KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin kuka da damuwa ta ke cewa “wlh likita ni ban taɓa yin iskanci ba ta yaya zan samu HIV?ka sake dubawa dai”da sauri na ƙaraso Daddy na bi na daga baya.
Iyani ta goge hawayenta tace “likita ta yaya za ta samu cutar ƙanjamau bayan ka tabbatar min ta na ɗauke da budurcinta har yanzu?koko result ɗin wata ce ka ɗauko?”Dr ya girgiza yace “ku yi haƙuri abinda sakamako ya bada kenan ta na ɗauke da cuta mai karya gangar jiki kuma tuni ta yi tsanani rashin zuwa kan lokaci ta na traitement a gida”
“Na shiga uku ni Nabee wacce irin baƙar rana na ke gani?”Iyani tace “Nabeela na zata ciki ne kika kwaso shiyasa har na kawo ki asibiti a min gwaji amman kika ce sai dai a maki na budurci ashe ga banza ne,to gidan ubanwa SIDA ta shiga jikin ki?”
“Haba ba haka ya kamata ki yi ba,rarrashi ta cancanta a wannan lokacin dan kuwa har da cutar Hanta gare ta ga kuma infections wacce duk ana ɗauka ne ta hanyar zina ko kuma biye-biyen maza na soyayyar shan minti “

Wani kuka ne ya kubce min ban san lokacin da na furta “Innalillahi wa’inna iley raji’un Nabee ke ce a haka?ke ce kika yi baƙi kika rame kika yakuce haka?Nabee kin ga illar zama KARUWAR GIDA ko?mi kuɗaɗen da kika tara suka amfana maki?minene amfanin budurcin da kika yi ta tattali ki na cin duniyar ki da tsinke?”
“Mimi ki yafe min na san ƙarshe na ya zo,na so cutar da ke da mahaifin ki amman Allah bai so ba.Yau gani a wulaƙance babu daraja babu kyawun surar da ke ruɗar maza suna biyata…”
“Na yafe maki duniya da lahira Allah baki lafiya,dan Allah Nabeela kiyi traitement yadda likita yace da sannu za ki samu sauƙi”banda gyaɗa kai babu abinda Nabee ta ke ta rairafo za ta zo wajen Daddy yayi saurin cewa ya yafe mata ya na mai jan hannuna mu ka koma can cikin room ɗin da triples suke mu ka ɗauko su mu ka dawo gida.

Wuni ranar nan haka nayi shi babu daɗi,sosai na ƙara tsorata da lamarin duniya yadda ya ke juyawa kamar juyin waina.Daddy kasa fita yayi doli ya zauna kusa da ni ya na min nasiha sannan ya ƙara da cewa “ki kula min da yara na ki basu tarbiyya ta ƙwarai ta yadda Ubangiji zai yi alfahari da mu na tsare amanar da ya ba mu”rungumesa nayi nace “in shaa Allah mijina kuma ka yafe min zargin da nayi ma na ka kasance da Nabee”ƙirjina ya shafo yace “bai komi my Life”ya faɗa ya na mai kai bakinsa kan nawa.

***Bayan wasu shekaru
Abubuwa dayawa sun faru,ciki kuwa har da samun lafiyar Fauziya na yoyon fitsari tuni tayi aure ,Fadila ma masha Allah ta jerawa Nasir yara sannan tuni ta fara aikin gwamnati mai tsoka ta canza rayuwar Anna wacce ta aza buri akan ta Nabeela ma ana ta ɗaukar magani a ƙarshe kuma ta auri Alhaji Tanimu wanda yayi sanadiyar laƙa mata ƙanjamau cike da baƙin ciki ta baiwa tsohon kyautar budurcin da samari da dama sun so karɓar sa ta hana.Iyani kuwa tuni tayi saranda daga shegen kwaɗayi na son kuɗi tare da nadamar rayuwa.

Ameera ma ta na zaune ƙalau da mijinta Abu Maleek,haihuwar su biyu duk maza.
Twins kuwa sosai suka girma ana ta karatu,Mami da Dr Ibrah ma an buɗe babin soyayya zahiri bayan ta ɓoye da aka yi.

A ɓangaren Daddy kuwa tuni na cika mashi gida da ƴan mata har shidda bayan haihuwar ƴan uku na haifi Agaishat mu na kiranta da Ummi sai Twins Nabeela da Nadeera sosai mu ke gudanar da soyayyar mu ni da ƴaƴana da mijina.
Har yanzu Daddy na ke kiransa duk da yayi bakin ƙoƙarin sa na ganin ya hana ni, wannan yasa yarana ma suke kiran sa da Daddy.

Ina zaune ina koyar da yarana karatu alƙur’ani Daddy ya shigo,duk suka fara yi mashi sannu da zuwa murmurshi kan fuskata na ke kallon su yadda ya ke rarraba masu abinda ya shigo da shi duk wanda aka ba sai yayi ihu koma gefe ya na murna.
Kusa da ni ya ƙaraso bayan ya gama da yaran ya jawo ni jikin sa ya zura min zoben gold da yatsana ya na mai furta “i love You so mush my farin cikin rayuwa”ƙanƙamesa nayi ina mai ɗora hannuna saman ƙirjinsa nace “na gode miji na gari”maganga ya raɗa min a kunne nayi murmushi na saci inda yara suke sai na hankalinsu bai kan mu,hannun shi na ja mu ka fara taka step…..

ALHAMDULLAH !!!!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30

Leave a Reply

Back to top button