KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

***Bayan 2week

Fadila ce zaune tsakiyar gado ta na danna waya da alamu shart suke ita da Nasir sai Shagwaɓa ta ke zuba mashi,shi kuwa bawan Allah bai cikin nutsuwar shi saboda yayi nadamar kusantar ta tunda har ya ga sakamakon yin haka gun ƙanwar sa.
A ɓangaren su Iyani kuwa doli ta ɗauki ƙaddara ba tare da tayi yunƙurin zubarwa da Fauziya ciki ba,ita kuwa ba ta so haka ba dan a cewarta abun kunya ne ƴan unguwa su ganta da ciki.
Tsangwama kuwa ta na shanta duk in ta gifta Iyani sai ta harareta tamkar idonta za su faɗo,Nabee kuwa ganin ƴar uwarta tayi cikin shege yasa ta ƙara ɗaukar matan tsaro har da zuwa gun wani malami yayi mata laya ta ɗaura ga ƙugu saboda zuwan ɓacin rana kar atai ta samu namijin da zai yi mata ta ƙarfi,amman wannan layar ba za ta taɓa barin namiji kusantar ta ba muddin ta na ga jikinta.

A tsinake ta ke shiryawa cikin wasu fitananun riga da wando wanda suka ɗame mata jiki,wani bungulin hijab ta saka kafin ta rataya bag.
“Iyani zan tafi school sai na dawo”ta na gama faɗa ba ta jira cewar Iyanin ba ta fice, adaidaita sahu ta tsayar da ya ɗauke ta ba su zame ko ina ba sai ƙaton compagnie.

Cike da yauƙi ta nufi office ɗin ba tare da neman izini ba ta buɗe ƙofar tare da kutsa kai ciki,da sauri Daddy ya miƙe tsaye ya zagayo sai da ya ƙanƙance ido sannan yace “mi ya ƙara maido ki office ɗina ?”murmurshi tayi tare da cire hijab tace “Washhh Allah na gaji masoyi ka ban ruwan sanyi man”ba ta kai ga ida maganar ba ya ɗauke ta da wani gigitacen mari.
Ihu ta buga tare da yin cikin shi za ta rungume shi yayi wani irin taɗe ta sannan yayi ball da ita,wayar rallonge ya ɗauka ya shiga zuba mata Nabee sai kuka ta ke haɗi da ƙoƙarin tashi amman Daddy na mayar da ita ihunta duk ya karaɗe gun.

PA ne ya shigo ya ceceta,da sauri ta saɓi hijabinta da hannu ta ari na kare???? “Suraj ka dubi tantiriyar yarinyar nan wai ta zo har office ɗina neman ra’ayina kwanakin baya ma ta zo na koreta,ban san inda ta samu lambata ba haka ta ke aiko min hotunan ta da mugunyar shiga.Amman da yake ƴar iska ce shine ta sake dawowa”haƙuri PA ya shiga baiwa Daddy ya na mai cewa “uwannan su ne ɓata gari barin su cikin gari ba ƙaramar illa za su yiwa mutane ba”Daddy yace “shiyasa fah na mayar da Mimi Niamey ka san classe ɗin su ɗaya ban san ko miyasa ta ke bibiya ta ba”PA yace “sir wannan da ka ganta ai ka ga KARUWAR GIDA saboda idonta a tsatsaye suke”cike da ɓacin rai Daddy ya rufe office ya nufi hanyar gida.

Tun da ya karyo kwanar ya ke jin zuciyar shi na wani matsiyacin bugawa,da mai gadi ya buɗe mashi get ya shiga yayi parking sai murmurshi mai gadi ya ke wanda Daddy bai san na minene ba.

Wani irin sarawa kan Daddy yayi ya na maimaita kalmar “yi da ƙarfi Dr na yauwa da ƙarfi”numfashin shi ne ya tsaya cak na wuccin gadi kafin ya samu zuciyar shi ta fara halbawa da ƙarfi da ƙarfi.
Zaune yayi a falo dafe da zuciya dan ba zai iya ƙarasawa ciki ba,kar ya tai ya ga abinda zai sa zuciyar shi yin bindiga.Ya na nan zaune ya ke jin sautin su tun suna yi da ƙarfi har suka ƙyale,can kamar minti biyar Dr Ibrah ya saɓo Mami zuwa falo babu kaya a jikinsu.
Wani irin sakin Mami Dr Ibrah yayi ya ta faɗi timmm lokacin da idon shi suka sauka kan Mu’azam babban aminin shi,”my lovely kan ka ɗaya da za ka sak….”ragowar maganar ce ta tsaya a maƙoshi sakamakon haɗa ido da suka da Daddy ya zuba mata idon shi da suka yi jawur tsabar ɓacin rai….
[29/11 à 15:22] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822

Page 27-28

Tsananin furgice,tashin hankali,rashin zaton faruwar haka ya haifarwa da Mami zubar jini tamkar wacce aka buɗewa pampo kafin wani lokaci tuni lumfashinta ya tsaya cak lokacin da tayi ƙoƙarin tashi tsaye ne juwa ta kayar da ita.
Duk tashin hankalin da Daddy ke ciki ganin Mami cikin wannan halin yasa ya mayar da shi gefe ya nufota ya na kiran sunanta da wannan damar Dr Ibrah ya koma ɗaki ya saka kayan shi tare da ficewa daga gidan.

Duk ruwan da Daddy ke malaya mata bai sa ta farfaɗo ba,ɗakinta ya shiga ya ɗauko mata kayan jikinta bayan ya saka mata ya ciciɓeta zuwa asibiti.

An ɗauki lokaci kafin likita ya fito “masha Allah mun yi nasarar daidaita numfashinta sai da kamar wuya cikin jikinta ya tsaya duba da irin shock da attaque ɗin da suka kawo mata farmaki,zuciyarta ma kingin kaɗan ta buga tsabar tsoro”banda ido babu abinda Daddy ya iya sarrafawa su ma likitan ne ya zubawa wasu,sai da zuciyar shi ta dawo daga suman wucen gadi sannan ya fara jujuya maganar likita bisa lizamin hankali a fili yace “ciki?ciki ne da ita?”cikin tausayi Dr yace “kayi haƙuri bawan Allah nima na so ace ya tsaya duba da shekarun da kuka ɗauka ba ku taɓa samun haihuwa ba,nayi mamaki ma sosai yadda ƙwan halittar ka har iya zama a cikin mahaifarta dan kuwa a wancan karon da na auna ku na ga kamar ma impossible ne saboda ƙarfin ƙwayar hallitar ka amman duba da lamarin na Allah ne shiyasa ban yi décourager ɗin ku ba”

Idon Daddy ne suka rikiɗa suka jawur kamar garwashin wuta,shi sam ya ma manta da ya taɓa zuwa wannan asibitin tun shekarun baya da suka wuce to wai mi ma ke faruwa?

Cikin ruɗani yace “Dr wannan shine ciki na wajen huɗu da ta samu amman uwancan duk da ta haife su”ido Dr ya zaro yace “kuma da kai?”kallon ban gane ba Daddy yayi masjid sai yayi saurin cewa “ina nufin kuma kai ne uban cikin na gaske?”

“Daram!dam!dimmm”haka zuciyar Daddy ta buga,yayinda yawun bakin shi suka kafe ƙwaƙwalwar shi ta daina tunani kafin wani lokaci zuciyar shi ta tsaya cak samakon hasaso abinda ya ke fatan ko a mafarki ne ba zai so ace hakan ta faru ba.

Wasu shekarun baya da suka shuɗe…

CEG3 makaranta ce da ke jamhuriyar Niger a garin Maradi,makarantar ta kasance ta ɗaya fannin ƙoƙari da hazaƙa a duk makarantun gwamnati da ke Maradi.
Ɗalibai ne zaune matasa ƴan 4em duk kowanensu sanye ya ke da uniforme,a tsarin classe ɗin 4em mafi akasari matasa ne sabbin balaga saboda a ƙiyasi ƴan 13 zuwa 15years ne.
Gungun students kawai kake gani kowa da abinda ya dame shi,wasu na cin abinci wasu na danna wayar hannu yayinda wasu ke hira.

“Yauwa yanzu abinda za’a yi kowa ya zo ya faɗa mana ra’ayinsa idan ya girma aikin mi zai yi”cewar wani ɗan matashin yaro mai suna Hafiz,nan fah kowa ya shiga faɗin ra’ayinsa haɗi da hujja wasu sun zaɓi koyarwa,wasu aikin soja,masu son kuɗi sun zaɓi aikin ɗan sanda dan karɓar cin hanci.

Hafiz ya dubi Mu’azam yace “ku biyu ya rage ku faɗi ra’ayin ku kai mi kake son zama?”murmurshi Mu’azam yayi yace “ina son na zama ɗan kasuwa nayi kuɗi na gina manyan gidaje,na sayi motoci dayawa ta yadda zan auri mata huɗu tsalatsala masu kyau “dukansu dariya suka yi dan kuwa kusan kowa ya san yadda Mu’azam ke son yin aure tun da ƙananun shekarunsa saboda ya na da yawan sha’awa.
Ibrahim shine kawai bai faɗi ra’ayinsa ba hakan yasa yace “ku tsaya-ku tsaya dariyar ta isa haka nan a bari na faɗi nawa nima”duk ƙyalewa suka yi suka zuba mashi ido.

Sai da ya gyara zama sannan yace “ni kuma likitan mata ni ke son zama,saboda na rinƙa kallon mata yadda ni ke so in yau na ga baƙa gobe fara zan gani daga nan nima sai nayi profiter eh yane”ihu suka kwashe da shi wasu na sake zuzuta shi yayinda Mu’azam ya kai mashi dukan wasa dan sun fi kusa duk a cikin délégation ɗin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button