KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822

Après chaque prière

(1)أَسْتَغْفِرُ اللَّهَ(2)اللَّهُمَّ أَنْتَ السَّلاَمُ، وَمِنْكَ السَّلَامُ، تَبَارَكْتَ يَا ذَا الْجَلَالِ وَالإِكْرَامِ

Je demande pardon à Allah [trois fois]. Ô Seigneur ! Tu es la Paix et la paix vient de Toi. Béni sois-Tu, ô Digne de glorification et de munificence. »

Muslim 1/414.

JUMMA’A MUBARAK MES FANS????

PAGE 31-32

Cikin ikon Allah an kai lefe gidan su Rahamatullah bayan Mu’azam ya je har ƙauyen su ya gaishe da iyayen ta.
Ba wani saka dogon lokaci ba wata biyu ne kacal,tuni Mu’azam ya fara shirye-shirye ɗakin Hajiya Babba aka gyara wanda ya ke cikin da falo ita kuma ta koma ɗakin shi mai ciki ɗaya.

Abotar su Mu’azam kuwa ta ɗan rage ƙarfi shi da Ibrah duk da sun shirya amman tuni ya gane da Ibrah ya na hassadar shi ne da ƙyashin abun hannun shi.
Munawara babu yadda ba ta yi da Kamal su tsaya har ayi bikin Mu’azam ba amman ya ƙiya a ƙarshe da ya ga za ta kawo mashi cikas yayi mata gami da Hajiya Babba ita kuwa ta shiga yi mata faɗa a ƙarshe ta ɗirka mata ɗan karan duka da ciwon jiki da birdin tsamanga Munawara ta isa Saudiyya tare da ƙudirin ita da zuwa Niger sai kuwa in gawarta za’a kawo tunda ba ƙaunarta Hajiya Babba ke yi ba????

***Bayan wata biyu

Tuni su Rahama an zama amare,zalama gun Mu’azam kuwa ba’a magana ɗaya rana sai ya nemeta fiye da biyar tun ta na kuka har ta saba sai ya zamana har ta fi mai kora shafawa dan wani sa’in ya na shago za ta kiran shi ta aza mashi kuka sai ya dawo gida ya yi mata abun????

Cikin zumɓurar baki Rahama ta shiga tuƙa tuwon ta na gunguni tare da zagin Hajiya Babba ƙasa-ƙasa ita da ta sa a yi tuwon laushi,cikin yanayin rashin jin daɗin rashin kunyar da Rahama ta tsiro Hajiya Babba ta dube ta tace “Rahamu yanzu haka ake tuƙa tuwo garin ku?duk kin bi kin ɓata madafa da gari kuma tuwon ki na ganin ya na ƙulalai shine kike zuba gari dayawa?to bani in yi kaya na tun farko sai da nace ku yi girkin ku in yi nawa”

Miƙewa Rahama tayi ta baiwa Hajiya Babba wuri,bakin pampo taje ta wanke hannunta ta shige ɗaki zaunawa tayi ta kalli baƙuwarta wato ƙawarta Rahama mai irin sunanta tace “wlh na gaji waccan baƙar tsohuwar ta sa ni yi mata ƙaddararen tuwo kiji fah da rana tsaka a saka ni girgizar jiki”
“Innalillahi yanzu takwara uwar mijin ta ki ce tsohuwar banza?”to kiyi saurin tuba ga Allah domin duk wacce ta haifa maka miji ta gama maka komi a duniya “wani uban tsuki ta ja tace “dallah kar ki kawo min ƙabli da ba’adi ke a ko ina sai kin nuna ke ustaziya ce tai can ki zauna ke uwar mijin na ki tayi ta juya ki,shi kuma mijin ki riƙa goya shi iyakar biyayya wai na ga kwanaki har wani duƙawa kike dan za ki miƙa mashi makuli mota kawai salon ya raina ki”

Ita dai ba ta ce komi ba dan ta riga da ta san namsake ɗinta babu abinda ta saka a gaba sai duniya,sallama tayi mata ta yi tafiyarta.

Dare nayi Mu’azam ya dawo,kunkume fuska Rahama tayi shi kuwa bawan Allah duk ya susuce ya shiga tambayarta lafiya buɗar bakinta sai cewa tayi “ai Hajiyar ka ce ta zage ni wai ƴar ƙauye ban iya girki ba,kuma fah ina tsaka da girki ta karɓe wai ai Ɗanta ya yo cefanen shiyasa ma ban yi girkin dare ba kuma ni yanzu yunwa ni ke ji”

Shiru Mu’azam yayi ya na ta juya zancen can dai yace “ina zuwa”ya faɗa tare da fita ya ja babur.
Gasasun kaji da frite ya sawo,sai da ya kaiwa Hajiya Babba na ta sannan ya wuce part ɗin su.
Cike da murna Rahama ta fara cin kajin a zuci kuma ta na kitsa yadda za’a yi ta haɗa tugun da zai sa su bar gidan.

***2years later

Arzikin Mu’azam ya buƙansa sosai dan har yayi na shi jarin yanzu kan ƙafafun shi ya ke tsaye daram,matsalar shi ɗaya ita ce rigimar Rahama kullum da sabuwar fitinar da ta ke kawo mashi yanzu ita kuma Hajiya Babba ta matsa doli sai ya ƙara aure saboda har yanzu Rahama ko ɓatan wata ba tayi ba.

Ɓangaren karatu kuma BEPC kawai Mu’azam ya ke da daga nan kuma ya tattara su ya maida gefe,yayinda Ibrah tuni ya fara karantar karatun likitanci yanzu haka ya na cikin shekara ta biyu.

Kuka Rahama ke yi wiwi kamar ranta zai fita jin wai kishiya za a yi mata,cikin ɗaukar shawarar da takwararta ta bata ta dubi Mu’azam tace “kafin kayi auren sai ka shirya mu fara zuwa asibiti tukunna a san daga ina ne matsalar ta ke”bai wani damu ba ya amince.

Da zuwan su aka gwada su likita ya tabbatar da duka lafiyar su lau matsala ɗaya ce shine kamar ƙwan haihuwar Mu’azam ya fi ƙarfin ƙwan hallitar Rahama maimakon in sun gamu suyi fécondé sai ya ƙona shi.Cikin dubaru na likitoci ya shiga kwantar masu da hankali sannan yace su dage da addu’a duk da su na da 1% na chance amman lamarin Allah sai shi.

Wannan batu sam bai kwantawa Hajiya Babba ba hakan yasa ta fara neman masu maganin gargajiya a ƙarshe dai sai ta gayyato wani malami kwanan shi bakwai a gidan su ya na aikin shi.
Jungum suka yi suna sauraren malam wanda ya ke ta yin murmushi can yace “tabbas akwai arzikin ƴaƴa amman da alamu duk mata sannan hakan za ta faru ne in kun dage da roƙon Allah ku yawaita yin saraka sannan mabuɗin arzikin ku shine ɗaukar Maraya ku ingata rayuwar shi”

“Maraya?ina za mu samu Maraya kuma malam?”cewar Mu’azam “gidan marayu za ku je ku yi adopter ɗin sabuwar haihuwa saboda ita ɗin haske ce tamkar tauraruwa yayin ɗaukar ta za ta canyara kuka ne tamkar lokacin ne aka fiddota daga cikin cikin mahaifiyar ta”malam ya faɗa ya na murmurshi “malam kuma doli sai mace?”Mu’azam ya faɗa dan ya fara ganin abun kamar an kaucewa hanya.

Tsawa Hajiya Babba ta daka mashi tace “ka fi shi sanin aikin shi ne?” Malam yace “istakhara nayi in kuma ka na so kai ma za ka iya yi,tabbas a mafarkina mace na gani haske ya luluɓeta”

Da sauri Mu’azam yace “malam bani karatun istahara ɗin”

Malam yace to ga addu’ar kamar haka:
اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْتَخِيـرُكَ بِعِلْمَكَ، وَأسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ الْعَظِيمِ، فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلَا أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلَا أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الْغُيُوبِ، اللَّهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الَأمْرَ (وَيُسَمِّي حَاجَتَه) خَيْرٌ
لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِي وَيَسِّرْهُ لِي ثُمَّ بَارِكْ لِي فِيهِ، وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأَمْرَ شَرٌّ لِي فِي دِينِي وَمَعَاشِي وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاصْرِفْهُ عَنِّي وَاصْرِفْنِي عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ ثُمَّ أَرْضِنِي بِهِ

Godiya Mu’azam yayi sannan Hajiya Babba ta sallami malam.
Dare na yi Mu’azam yayi raka’a biyu sannan ya karanto addu’a da malam ya bashi yayi tawasli da Allah tare da miƙa dukan yarda shi.

***GIDAN ALHAJI

Dr Ma’aruf ne sanye da kayan likitoci,idon shi manne da farin glass hankali tashe ya shigo gidan.
Kallon Abban nasa yayi yace “Abba doli sai an tafi asibiti ka yarda da ni dan Allah wlh ba za’a samu matsalar komi ba”cikin yarda da Ɗan na shi ya tallabo Agaishat wacce ta jigata saboda zafin naƙuda mota ya sakata tare da ɗaukar kayan haihuwa suka wuce asibiti.

Allurar naƙuda Dr Ma’aruf yayi mata sai addu’a ya ke yi Allah sa matan biyu su haifu lokaci ɗaya,waccan ɗayar ta fara nishi da sauri ya tafi ya karɓi haihuwar ta cikin ikon Allah ko minti biyu ba’a yi Agaishat ma ta haihu.
Bisa gado ya ɗora jariran wanda suka kasance duk mata ne,sai da ya rumtse ido sosai sannan yayi masaye wato ya canza su ya baiwa Agaishat ƴar wacan matar ita kuma ya bata ta Agaishat.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button