KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ta na ƙoƙarin saka riga ya shigo bakin shi ɗauke da sallama,da sauri Rahama ta wawuri hijab ta saka a birkice ma ya ke.
Murmushi Mu’azam yayi ya na kokowa da numfashin shi saboda rabin breast ɗin ta da ya gani ta sama farar bra ɗin jikin ta.

Cikin masifa tace “Mu’az miye haka sabida Allah in fah ka tarar da ni ciki mugun hali?amman ai ka ma riga ka gani”ta faɗa ta na turo baki haɗi da juya mashi baya.

“Kiyi haƙuri babyna anty tace na shigo ai”ya faɗa cikin kalar tausayi,”shine dan tace ka shigo sai ka biye mata ko?”ta faɗa tare da juyowa ta watsa mashi harara.

Murmushi yayi yace “baby ni kike harare kuma?” Ta bashi amsa da “eh ɗin ai kai ne minene na zowa tun da safe ?”

“Baby sabuwar waya na saya maki shiyasa nace bari na biyo na kawo maki tun jiya na saye ta amman nace bari har na gani in ba ta dawata matsala sai na kawo maki”Mu’azam ya faɗa tare da miƙo mata waya sabuwa dal a kwali.

Har ƙasan zuciyar ta taji daɗin haka sai dai ta ƙi nunawa a fuska sai ma kumbure-kumbure da ta ke yi,cikin rashin jin daɗin sauyin na ta yace “dan Allah baby kiyi haƙuri Allah ba zan sake ba,karɓi ki duba ki gani Allah sa za ta burge ki”ya ida maganar da ɗan murmurshi.

Karɓa tayi ta fiddo ta,tecno ce Spark 5,tsabar daɗi ba ta san lokacin da murmurshi ya suɓuce mata ba.
Mu’azam kuwa bawan Allah wata irin ajiyar zuciya ya sauke ganin murmurshi kan fuskar Rahama.

Tsayawa tayi ta na kallon shi “mi kake ma murmurshi?”amsa ya bata “saboda ganin ki cikin walwala”wani tausayin shi ne ta ji yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da ɗan ƙarfi “tabbas Mu’azam shine masoyin gaskiya”ta faɗa a zuci idonta na cika da ƙwalla.

“Ina son ka Mu’az”ta faɗa hawaye na zubowa a kumcinta,wani girrrr ya ji haɗi da yarrr a take kuma tsikar jikinsa ta miƙe yau ne karon farko da ta taɓa faɗa mashi kalmar so.

Shi ma bai san lokacin da hawayen suka zubo mashi ba,ya duƙa yayi sujada shukur ita kuwa dariyar shi ta shiga yi ganin yadda ya ke ta yiwa Allah godiya da ya gwada mashi wannan rana.

Ishalle da ke bakin ƙofa laɓe duk ta na jin komi ta murmursa ta na mai barin gun,sallama Mu’azam yayi mata ya wuce shago.

Ya na zuwa ya tarar da Dr Ibrah zaune shi da wani yaron da suke gudanar da sana’ar tare “sai yanzu ka tawo?”cewar Ibrah ya na mai kallon Mu’azam wanda ke tangale babur.

“Eh wlh ka ga na daɗe ko?gidan su baby na biya ya ne da fatan ka tashi lafiya?”cewar Mu’azam ya na mai baiwa Ibrah hannu wanda yayi kicin-kicin da fuska jin ya ambaci sunan Rahama.

“Lafiya kake wani cin magani?”Mu’azam ya tambaye shi “ban sani ba,kai shikenan wannan yarinyar ta maida ka ɗan ƙaramin mahaukaci komi Rahama sai kace wata autar mata mtws ni ban ga ma abinda ka gani a jikin ta ba da har kake rawar jiki a kanta”Ibrah ke magana cikin tsantsar fushi da kishi.

“To ni dai ina son ta a haka kai ma ya kamata ka so duk abinda ni ke so”Mu’azam ya faɗa cikin rashin jin daɗin abinda abokin nashi ya faɗa a kan Rahama.

Baki Ibrah ya taɓe yace “can ku ƙarata kai da kaji za ka iya,ni tsohuwar wayar ka na zo karɓa tun da jiya ka sayi sabuwa” sosai ƙeya Mu’azam yayi yace “ai Rahama na saya ma ita shiyasa ma ka ga na daɗe ban zo shago ba can na tafi na kai mata”waro ido Ibrah yayi yace “la’ilah illallah wayar 95.000f ɗin ce ka baiwa wata ƙatuwar banza Mu’azam kan ka ɗaya kuw…”hannu ya ɗaga mashi yace “Ibrah ya isa haka kar ka ƙara cewa Rahama ƙatuwa saboda duk fafutuka da neman ni ke yi domin ita ni ke yin su dan haka zan iya mallakawa Rahama duk abinda na mallaka”cike da fushi Ibrah ya bar gun.

Wunin ranar haka Mu’azam yayi shi a jagule dan sosai ya ke son abokinsa amman ko kaɗan bai kamo ƙafar Rahama ba, murmurshi yayi tuna manyan breast ɗin ta yammm haka jikinsa yayi tare da jin son yin aure ya taso mashi.

Sai marice ya koma gida inda ya tarar ana ta shirye-shiryen bikin Munawara wanda ya rage kwana biyu kacal,ɗakin shi ya buɗe ya aje kayan da ya shigo sannan ya shiga banɗaki yayi wanka.
A tsanake ya ke shirinsa inda ya saka wasu fararen kaya uwanda suka yi masifar karɓar sa,in ka ga Mu’azam za ka ɗauka ya kai 25years.
Turare ya saka ya buɗe ledar da ya shigo ita ya fitar da na shi sannan ya ƙulle,ya na ƙoƙarin fita yaji muryar Hajiya Babba “ina zuwa kuma yanzu daga shigowar ka,?”waigowa yayi ya gaishe ta sannan yace “zan kaiwa Rahama kayan shigar biki ne”Hajiya Babba ba tace komi ba.

***GIDAN ALHAJI

“Alhaji aure-auren nan ya isa haka,yawan auren nan ba shi zai sa ka samu abinda Allah bai nufa za ka samu ba”wata ƴar datijuwa ke faɗar haka yayinda shi kuma Alhajin da ta ke yiwa magana ya rabka uban tagumi.
Can ya ɗago ya dube ta yace “ki bar wannan zancen dan tuni an ɗaura yanzu haka yau bayan sallah isha’i amarya za ta shigo”ya na gama faɗar haka ya miƙe tsaye ya fito babban falo yayinda Hajiya ke take masa baya.

Samari ne a ƙalla sun kai ashirin da wani abu,duk rusunawa su ka yi su na gaishe da mahaifinsu bai amsa ba sai da ya zauna kan wata farar kujera wacce ta banbanta da ta cikin falon sannan yace “lafiya lau na ke,na sa an tara ku ne a nan dan na shaida maku yau za’a kawo sabuwar tantin ku ina son ku buɗe kunnuwan ku da kyau duk wanda yayi mata rashin kunya akan auren uwar sa”duk sunne kai suka yi Ma’aruf wanda shine babban su kuma ba zai wuce 34years ba yace “auren kuma again?ina roƙon Allah ya sa alkhairi ya sa kuma wannan shine na ƙarshe ya cika ma burin ka”murmurshi kan fuskar Alhaji yace “amen ɗan arziki”Hajiya kuwa ji tayi kamar taje ta maƙure Ɗan na ta dan kuwa kaf cikin yaran shi kawai ke son abinda Alhaji ke so.

Dare na yi kuwa ƴan kan amarya suka zo tun daga Agadez suka kawota,yarinya ce sharaf ƴar duma-duma mai jini a jiki kallo ɗaya za ka yi mata ka san taji Addini duba da yanayin shigarta ba irin yadda amaren zamani suke caɓa kwalliya ba,a goshinta kuma ƙaton tabo ne baƙi ƙirin na sallah.

Alhaji cike da zumuɗi ya gabatar da duk abinda Shari’a ta gindiya tambayoyin da yayi mata na hukunce-hukuncen sallah da sauran su ras ta bashi amsar su.
A slow ya dinga binta har ya mayar da ita cikakkar mace,azaba kam ta sha ta, Alhaji da kan shi ya gasa ta ita kuma sai noƙewa ta ke yi….

**

Cike da murna Rahama ke buɗa kayan da Mu’azam ya kawo mata har kala uku,farar shadda ta shigar safe, lèche na shigar rana sai lafaya ta kan amarya.
Ishalle sai yaba kayan ta ke can tace “ya kamata azo kuma ayi bikin ku kafin ƴan baƙin ciki su kutso kai,kawai ki ce mashi ya turo magabatan shi”dariya Rahama tayi tace “toh ai sai gobe ne zai gabatar da Ni ga danginsa sannan kuma ai sai mun tafi ƙauye ya gaido su Inna”(Ishalle ba ta haihuwa shiyasa ta ɗauko ƙanwarta Rahama daga ƙauye wajen iyayenta,kishiyarta ɗaya sai dai ba gida guda suke ba wannan kenan)

Ranar biki Rahama ta tsantsara ado suka tafi ita da Ishalle,sosai kuwa suka samu tarba mai kyau gun Hajiya Babba sai nan-nan ta ke yi da su.
Dangin Abban su ma sosai suka yaba da Rahama ita kuwa sai sunne kai ta ke,Gift ɗin da ta kawowa Munawara sai kowa yayi san Barka dan kuwa sai da ta danne zuciyar ta tayi mata sayayya irin ta amare.

Da dadare a ka kai amarya gidan surukanta wanda ya ke nan cikin unguwa,Mu’azam kuwa sosai ya ke murna dan kawu Tanimi yace in shaa Allah shi ma in ya shirya za su je nema masa auren Rahama…..
[03/12 à 09:18] Cham~rose????: KARUWAR GIDA

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button