KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ina ruwana da ƴar ki ni tawa na sani dan haka ki shaida mashi da zarar ya dawo,gobe kotu za ta raba mu”ta na gama faɗa ta fice,tsuki Nabee tayi ta koma ɗaki a zuciyarta ta na mamakin yadda har ƴan mata suke sakacin baiwa namiji kansu kamar shashashu koko dan ba su ƙwarai a barikin ba ne ?oho


Cike da masifa Hajiya Babba ta shiga balbale Alhaji Kamal da faɗa sai kace ba sirikin ta ba,a haka dai ta tattare kayan su ni kuwa sai murna ni ke zan koma gida gun Daddy.

Washegari 16h tuni motar mu ta dira a Maradi, drever Daddy ya aiko ya ɗauke mu.
Gidan Hajiya Babba aka kai mu,da murnata na buɗe mota na fito na shiga da gudu ina “Daddynaaa “cak na tsaya gani baƙin fuska duk miƙewa suka yi suna kallona nima haka sai dai na tsayar da dubana ne ga mai irin fuskata.

Murmushin da yafi kuka ciwo Daddy yayi yace “Mimina “a Shagwaɓe na je na faɗa jikinsa ina turo baki nace “i miss You Daddyna shine ka ƙi tafiya ka tarbo ni ai da kai na so idona su fara gani sai kawai ka turo min drever”laƙace min hanci yayi yace “ba ki ga baƙi ba ne?”juyawa nayi gun su sai na ga ashe mu su ke kallo.

“Yau na ga ragguwa yarinya dan rashin tausayi kika bar ni da dakon ƙaton aljanin ki,ina dalili yarinya kamar wata…”maganar ce ta maƙalewa Hajiya Babba ganin ashe da mutane falon gaisheta suka shiga yi ta na amsawa tare da yi masu kallon ko ina ta san su.

Teddyna ta jefo min ta na hararena nayi dariya ina kakaɓe shi dan ya faɗi, Hajiya Babba na zaunawa Daddy yayi gyaran murya ya fara bada labari tiryan-tiryan tun daga ranar da aka ɗauko ni daga gidan marayu.

Hawaye shararaaa haka suke zuba a idona na ƙurawa Daddy su ƙyaftawa ban yi,hutu na wucen gadi kwanyata ta tafi ba ta dawo ba sai da naji Daddy na cewa “Mimi ga biologique parents ɗin ki nan”…..
[07/12 à 07:45] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822

Page 37-38

Banda kallo babu abinda nayi saboda sam zuciyata ta kasa yin aikinta daidai ya da ya kamata, Agaishat ta taso daga inda ta ke ta zo ta rungume ni wani yammm naji da sauri na sauke ajiyar zuciya ita kuwa kuka ta ke.
Samun bakina nayi da furta “Momyyy”cire ni tayi daga jikinta ta ƙurawa fuskata ido ta na murmurshi tace “dauther ina son ki sosai na godewa Allah da gwada min wannan rana,ta so ki je gun Abban ki saura kaɗan zuciyarsa ta buga saboda ke”ta faɗi haka ta na mai miƙar da ni tsaye mu ka nufi gun dattijon arziki wanda ya ƙura min ido tun shigowa ta.

Duƙawa nayi zan gaishe da sauri ya jawo ni na faɗa jikinsa,wasu sanyayun hawaye suka shiga malala a idon shi “Fadimatu na? Allah raya ki a kan sunnah ya tsare min ke daga sharrin ƴan hassada da baƙin ciki…”kuka ne yaci ƙarfinsa sai ya ƙyale.

Hajiya Babba wacce tayi suman zaune tace “oh Allah duniya babu kyau an raba tsoka da jini gudun mugayen ɓoye,ina ta Rahamun ta ke ta san da maganar ?baiwar Allah ta so Mimi kamar ranta”ɗagowa Daddy yayi da jajayen idonsa yace “na saketa ai”da sauri duk mu ka kalle shi dafe zuciyar shi yayi sannan yace “laifi ta yi min mafi muni wanda duk mai ƙaunata ba zai bari na cigaba da zama da ita ba,Rahama ta cuce ni Hajir mu ta rasa da wanda za ta ci amanata sai da babban abokina”

“Mine?cin amana kuma?”cewar Hajiya Babba shiru Daddy yayi dan sai yanzu ya gane da bai kamata ya faɗi haka ba “Mimi tashi kije ki yi wanka”cewar Hajiya Babba ,jiki ba ƙwari na miƙe tare da nufar part ɗin ta.

Sai bayan Mimi ta tafi ne sannan Daddy ya fayyace masu komi Hajiya Babba kuka ta saka Momy na bata haƙuri,Abba kuwa nasiha ya shiga yiwa Daddy dan ya ɗauke shi tamkar ɗan cikinsa.
Dr Ma’aruf ya gyara zama yace “gobe ka same ni a asibitin mu zan duba na hauda ka kan magani, sannan ka kawo min result ɗin da sauran suka yi ma gwaji” Daddy yace “in shaa Allah na gode”.

Dakyar suka daidaita nutsuwar su suka fara shan fruits,ni kuwa ko da na gama wanka na shafa mai da turare kayan da Hajiya Babba ke tara min na ciro riga t-shirt fara da buje blue na jeans.
Tunda na fito mu ka haɗa ido da Daddy wanda ke saiti da ƙofar ɗakin, murmurshi na sakar mashi shi kuwa Daddy zuciyarsa ce ta shiga bugawa ganin na shanun Mimi sun yi tsiriri a tsaye suna zagin sa????kawai haka yaji haushi ko bra ba ta saka ba za ta fito haka alhalin akwai mutane falon.

A shagwaɓe na faɗa jikin Daddy daga zuwana “shine ka fara ci ka manta da ni”na faɗi haka ina mai amshe apple???? ɗin hannunsa, murmurshi yayi yace “Mimi uwar rigima ai na zata ma kin kwanta saboda gajiya,yanzu yaya kike ji komi normal ?”Kai na gyaɗa na guntsiri apple ɗin daidai shatin haƙoran sa sannan nace “Daddy wai sai yaushe Tantie Munawara za ta sauka daga dokin kafiya? ni dai na matsu na gan ta mijinta na da kirki”Daddy yace “sai ranar da kasuwar apple ta tashi”ya faɗi haka ya na kimtse dariya,ƙafafu na shiga bugawa ina kukan shagwaɓa nace “Allah ba santi nayi ba kawai dai na tambaya”

“To Sarkin surutu sai ki sauko ki ci abinci dan na san in an biye ta taki ba za ki ci ba”cewar Hajiya Babba ta na juye dafafun zabi wanda suka sha jar miya kallon Daddy nayi nace “ni ba zan ci ba kar na ɓata hannu na”murmurshi yayi dan ya san mi ni ke nufi a duk lokacin da nayi sha’awar ya ciyar da ni da hannunsa haka ni ke faɗa.

Hajiya Babba ta taɓe baki tace “na ga yaushe za ka barin sangarta ƙatuwa har haka wai fah sai dai ya bata a baki kamar jaririya “cikin shagwaɓar da ta zame min jiki nace “ni dai ba ƙatuwa ba wai duka-duka ma nawa ni ke da ake sa min ido?haka fah jiya ta ƙi ban abinci a baki alhalin Daddy cewa kayi ta je ta kula da ni”duk dariya aka yi Hajiya Babba tace “ah to ni ban iya gantali ba ƙatuwar budurwar da ko yau sai a ɗaura mata aure zan baiwa abinci a baki dan dai duniya ta zo ƙarshe can shi da ya sangartar da ke ya baki”

Baki na turo nace “to na ma fasa ci ban so”na faɗa ina shirin tashi Daddy ya mayar da ni na zauna “miye haka Mimi ki nutsu mana ko ba ki ganin ba mu ɗaya ba ne akwai baƙi?koko so kike Abba yace na sangartar mashi da yarinya?”Daddy ya raɗa min a kunne,turo baki gaba nayi na juyo ina facing shi har zan yi magana ya aza min yatsansa a baki.

Cikin plate Hajiya Babba ta zuba min Daddy ya karɓa ya na bani shi ma ya na ci,yayinda su kuma suka gewaya suna ci su ma.
Ƙurawa Daddy ido nayi ina jin wata irin ƙaunarsa a raina,shi ma jefi-jefi ya ke kallon ƙwayar idona.Sai da mu ka ci mu ka ƙoshi sannan Daddy ya aje plate ya zuba mana jus,miƙewa nayi na fita zuwa harabar gidan.
Iskar Ubangiji na shaƙa na lumshe ido,an ɗauki kamar minti goma suka fito Hajiya Babba riƙe da hijabi a hannunta saka min tayi kafin na tambayeta lafiya naji Daddy na cewa “Mimi sai in na zo ki kula da kan ki”idona ne suka yi rau-rau na kalli Daddy nace “zuwa ina?”Hajiya Babba tace “ai kaji sakalci Abban ki za ki bi kuje can gida”wani kukan kura nayi na faɗa jikin Daddy na ririƙe shi ina kuka tare da girgiza kai.

Rumtse ido yayi ya na jin abubuwa na mashi yawo a kwanya,na ɗaya saukar dukiyar Fulaninta a kan ƙirjinsa na biyu sautin kukanta.Dakyal ya aro jarumta ya shiga bubuga bayanta,cikin murya mai taushi gami da kasala yace “yi shiru Mimina ai zan zo zuwa dare “kafaɗa na maƙe ina gyara kwanciya kan ƙirjinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button