KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ku shiga mota ina zuwa”cewar Daddy,wucewa suka yi Hajiya Babba kuma ta koma ciki saboda karyewa da zuciyarta tayi.
Haɓata ya ɗago ya ƙura min ido,ta saman gashin idona da suka jiƙe da hawaye ni ke kallon shi.Iska ya fara hura min a fuska na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya, daidai saitin laɓana naji ya sauke na shi kafin ya janye yace “ina son ki,ki kula da kan ki ke ɗaya ce mace a can ƴan uwan ki na can na jiran ki saboda bege”idona na a lumshe nace “Daddy mu je tare”murmurshi yayi mai ɗan sauti ya cire ni daga jikinsa ya ja hannu na zuwa mota ina hawaye ina ji ina gani Daddy ya buɗe seat ɗin baya ya sanya ni ya rufe.Wani kukan ne ya kubce min ina leƙen Daddy ta glass Ma’aruf ya yi mata key mai gadi ya buɗe mana gate.

**Cike da tashin hankali Mami ke duba takardar,ihu tayi ta dire daga bisa gado ta fito daga cikin asibitin.Direct bakin hanya ta nufa ta tari mai adaidaita,ya na sauketa ta shiga ciki a falo ta tarar da Ameera ita da Twins duk sun dawo daga school.
Ɗakinta ta shiga ta ɗauko kuɗi ta miƙawa Ameera ba tare da tace komi ba ta nuna mata hanyar waje hakan yasa Ameera fita,Twins kuwa sai sannu da dawowa suke yi mata amman ta ƙi kula su.
Dr Ibrah ta kira ta shaida masa komi dariya ya shiga ƙyarƙyatawa kafin ya kashe kiran,ba’a fi minti goma ba ya zo gidan.Da gudu Twins suka rungume shi suna mashi oyoyo,Ameera kuwa yi tayi kamar ba ta san da zuwan shi ba.
Mami ta fito ta na kuka,Dr Ibrah ya taɓe baki yace “to miye na kuka dan ya sake ki?kuma fah yaran nan duk kin san ni ne mahaifin su to damuwar ta mi ce?”kai Mami ta girgiza tace “na cutar da Mu’azam na haifa masa shegu cikin gida ya ciyar da su haɗi da ɗawainiya yanzu kuma har gidan ya ce ya bar min ba zai iya sake rayuwa cikin sa ba”ta ida maganar cikin fashewa da kuka.
Ameera ta miƙe tsaye ta na jin abun kamar almara “ni ne sabon Daddyn ku kun ji ko?daga yau Daddy za ku kira ni kun ji ko?”Dr Ibrah ya faɗa ya na rungume Twins .
Kuka Ameera ta fashe da shi ta fita da gudu da sauri Dr Ibrah ya fito ya na kiran sunanta ganin haka yasa mai gadi liƙe ƙofa.
Ƙarasawa Dr Ibrah yayi ya ɗauketa da wani gigitacen mari yace “gidan uban wa za ki je?”cikin kuka da rashin tsoro tace “gidan uban ka zan je shege zakka ɗan asara da ba zai ganin Annabi ba da yarda Allah mutuwa kare za ka…”waro ido yayi ya sake ɗauke ta da mari kafin ya fincikota ya shiga bal da ita a ƙarshe ya jata ƙiii zuwa ɗaki.
Banda kuka babu abinda Mami ke yi tare da dana sani maras amfani,ganin bugun da Dr Ibrah ke yiwa ƴarta yasa ta miƙe da sauri Ameera tace “kar ki taɓa ni ban son ki ban ƙaunar duk mai ƙaunar ki sannan sai na shiga duniya na zama shaƙiƙiyar tantiriya sai na kawo maki shegu kin raina tunda rainon su kawai kika iya”tayi maganar ta bubuga hannunta da table.
Cak Mami ta tsaya ta na jin zuciyar ta na barazanar faɗowa,tabbas ta san Ameera ta aika yin karuwanci ga ɗiyar *KARUWAR GIDA* ai ƙaramin abu ne amman sam ba za ta lamunta ba.

***GIDAN ALHAJI

Tamkar wata tv haka duk suka sani a gaba su na kallo duk yaran murmurshi kan fuskarsu yayinda matan suka turniƙe fuska kamar tsohon kashi.
Momy kuwa ta na zaune kusa da ni ta riƙe hannuna gam,Abba na zaune daga gefe ya na murmurshi Dr Ma’aruf yace “tanti amaya ya kamata a kai little ɗaki ta huta kin sa da gajiya a jikinta”murmurshi Momy tayi ta ja hannuna zuwa ɗakinta.Lafiyayen gadonta ta nuna min na kwanta bisan shi, hasken ɗakin ta kashe min na rungume pilow ina jin wasu hawaye na ziraro min kewar Daddyna ni ke yi murmushi nayi tuna ba shine biologique parent ɗina ba…..
[08/12 à 16:05] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822

Page 39-40

Kamar yadda Daddy yayi alƙawali da dadare sai gashi kuwa,kowa na gidan ya hallara banda Mimi wacce rashin sabo ya sa tayi zamanninta a ɗaki.

gani a cikin gidan ku amman ban gan ki ba shine text ɗin da na karanta wanda ya fito kuma daga Daddyna,zumbur na miƙe ko kallabi ban saka ba balle wani hijab da ɗan guduna haɗi da murna na nufe shi na faɗa jikinsa duk da kuwa ƙoƙarin hana ni da ya so yi.

“Daddy ka zo ka tafi da ni ne?dama ni na gaji ni ɗaya babu su Twins kuma Teddyna ya na can gun Hajiya Babba”na faɗa ina mai kwantar da kaina bisa kafaɗarsa,sumar kaina ya shafa yace “Mimi ai kin zo gida kuma ke da can sai in kin zo ganin mu”da sauri na girgiza kai nace “a’a Daddy dan Allah kar ka bar ni nan wlh ban san kowa ba kuma fah su nan babu mace ƴar yarinya to da wa zan yi hira?”dariya kusan rabin mutanen suka yi kafin Dr Ma’aruf yace “ai shiyasa Abba ke son ki dawo nan ɗin amman kar ki damu zan cewa Fatima (cewa da Ɗiyar shi)ta dawo nan da zama”kafaɗa na maƙe na jimƙe hannun Daddy.

Mutanen falon duk Alhaji ya sallama ya bar Momy da Ma’aruf kawai wanda tun ɗazu suka yanke shawara duk da ba su san ko Mu’azam zai karɓeta ba ni kuwa ina jikin Daddy na lafe kamar mage.
Gyaran murya Abba yayi yace “Mu’azam banda bakin gode maka sai dai in ce Allah saka maka da alkhairi ya biya maka buƙatunka duniya da lahira,sannan a ƙarshe ina neman wata alfarma dan Allah amman sai ka min alƙawari za ka amince”ɗagowa Daddy yayi kalli Abba murmurshi kan fuskar shi yace “to Abba ina jin ka in shaa Allah “

Sai da Abba ya sake nutsuwa sannan yace “ina son ka cigaba da riƙe min Fadimatu a gun ka na san za ka fi kula da ita sai dai wannan karon ba’a matsayin Ƴa za ka riƙe ta ba a matsayin mata”da sauri Daddy ya zabura yace “Mata?mata dai?aure? Mimi? Abba…”hannu Abba ya ɗaga yace “kar ka manta ka min alƙawali”Daddy yace “ita fah Mimi yarinya ce har yanzu kuma kamar an cuce ta an gama ta da tsoho”dariya Ma’aruf yayi yace “haba Mu’azam duka-duka nawa kake ba fa za ka wuce 45years ba amman bari mu tambayi Mimin Daddy ko ta amince”ya ida maganar cikin barkwanci.

Ƙara ɓoye fuskata nayi cikin ƙirjin Daddy dan duk abinda su ke ina jin su magana ce kawai ban yi,yadda Daddy ke shafa gashin kaina yasa barci ɗauke ni ban ma san abinda suka yanke ba akai.

Washegari da asubah Momy ta tashe ni nayi sallah,ina gamawa na zumɓuro baki ganin ashe wayo Daddy ya yi min bai tafi da ni ba.
Momy da ke daga gefe ta na lura da Mimi kai kawai ta girgiza ta na jin son ƴarta har ƙasanƙasan zuciyarta,zuma ta miƙo min wacce ta sha haɗi ni kuwa Uwar son zaƙi na shiga sha.
Wayata na ɗauka na danna kiran Daddy sai turo baki ni ke yi ina tsara yadda zance mashi amman har ta gama ruri bai ɗauka ba.
Daddy kuwa da ke can kwance cikin ɗakin shi tun na farko kafin su tashi daga gidan Hajiya Babba kwanci ya gyara ya na mai cigaba da kallon hotunan Mimi,sam ya kasa daina kallon ƙirjinta tunda aka bashi ita aurenta ya samu kan shi da kalle surar jikinta.

Kiran ya maida mata,ni kuwa ganin appel ɗin shi yasa na ɗauka cikin sanyin murya nace “Daddyna ina kwana?shine jiya ka tafi ka bar ni a nan haba dai”na ida maganar cikin shagwaɓa.

Numfashi ya fesar kafin yace “Mimina?”a yadda yayi maganar yasa ni yin shiru ina jin zuciyata na bugawa “Mimina?”ya sake faɗa “uhum!”murmurshi yayi mai sauti yace “rigima ko?”ido na rufe na turo baki gaba nace “ba kai ne ka bar ni ba”Daddy yace “yaushe kike son dawowa nan ɗin ?”cikin zaƙuwa nace “yau ni ko yanzu ma”Daddy yace “kenan na faɗawa Abba a ɗaura auren yau?”kai na girgiza kamar ya na gani na dan wani tsoro ne ya zo shige ni nan take.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button