarta TecnoPop2 ihu tayi ta na murnar yau ita ma ta zama kamar kowa an barta za ta riƙe wayar hannu,dukan su dariyarta suka shiga yi dan kusan kowa ya san yadda ta ke son kullum Daddy ya barta ta fara aiki da waya yau kuma sai gashi ya sawo ya bata da kan shi.

Ko da mu ka gama cin abinci na tattare wanda mu ka zubda na gyaran wurin,kishingiɗawa nayi ina shart ina duba saƙonni abokaina uwanda suka min comment na Teddyn da na ɗora.Murmushi nayi na ɗora Teddyn a ƙirjina nayi selfie na sake ɗorawa nan kuwa wata ƙawata Nabee ta min reply da wlh mijin ki na da aiki,saboda wannan iskancin naki ya fara yin yawa kin ɗauki Teddy kin ɗora a ƙirji sai kace wani mijin ki.Ni kuwa ko dai aljannun ki ke son Teddy ? da ɗan mamaki na maida mata “aljannu kuma?”ta maido min da eh mana tunda sun hanaki ki yi saurayi kin ce duk Mazan duniya ba su burge ki sai mutumen da ke kan ki ba ki san waye ba,to a nan minene in ba alkannu ba? shiru nayi ina tunanin furucinta sai na ga kuma kamar ta na da gaskiya,fuska na ɗan ɓata tare da tashi zaune ina mai maganar zuci “to wai ma ya aka yi na son shi alhalin babu wata alama da ke nuni ya san da zamana?na fara jin tsoro gaskiya”ban san duk abinda ni ke Daddy na ankare da ni ba sai da naji yace “Mimi ya dai?”a daburce na kalle shi ganin ya kafe ni da ido nace “kaina ke min ciwo” “ok tashi ki je ki kwanta ƙila ƙarar tv ce ga kuma ta uwannan (cewa da twins da suke zaune kusa da shi)”jiki a mace na ɗauki Teddyna duka biyun na nufi ɗaki.

Daram ƙirjina ya buga saboda abinda kunnuwana suka jiyo min,na zaro ido waje ina kallon Ameera wacce daga bata waya yau har ta fara aikata masha’a da ita.Ba komi naji ba sai sautin blue Film da ta ke kallo,komawa nayi da baya dan alamu sun nuna ba ta san ma na shigo ba tsabar yadda ta ƙure volume.
A falona na kwanta kan bisa doguwar kujera na rungume Teddyna gam kamar za’a ƙwace min shi, ba komi yasa ni yin haka ba sai tsoro da ni ke ji “ta yaya Ameera da ba za ta wuce 13years ba har ta san kallon blue Film?wane irin ƙawaye Ameera ke mu’amula da su a makaranta?shin dama can ta na kallo koko yanzu ne da Daddy ya bata waya aka turo mata?”wannan sune tambayoyin da ni ke yiwa kaina.
Jin motsin zubar ruwa alamun ta shiga wanka yasa ni saurin shiga ɗakin,wayar na ɗauka wacce ta aje kan bed da sauri na dawo falo “tashin hankali na furta a fili”ganin videos sun fi kala goma cikin wayar alamu sun nuna ta WhatsApp aka turo mata su.
Ɗaya na kunna na tsaya ina kallon ikon Allah yadda turawan ke iskancin su babu ko kunya,har tsawon 5mns vidéo ta ida saurin maida mata wayarta nayi ina mai tambayar kaina “to miye amfanin kallon?”dan kuwa ni dai Allah na gani ban ji wani abu wai shi désir ba,amman dan son sani yasa na turawa Nabee text kamar haka dan Allah wai minene amfanin kallon blue Film?sannan mi ya ke ƙarawa ba’a ɗau lokaci ba ta maido min da amsa domin nishaɗi da rage damuwa sannan za ki ɗan rage zafi da dattin mara???? tsayawa nayi ina ta juya kalaman ta a ma’auni amman sam na kasa fahimtar su wanda kuma lalle ina buƙatar ƙarin bayani.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button