KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL


Ganin kukan bai yi min yasa na tashi na shige toilet na yi wanka tare da shiryawa cikin riga da wando na sous-vêtement farare,kiran Nabee ne ya shigo wayata da sauri na koma falo inda na barta,na ɗaga kafin in ce wani abu ta riga ni “my lovely dauther kiyi haƙuri jiya ina can wani gun ne shiyasa ban ɗauki kiran ki ba kuma sai na shigo a gajiye washhh Allah”ta ƙare zance ta na mai yin miƙa.
Rumtse ido nayi ina jin takaici wato ita da Daddyna suka sheƙe ayarsu shine ta ke gayamin?tabbas kuma ƙamshin da naji Daddy na yi irin na turaren Nabee ne kenan zargina ya zama gaskiya?
Jin ban ce komi ba ne yasa Nabee cewa “ina my sugar Daddy ya ke?”a tsawace nace “Nabee ki shiga hankalin ki wlh in kika yi kuskuren gwada karuwancin ki ga….”sauran maganar ce ta maƙale min ganin Daddy ya shigo ya na kallona.

Can ɓangaren Nabee ta sheƙe da dariya tace “na nawa kenan?wai an cewa kuturu Allah ya la’ance ka ai tuni…”ban ida jin abinda tace ba Daddy ya amshi wayar ya kara a kunnen shi rumtse ido yayi jin abinda Nabee ɗin ke faɗa,”yanzu ita ba ta ko jin kunya Ƴata ta ke gayawa wannan maganar?”Daddy ke faɗa a zuci kafin ya kashe kiran ya maido hankalin shi gare ni.

Kaina a duƙe tuni idona sun fara ɗigar da ruwan hawaye,ɗago haɓata yayi sai kawai ya jawo ni zuwa jikin shi dan bai san abinda zai ce ba ta ina ma zai soma?
“Daddy ka kai ni gun Hajiyar mu ina son komawa can da zama”na faɗa cikin muryar kuka bayana ya bubuga yace “no Mimi ba za ki koma can ba zan dai kai ki sai ki wuni in ya so da marice sai naje na ɗauko ki kin ji?”kai na ɗaga ina mai barin jikin shi na nufi bedroom.

Daddy kuwa huci ya sauke,ya shigo ne dan ya ga jikin Ameera sai kuma ya tarar da wannan kayan baƙin cikin na KARUWAR GIDA da ta ke tsarawa ƴarsa abinda zai sa zuciyarta ta buga,dan kuwa ya san ba iya abinda ya faru ba ne kawai Nabee ta gayawa Mimi har da ƙarin ta kawai dan sawa Mimin tension.

Ƙaton hijab kawai na aza bisa tare da ɗaukar coton(auduga)dan wani sa’in period ɗina ya na dawowa duk da dai dama kwana ɗaya ne ni ke yi ya tsaya.
Kallona yayi yace “Mimi a haka za ki je?”kallon kaina nayi nace “mi nayi Daddy?”kai ya girgiza dan ya gane wayon da Mimi tayi na saka bungulin hijab a tunaninta bai hangi ƙafarta ba, ya ga har yanzu riga da wando ne.

Kai na ɗan sosa sai kuma na fuske na ɗauki Teddyna,gaba ya yi ina bin shi a baya har mu ka fito a farfajiya.
Seat ɗin mai zaman banza na shiga Daddy zaman drever,ai kuwa ƙamshin turaren Nabee ne ya cika motar duk sai naji raina ya ɓace tare da jin haushin Daddy “wato a cikin motar ma suka kasance?miyasa Daddy zai min haka ya bayyana sirrin shi ga sa’ar ƴar cikin shi?duk ƙoƙarin da Mami ke yi bai gani ne komi?”Teddyna na rungume tare da ɓoye fuskata har mu ka zo gidan Hajiya Babba.

Mu na shiga falon Twins suka rugo suka rungume ni,cikin dariya nace “to ku sake ni kar na faɗi,ashe nan kuka zo ?ni shaf na ma manta da ku shiyasa ban ji motsin ku ba”Imane tace “eh jiya Daddy ya kawo mu yace nan za mu zauna har sai kun samu lafiya”murmurshi nayi na ja hannunta dan tuni Ihsane ta bar guna ta nufi Daddy .

Fitowa Hajiya Babba tayi daga kitchen gaisheta nayi ta amsa tare da tambayata jikina,nace “da sauƙi alhamdullah”Daddy ne ya matso suna gaisawa da mahaifiyar ta shi amman duk rabin hankalin shi na ga Mimi wacce ta rakuɓe ta rungume Teddynta tayi ƙasaƙe alamu tunani ta ke.

Tashi Hajiya Babba ta yi ta koma kitchen zuwa can suka fito ita da mai aikinta wacce ke riƙe da ƙaton tray,hijab ɗina na cire na zo na zauna ƙasan Capet na fara haɗa abun breakfast ɗin.

Doya ce aka soya da ƙwai tare da yin wata ƴar sauce ta mayonnaise sai kayan tea,a cikin ƙaton plate n’a zuba duk suka gewaya suna ci har da Hajiya Babba ni kuma tea ni ke sha ina satar kallon Daddy yadda ya ke ci a nutse sajen fuskar shi na ɗan motsawa a hankali hakan ba ƙaramin tafiyar min da hankali ya yi na.

Ina kurɓar tea ina kallon shi tare da sakin murmurshi,kofin tea ɗin na aje na kwanta bisa salon mai zaman mutum uku Teddyna rungume a hannuna.
A hankali na fara rera waƙa wacce taƙamaima ban san ya ake yin ta ba kawai in na wuce a hanya wani sa’in ina jin ta a gari,to kawai yanzu sai na samu bakina da rerata Yaushe ne buƙatar za ta biya yau ne ko gobe?????da ina da hali janyo shi zan yi mu yi zobe????da siyasa ce tabbas da nai yi zaɓe???? da sauri nayi shiru jin Hajiya Babba na cewa “iyeee!takwara ta aure ta ke so”da sauri na miƙe zan ruga sai aka yi rashin sa’a Daddy ma da ya miƙe ya na dariya zai wanke hannun shi sai mu ka yi karo dafe goshi nayi zan faɗi sai kawai ya taro ni na faɗa jikin shi.

“Subahanallah Mimi kiyi a hankali mana,ga shi kin sa na shafa maki maiƙon mai a kaya”cewar Daddy ya na mai daidaita min tsayuwa,baki na turo gaba ina kallon inda yayi tâche ɗin.
Su Twins dariya suka shiga yi min ganin ina gunguni tare da buga ƙafafu a ƙasa, murmurshi Daddy yayi yace “ayya ki yi haƙuri ai gobe ma zan saya maki wasu tunda na ga so kike ki zama kamar ƴar ƙwllo kullum cikin kayan gudu”Hajiya Babba ta karɓe zancen da cewa “ai kuwa dai yau na ga sakalci goɗai-goɗai da ita ka tsaya ka na sangarta ta a haka ai ba gata kake mata ba dan kuwa babu namijin da zai ɗauki sakarcin takwara komi kuka sai kace pampon an taɓa ido ba su tsayawa sai zubar da hawaye”baki na kwaɓe nace “Daddy kaji ko Allah yanzu Hajiyar mu ta bar ji da Ni kawai ka mayar da ni gida “na ƙarashe maganai ina yin kukan wasa.

Kai Daddy ya girgiza ya shiga kitchen ya wanke hannun shi,ko da ya fito bai tarar da Mimi ba dan tuni ta wuce ƙurya ɗakin Hajiya Babba.
Sallama yayi masu ai kuwa Twins suka laƙe mashi doli ya tafi da su gida,Hajiya Babba ta miƙe ta shigo ɗaki “binciken miye ake min a ɗaki?”ban ko juyo ba na shiga duba kayan da ta ke tara min na ciro wasu baƙaƙen riguna guda biyu,da sauri ta karɓe su ta na cewa “ba fah zan baki su ba sai kin yi aure dan haka kar ki yi wahala”na turo baki gaba nace “dan Allah Hajiya Babba ki bani Allah ina son yin kwalliya da su ne”dariya tayi irin ta su ta tsofi tace “ai kam ba zan bayar ba ko Amadu dakyar na bashi turaren da ya kai maki jiya shi ma dan ya nace ne”.

“Wane turare Hajiya Babba?”na tambayeta ta bani amsa da “turaren da dai na saba saya maki tun ki na ƙarama amman dan shegantaka shine kika canza wani kala kika bar saka shi shiyasa ni ke tara maki shi a nan in kin yi aure sai ki cigaba da amfani da shi,na san mijin ki zai so ƙamshi saboda ko a can Saudiyya matan su shi suke shafawa”shiru nayi ina tunani “to ko dai Daddy bai tafi gun Nabee ba?dan ban mancewa da Nabee ta ji ƙamshin turarena ne tayi ƙwaƙuwa na bata ɗaya sai kuma ta cigaba da sayen irin shi yayinda ni kuma na canza wani iri daban.To amman in haka ne miyasa Nabee za ta gayi maganar ɓatanci a kan Daddyna har tace sugar ɗin ta ne?”.

Wata rose ɗin riga da Hajiya Babba ta yaɓa min a fuska ya sa ni dawowa daga duniyar tunani,ihu nayi na rungume Kakata nace “thank You my granny,ya aka yi kika san ina son launin rose?”na tambayeta ina mai sake ɗaga rigar.
“Ko uban ki ai na san launin da ya fi so balle ke da aka haifa jiya”cewar Hajiya Babba ta na mai maida kayan yadda suke,”kai Hajiya shine har da saka Daddyna?to ni dai kar ki rufe kayan ki bani mayafin da zan haɗa rigai”ba ta tanka ni ba ta jawo min wani farin adiko fari sol wanda aka yi ma adon duwatsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button