KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ɗan iska in mutane suka gane ai sai a kore ka”cewar Mu’azam, Ibrahim yayi dariya yace “ai shi Dr Ibrah ya na da ilimi da wayo ba zai yi yadda za’a gano shi ba ƴan ƙauye kawai zan rinƙa eh yane” Mu’azam yace “ku na ji fah wai Dr Ibrah hhh shi har ya ga ya zama likitan hhh”nan aka shiga yiwa Ibrahim dariya ana ce mashi Dr Ibrah ashe wannan abu yayi mashi ciwo sai ya ga kamar da gayya Mu’azam ɗin yasa yin haka collègues sun dare shi.

Cikin fushi ya miƙe ya fice ya bar class ɗin,da sauri Mu’azam ya bi bayansa ya na kiran sunan shi amman ya ƙi ko da juyowa ne balle ya tsaya.Da gudu ya sha gaban shi tunkuɗe shi Ibrahim yayi ya wuce ya bar Mu’azam da mamaki.

Washegari da suka dawo école sai students suke kiran Ibrahim da Dr Ibrah to fah shikenan sunan ya bi shi tun ya na faɗa da jin haushi har ya haƙura amman har yanzu ba su shirya da Mu’azam ba.

A gajiye ya shiga gidan ya na dab da shiga ɗakin shi ya ji muryar Hajiya Babba na cewa “yau kuma lafiya na ga sai ɓata fuska kake kuma ko gaishe ni ba za’a yi ba?”ƙeya ya ɗan sosa yace “a gajiye ni ke wlh ina sauri naje na kwanta ne”cewar Mu’azam Hajiya Babba ba ta ce komi ba sai kayan Munawara da ta ke kwashewa kan igiyar shanya.

Mu’azam na shiga ɗaki ya haye ƴar sofar shi,tunanin canzawar Ibrahim ya ke son yi tare da nemo mafita amman abu ya sauya salo sakamakon ƙugi da marar shi ta ke.
Dafe marar yayi ya furta “ya Allah!”a zuci kuwa cewa ya ke “ƙila wannan shine silar mutuwata ta yaya zan jure wannan muguwar sha’awar a ƴan ƙanƙanan shekaruna?banda kuɗi balle in ce zan yi aure,to wace ce ma za ta aure ni ?”huci ya furzar tare yunƙurawa ya tashi.

Dala biyar ya lalabo a aljihu tare da fita waje ya leƙa ya aiki wani yaro ya sawo mashi ƙanƙara,yaron na miƙo mashi ya buga ƙanƙarar ga bango sannan ya shige ɗaki.
Cikin wani ƙyale ya saka ƙanƙarar ya fara dannawa ga mararsa,a hankali ya ke fitar da numfashin wahala a sannu ciwon ya ke ragewa can barci ya ɗauke shi.

Sai wuraren ƙarfe biyun rana ya farka wandon shi duk ya ɓace da sperm saboda mafarkin da yayi,bokiti ya cika ya je yayi wankan tsarki haɗi da yin na sabulu a ƙarshe ya wanke wandon.

Doguwar riga ya saka ya fito daga banɗaki,alwala ya ɗaura kafin ya wuce masallaci.
Ya na dawowa ya tarar da Munawara zaune a ɗakin shi ta na jiran sa,cikin sangarta tace “ya Mu’az tun ɗazu ni ke jiran ka kazo mu ci abinci”bai ce komi ba ya zauna haɗi da buɗe abincin da ta kawo masu.
Bismillah yayi ya fara ci ita ma sai ta saka hannunta,”Ya Mu’az albishirin ka”ɗagowa yayi kalleta ganin sai murmurshi ta ke zubawa “ya aka yi ne?”sai da ta ɓoye fuskarta tace “dama ɗan gidan Alhaji Abubakar ne yace ya na sona zai aure ni sai mu tafi Makka “shiru yayi ya na kallonta yarinyar duka ba za ta wuce 12year ba amman murna ta ke za ta yi aure.

“Yaushe ya gaya maki haka?kuma kin tabbata dagaske ya ke?”cewar Mu’azam kafin Munawara tayi magana suka jiyo muryar Alhaji Abubakar da sauri Mu’azam ya fita ya na amsa sallamar saboda duk unguwar Alhaji Abubakar ya fi su kuɗi sannan mutumen kirki ne tun rasuwar mahaifin su shi ya ke aiko masu da abinci duk wata.

Cikin girmamawa ya gaishe shi haɗi da yi mashi iso gun Hajiya Babba,har Mu’azam zai fita Alhaji yace “dawo ka zauna yaron kirki “zaunawa Mu’azam yayi.

Nan Alhaji yayi gyaran murya tare da gaya masu abinda ya ke tafe da shi dangane da auren Munawara da yaron wajen shi Kamal ke so, Hajiya Babba tayi murmurshi tace “ai Alhaji duk ƴaƴan ka ne duk yadda kayi daidai ne,ko yau kace za’a ɗaura ni ban ga wata matsala ba tunda da kai da kaya duk mallakar wuya ne”.

Sosai Alhaji yayi godiya ya dubi Mu’azam yace “ya karatun har yanzu ka na nan kan bakar ka na son karantar business ko yaya ?”kai Mu’azam ya ɗaga yace “eh in shaa Allah” “ok babu matsala gobe ka zo ka same ni tun da ba’a makaranta sai mu tattauna ka ga za ka iya farawa tun yanzu ta yadda a gaba ba za ka ji wahalar shi ba”godiya Mu’azam yayi.

***Bayan 1week

Hajiya Babba ta gayyato dangin mahaifin su Mu’azam suka tarbi lefen Munawara,dukan su sun yaba inda kuma a nan take aka ɗaura aure biki kuma sai zuwa gaba.
Ɓangaren Mu’azam kuwa tuni ya fara kasuwanci wanda Alhaji ya ɗora shi a kai,a kullum in ya taso daga school shago ya ke wucewa yayinda kuma weekend ya ke zuwa da safe tuni cikin ƙanƙanan lokaci Mu’azam ya fara canzawa yayinda shagon da Alhaji ya bashi ya ƙara bunƙasa.

Ganin Mu’azam ya sayi babur shine yasa Ibrahim saukowa daga dokin gaba,nan fah suka shirya inda a kullum Mu’azam sai ya je gidan su Ibrahim ɗaukar shi sannan su wuce school.

Tafe ta ke ta na yauƙi irin na ƴan matan zamani sai wani karairaya take ta na juya ƙugu,cak Mu’azam ya tsaya daga tuƙin da ya ke ya ƙura mata ido ta miror har ta kawo daf da su.

“Am ƴan mata sannu”ya samu bakin shi da furtawa,tsayawa Rahama tayi tare da dafe ƙugu tayi wani fari da ido wanda ya sa zuciyar Mu’azam da gangar jikinsa amsawa.

“Ka tsayar da ni malam ina sauri ne”ta faɗa cikin dadaɗar murya wacce Mu’azam yaji duk duniya babu muryar da ta kai ta ta daɗi “dan Allah in ba za ki damu ba ina son ki ban lambar wayar ki”wani kallo tayi mashi irin na tara saura kwabo.

Dr Ibrah yace “please ƴan mata ki taimakawa abokina mana ganin ki kawai ya sa duk ya fita hayyacin shi,in kin ƙi ba shi ƙila ya some min nan”ya ida maganar cikin raha wanda hakan yasa ta yin murmushi haɗi da zayyano mashi numberta.

“Sunan jaruma?”cewar Mu’azam “Rahamatullah”ta bashi amsa…..
[02/12 à 12:29] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822

29-30

Tunda Mu’azam ya gamu da Rahma ya ɗauki son duniya ya ɗora mata,gabaɗaya hankalin shi na kanta komi ya samu Rahma dai tsabar son da ya ke yi mata ya sa duk wani abu da ya shafi harafi mai R ya ke son shi.

Tuni sunanta ya je gun Hajiya Babba babu kunya haka zai zauna yayi ta bata labarin Rahama,Munawara kuwa kullum cikin tsokanar shi ta ke ta kan ce duk ranar da Rahama tace ba ta son shi daga ranar gidan mahaukata za su kai shi.

Ɓangaren Rahama kuwa ba wani sosai ta ke son Mu’azam ba dan ita tafi son namiji kalar fatar ta wato fari,sai irin yadda ya ke yi mata hidima yasa ta bashi wani gurbi a zuciyar ta .

Cikin masifa Ishalle ta ɗaga labulen ɗakin tace “ke Rahamu uwar mi kike yi da har yanzu ba ki fito ba?ko ba ki ji tun ɗazu aka aiko Mu’azu na waje ya na kiran ki ba?”

“Kimtsawa ne ni ke yi tashina daga barci kenan,amman tsabar jaraba har ya ƙumo sammako ya zo mtsw”ta ja tsaki “to zauna nan dan ubanki garin kallon ruwa kwaɗo yayi maki ƙafa kaf samarin ki akwai tamkar shi?ina ce katifar da ta ke sa ki ranar barci shi ya saya maki ita ko?”Rahama ta turo baki tace “kai anty abun kuma har da gori dan ya saya min katifa?”tsuki Ishalle tayi ta saki labulen direct ƙofar gida ta leƙa ta cewa Mu’azam “Bismillah shigo mana ka tsaya waje kamar wani baƙo”kai Mu’azam ya sosa yace “antyn mu ina kwana?”tace “lafiya lau wuce mana ta na cikin ɗaki”babu muso Mu’azam ya nufi ɗakin Rahama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button