KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL
Abincin ta zuba haɗi da ɗaukar exotic sannan ta fito,kiciɓus suka yi da su Mami wacce ta rako Dr Ibrah.
A ɗan daburce Mami ta kalleta tace “yo ba ki je asibitin ba?”dan dama Dr Ibrah ya gaya mata yadda suka yi,kai Ameera ta girgiza tace “na tafi dawowa nayi ɗaukar abinci” Mami ta ce “toh lafiya kike kuka ko wani abun ne?”kallon mahaifiyarta ta tayi sannan tace “Daddy ne tun zuwan mu bai tashi ba kuma an naɗe mashi wuya”ta ƙarashe maganar ta na fashewa da kuka wata ajiyar zuciya Mami ta saki dan ita azaton ta ko tun ɗazu Ameera ta dawo ta ganta ita da Dr Ibrah.
“Allah baku lafiya ga baki ɗaya ke ma ya kamata ki kula da kan ki sosai ni zan wuce”cewar Dr Ibrah,godiya Mami tayi kafin tace “ni zan koma ɗaki na kwanta ki gaishe shi da jiki”bayan Mami Ameera ta bi da kallo kafin ta fita ta na yiwa Mamin addu’ar shirya tare da alƙawarin ita ma sai ta zama KARUWAR GIDA ko dan ta ramawa Daddyn ta????
***Niamey
Mu na sauka babban birnin Niamey na sake kiran wayar Daddy a karo na barkatai wannan karon kuma a kashe najita,cikin sanyin jiki na kira lambar da ya bani yace in mun sauka na neme shi.
Ashe tuni ma ya na cikin gidan EMA,gaishe shi nayi ina mai nuna mashi Hajiya Babba wacce ke ta masifa an ƙi fiddo mata kayan su daga cikin Boot????kai ya girgiza a zuci yace “su Hajiya Babba manya ashe har yanzu ta na nan dai yadda na santa”ƙarasawa yayi gun ta ya gaishe ta amsawa tayi ta na mai cigaba da mita .
Har mota ya kai su sannan ya dawo ya fara ɗaukar masu kayan da suka raɓe,sai da ya gama sannan ya zagaya ya zauna seat ɗin drever.
A hanya ya ke ɗan jan mu da hira har mu ka kawo gidan da Daddy yasa aka kama mana haya,a gajiye duk mu ka shiga ciki Alhaji Kamal ya fita nemo mana abinci.
Ko da ya dawo har mun yi wanka mun canza kaya haɗi da yin Sallah Asar,gasasun kaji ne haɗi da frite ya sawo mana sai lemun kwalba.
Hajiya Babba ta baje sai ci ta ke ni kuwa shiru nayi na koma gefe ina tunanin Daddyna ko lafiya bai ɗaukar kira ita kuwa Mami fushi ni ke da ita dan a mota Hajiya Babba tayi ta faɗa min mugayen halayenta lokacin da suka zauna gida guda haka ba ta tausayin Daddyna.
“Mimi lafiya ?ke ba za ki ci abincin ba?”cewar Alhaji Kamal,Hajiya Babba ta ja baki tace “ta ya za ta ci ta tsaya tunanin Abbanta sai kace wani ɗan yaro duk ta wani damu dan bai kira ba”dariya Alhaji yayi ni kuwa na turo baki gaba cike da jin haushi na nufi ɗakin da mu ka ajiye kaya wanda ya ke ɗauke da matala 3places ta sha shimfiɗa ta alfarma.
A can Maradi kuwa sai wajen sallah magrib ya farka,sannu Ameera ta shiga yi mashi bai amsa ba kawai dai ya sakar mata murmurshi.
Likita ta fita ta kira ya zo ya duba shi “gobe zuwa safe in shaa Allah za’a sallame ka bayan ka biya kuɗin da aka yi ma aiki”cewar Dr ɗin ya na kallon Daddy.
“Na gode sosai da kulawa”cewar Daddy, toilet ya nufa yayi wanka haɗi da alwala.Saloli ya shiga yi tun asubah har magrib ya na nan zaune har aka kira isha’i,bayan ya gama ya juyo ya kalli Ameera yace “Ameera samo min exotic”da toh ta miƙe ta fita zuwa frigon asibitin lemun da ta aje ta ɗauko mashi ya karɓa ya yi Bismillah ya sha.
Bayan yayi Hamdallah da Ubangiji ya ke tambayarta ya aka yi ta sani?babu abinda da ta ɓoye mashi tun daga zuwan Dr Ibrah maganar da taji su na yi ne da Mami kawai a ba ta gaya mashi ba.
Shiru Daddy yayi ya na saurarenta tabbas zargin shi ya zama gaskiya,ta yaya Dr Ibrah zai zo gidan shi bayan duk abinda ya faru tsakanin su?bai ce komi ba sai Twins da ya ƙurawa ido suna sharar barci saboda gajiyar da suka yi.
Washegari tun da safe Dr Ibrah ya sake zowa wai ya zo dubiya ne Amman a zahiri cashe ayar su suke shi da Mami a falo,sai masha’ar su suke.
Daddy kuwa sai da aka sa wayar shi da aka ɗauko daga mota caji yayi masu transfer kafin ya nufo gida Ameera na addu’ar Allah ya toni asirin mahaifiyarta.
Mai gadi na buɗe gate Daddy ya cinno hancin motar shi cikin gidan….
[28/11 à 06:29] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822
Page 25-26
Cak Ameera ta tsaya ganin Mami kwance Dr Ibrah na ƙoƙarin saka mata ƙarin ruwa a hannu,bungulin hijabin da ta sanya ya fi komi baiwa Ameera mamaki “yaushe Mami ta fara saka hijab?wai ma miye ya ƙara kawo wannan mutumen…”Daddy ne ya katse mata tunani da cewa “Ameera ja daga bakin ƙofa mana kin tare hanya”cikin ɗakin ta ida shigewa yayinda Twins suka danno kai sannan Daddy.
Kawar da kai gefe yayi kai kace bai gan su a falon ba haka ya wuce part ɗin shi,wanka yayi ya shafa da turare mai ƙamshi sannan ya saka kayan shan iska.
Ko da ya dawo falo Dr Ibrah ya bar gidan “ashe accident aka yi?”cewar Mami ta na ɓata fuska ita ila doli fushi ta ke har yanzu bai tankata ba sai wayar shi da ya ke latsawa ya na karanta text murmurshi kan fuskar shi nayi kewar ka ji na ke kamar nayi tsuntsuwa na dawo
???? Daddyna shine ko ka kula ni babu kira babu saƙo sai kace wacce aka yi kyauta da ita
???? dan Allah kayi min magana da zarar ka kunna waya sannan ka faɗa min dalilin ƙin kula ni har da kashe waya
????
Duk text ɗin Mimi ne wasu bai ma samu damar karanta su ba ya danna mata kira,a Shagwaɓe ta ɗaga gami da sallama wata sanyayar ajiyar zuciya Daddy ya sauke jin muryar ta.A zahirin gaskiya tabbas shi ma yayi kewar ta sosai bai taɓa wuni ɗaya bai ji motsinta ba wannan ne karon farko,”Daddyna nayi kewar ka”na faɗa kamar zan yi kuka lumshe ido yayi yace “Mimi da fatan kun sauka lafiya?”da sauri nace “a’a Daddy ni dai tun zuwan mu ban ci komi ba tea ne kawai ni ke sha sai wata ƴar busassar kaza da na ci yanzu”murmurshi mai sauti Daddy yayi wanda har sai da naji shi “kai Mimi kazar ce busassa?to tayi daɗi kuwa?”dariya nayi nace “to ɗan kaɗan dai,wai miyasa ka ƙi nema na koko har ka fara mancewa da ni ?”Daddy yace “wayar ce ta ɓata sai yanzu wanda ya tsinceta ya kawo min”ajiyar zuciya na sauke nace “alhamdullah dama Hajiya Babba tace lafiyar ka lau in bar damuwa da ke ai ba ƙaramin yaro ba n…”dundun da Hajiya Babba ta kai min ne yasa nace “Washhh Daddy???? Allah wannan tsohuwar so ta ke ta karya maka ni,wani irin duka ta yi min kamar ta bugan guduma”
Daddy bai ce komi ba sai ji yayi Hajiya Babba na magana “ni dai ka turon kuɗin mota na koma wannan sangartatar ƴar ta ka ta hana ni shaƙat sai shegen son jiki ba ta moruwa ga ƴar karen sakuwa sai kace autar mata”dariya Daddy yayi yace “ina kwana Hajiya ?”
“Au !ni ke kiɗina ni ke rawata ko?yanzu ina faɗa maka laifin ƴar ka shine kake wani gaishe ni?”ƙeya Daddy ya ɗan sosa yace “afuwan Hajiyar mu kin san halin Mimi sarai ba ta son wahala ne,kuma please kar a cutar min da ita zan turo kuɗi sai a nema maku ƴar aiki” “da dai ya fi”cewar Hajiya Babba ta na mai miƙo min wayar.
“Daddy ina Mami na?”shiru yayi ya kalli gefen da Mami ta ke kwance ta na barci tuni kuma sérum ɗin ya ƙare,tashi yayi ya cire mata haɗi da gyara mata hijab ɗin ta fuskarta ya ɗan tsurawa ido.
Allah ya sani irin son da ya ke yi mata kawai ƴar canzawarta ne bai kwanta mashi a rai ba ga kuma zarginta da ya fara “hello”na faɗa ɗan ƙarfi,lumshe ido yayi yace “umhum!”na turo baki cikin shagwaɓa nace “Daddy shine ka ƙyale ni ?ina Mami?” “Ta na barci”ya bank amsa a takaice,shiru nayi ina tunani dan wannan ba ɗabi’ar Mami ce ba yawan barci a ko wane lokaci ta na ƙoƙarin faranta ran iyalenta shiyasa ta ƙauracewa duk abinda yayi kama da raggonci.
“Mimina zan kira ki an jima”ya na gama faɗa ya kashe ya na sauke wani irin numfashi saboda canjin yanayi da ya fara ji,Ameera wacce ta yiwa Twins wanka ta canza masu kaya ta fito tare da cewa “Daddy mi za’a dafawa tunda Mami na kwance?””ki dafa shinkafa dafa duka sai ki gasa kifi”da “toh”ta amsa ta nufi kitchen Daddy kuwa fita yayi izuwa farfajiyar gidan.