KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL
Cike da murna Alhaji ya ɗauki baby girl ɗin ya na mata huɗuba,tuni kuwa alhalin shi suka cika asibitin amman ƙememe ya hana kowa ya taɓa yarinyar.
A hankali Dr Ma’aruf ke shafa kan ƴar ƙanwar ta sa lokacin da Marâtre uwar marayun ta karɓe ta daga hannun shi “a kula da ita sosai ita ɗin marainiya ce mahaifiyata ta mutu wajen haihuwar ta sannan dama ta ce ko ta haife ta jefar da ita za tayi saboda ba ta hanyar aure aka haife ta ba”Dr Ma’aruf ke faɗar haka kafin ya tafi ya na jin son yarinyar cikin ɓargon zuciyar shi.
Cike da murna Rahama ta shirya saboda mafarkin da Mu’azam yace yayi,cikin ƴar ƙaramar motar shi suka shiga su dukan su har da Hajiya Babba ba su zarce ko ina ba sai gidan marayu.
Babu ɓata lokaci shugan gidan marayun ya kai su ɗakin da ake aje sabin haihuwa,marâtre ita ta rinƙa ɗauko jariran ta na miƙawa Mu’azam da ɗaya-ɗaya duk in an bashi sai ya aje.
“Inyaaa !inyaaa”haka jaririyar ke cancara kuka murmurshi dukansu ukun suka yi Mu’azam yace “alhamdullah na ɗauki wannan”marâtre tayi murmurshi tace “Allah sarki ko minti goma ba’a yi ba da wani likita ya kawo mana ita mahaifiyar yarinya rasuwa tayi”nan da suka cika takardu komi da komi Mu’azam yayi mata huɗuba ya juyo ya kalli Hajiya Babba yace “wane suna za’a saka mata?” “Fadimatu”ta bashi amsa ta na murmurshi shi ma murmurshin yayi yace “takwara kika yiwa kan ki kenan?to ni kuma zan rinƙa kiranta da Mimi“…..
JUMMA'A RANAR HUTUNA CE BAN POSTING
[04/12 à 14:10] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822
Page 33-34
Kiran Dr Ma’aruf marâtre tayi kamar yadda ya buƙata cewa duk ranar da aka samu wanda zai ɗaukar jaririyar ayi mashi magana.
Babu ɓata lokaci kuwa ya zo adresse ɗin Mu’azam ya karɓa sannan ya bi su har gidan su ya ga muhallin su kafin ya koma.
Wanka Hajiya Babba ta yiwa takwarar ta na ruwan zafi sai kuka ta ke canyarawa,mai ta shafa mata ta saka mata kaya masu kyau cikin wanda Mu’azam ya sawo mata.
Karɓar ta Rahama tayi ta shiga bata madara cikin biberon ai kuwa ta fara sha, Mu’azam ya shigo cike da murna yace “Hajiya Babba albishirin ki?”tace “goro”takardun gida ya ajiye a gabanta sannan ya zauna bisa tabarmar ya tanƙwashe ƙafafun shi yace “Dr nan ne ya bani kyautar gida mai kyau ɗan madaidaici sannan kuma har da kaya ya zuba cikin su,babban abun farin ciki da ya tambaye ni nayi karatu ko yaya ne nace mashi eh kawai sai ya bani shuwagabancin compagnie ɗin shi yanzu haka gobe zan fara aiki”wata irin buɗa Hajiya Babba tayi tace “madallah dama malam yace ita ɗin rahama ce gare mu ga shi kuwa tun ba’a yi nisa ba mun fara samun canjin ratuwa,kai masha Allah bari mu tashi mu fara shirin komawa can in ya so nan ɗin sai mu saka ƴan haya”ta na gama faɗar haka ta miƙe tare da shigewa ɗaki ta fara haɗa kayanta????
Mu’azam ya kalli Rahama yace “ya na ga ba kya farin ciki?”murmurshin ƙarfin hali tayi dan ita sam ba ta so Hajiya Babba ta bi su can sabon gida????
Kwanci ta gyarawa Mimi sannan tace “ai abun murna ne sosai ga Ɗiyar nan sai kace kai ka haifeta dan har kama kuke yi”hannu ya sa ya ɗauki Mimi yace “kai haba bari na gani”Rahama tace “Allah kuwa kawai dai dan ta fi ka hasken fata ne”murmurshi yayi yace “farin mahaifiyarta ne tayi,kin ga an raba biyu ni na ɗau kama ke kuma kin ɗau farin fata”
Ranar nan su Mu’azam ba su kwana a ko ina ba sai a sabon gidan da Dr Ma’aruf ya basu wanda ke ADS can wajen masallacin jingile,Hajiya Babba sai zaga gida ta ke ta na kwararawa Dr Ma’aruf albarka.
***GIDAN ALHAJI
Cike da murnar yau Allah ya azurta shi da samun ƙaruwa ta Ƴa mace ya haɗa ƴar ƙaramar walima iya ahalin shi,zuwa yanzu duk yaran shi murna suke su ma sun samu little sis dama can su yawan aure-auren ne ba sa so.
Duk wanda ka gani fuskar shi a sake ta ke ya mai nuni da farin ciki amman banda Ma’aruf da ya koma gefe ya na tunanin ya rayuwar ƙanwarsa za ta kasance duk da dai ya fara ingantata ta hanyar canza masu muhalli mai kyau.
Alhaji ya ɗauki baby girl ɗin sannan yayi gyaran murya yace “alhamdullah gida yayi ƙamshi,ya haskaka,ya girmama da zuwan Raihan”duk taɓi ɗiyan shi suka shiga yi Agaishat ta ɗan murmusa yayinda sauran matan Alhajin suka cicije.
Hidimar da ake ta shagaltar da mutane hakan yasa Hajiya ta zuba wani garin magani farin fal a cikin biberon ???? ɗin da ake baiwa Raihan ruwan zam-zam.
Cikin rashin sani kuma Agaishat ta ɗauka ta baiwa Raihan ruwan,ashe duk abinda ke faruwa a kan idon Ma’aruf
Mimi na cika kwana bakwai aka yanka mata ragon sunanta Fadimatu, gagarumin biki aka yi dan kuwa kusan dama Mu’azam mutumen jama’a ne.
Soyayya ƙauna suka haɗe gu ɗaya suka yiwa zuciyar Mu’azam ƙawanya sosai ya ke son Mimi fiye da komi na shi,a haka har Mimi ta fara girma ta fara ce mashi Daddy Rahama kuma Mami.
Mimi na cikin shekara ta biyu Allah ya yiwa Daddy wani irin buɗi na arziki,nan fah Mami ta aza masifa a doli suka tashi suka koma sabon gidan da ya gina yayinda Hajiya Babba kuma ta zauna wancan.
***Bayan 4years
Daddy ne da Mami zaune gaban Dr Ibrah wanda yanzu ya zama cikaken likita,bayani dai ya sake yi masu kan dukan su lafiyar su lau kawai su jira lokaci.
Su na shirin miƙewa yace “am tsaya na ɗibi jinin ku sai na kaiwa wani abokina mu ga shi mai result ɗin shi za ta bada”babu muso kuwa suka tsaya ya ɗiba sannan suka dawo gida.
Washegari tun da safe Daddy zai tafi aiki ya ja hannun Mimi suka fita tare ya biya ya aje ta gidan Hajiya Babba.
Fitar Daddy babu wuya Dr Ibrah ya shigo gidan,sai da ya shigo falon ya ƙwala sallame.Mami ta fito daga ita sai kayan barci jigida nayi mata kacau-kacau cak ta tsaya ganin ashe ba Daddy ba ne,har za ta juya sai taji muryar Dr Ibrah “masha Allah a nan Allah yayi babba ƙaddara wacce ba ta dace da baƙar fata ba”da sauri ta juyo ta na kallon shi .
Gira ya ɗaga ya ajiye takardun hannun shi ya fara takawa zuwa gare ta,wuyanta ya sunsuna yace “Hummm komi ma na Gimbiya haɗaɗe ne”lumshe ido Mami tayi ta na jin tsikar jikinta na tashi.
Wuyanta Dr Ibrah ya fara yiwa kissing kafin ya koma ga lips ɗin ta,cikin ƙanƙanan lokaci ya birkita mata lissafi.Ɗaukarta yayi cak ya nufi ɗaki da ita,abinda Mami ba ta taɓa tunani ba shine ya faru wai ita ce tayi zina da wayon ta.
Kuka ta shiga yi sosai Dr Ibrah na bata haƙuri,ganin ta ƙi barin kukan yasa ya kimtsa ya bar mata gidan kafin a rutsa shi.
Da marice Daddy ya shigo gidan amman sai yaji shi tsit, ɓangaren Mami ya nufa yaji ƙofar a ƙage fitowa yayi ya nufi kitchen dan ya ga babu komi a dining nan ma wayam .
Falo ya dawo ya zauna idon shi ya sauka da farar takarda,ya ɗauka ya karanta sai ya miƙe murmurshi kan fuskar shi ya nufi ɗakin shi wanka yayi sannan ya kira Dr Ibrah amman har ta gama ringing bai ɗauka ba.
Motsin da ya ji yasa shi waiwayo Mami ce kallonta ya tsaya yi ganin tayi wani irin sanyi”ashe har ka shigo ?barka da zuwa ina Mimi”
“Yauwa!ta na gun Hajiya Babba yau amarci ni ke son mu sha sosai”ya ɗaga mata gira gabanta ne ya faɗi sai ta ke ganin tamkar zai gane ne in ya kusanceta.