KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ina nan zaune Ameera ta fito cikin shirin doguwar riga ta atamfa ta cire uniforme ɗin makaranta,saurin kawar da idona nayi daga kallonta saboda wata irin kunyarta ma na ji……
Comment and share Please
Jikar Rabo ce ????
[17/11 à 07:54] Cham~rose????: KARUWAR GIDA…????????♀️LOVE and ROMANTIC STORY
```MRS SADAUKI```????
☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Whatsapp OR Call 08066268951
PAGE 3-4
Teddyna na kwasa na wuce bedroom,kan bed na zube na rungume sabon da Daddy ya sawo min ɗayan kuma sa ka shi tsakiyar ƙafafuna ban jima ba barci ya ɗauke ni.
A hankali ya fara kusanto da fuskar shi ga tawa wanda hakan ya sa bayi saurin lumshe idona,danshin yawun shi naji tare da saukar lips ɗin shi kan nawa.Ya ranƙwafo yayi min rumfa sai kuma yayi ƙoƙarin miƙewa da sauri na jawo shi hakan yayi sanadiyar ɓallewa batoran rigar shi wacce ta ɓoye sirrin cikar haibar shi, murmurshi na saki ina mai buɗe idona na zuba su ga fafaɗen ƙirjin shi wanda ya ke cike da gargasa.Hannu na kai na ɗora saitin heart ɗin shi wacce ina jiyo sautinta a duk lokacin da mu kayi kusa da juna,ina shirin ɗagowa na kalli fuskar shi kawai yayi saurin miƙewa tare da juya min ya fara takawa ya nufi ƙofar fita.
“Kar ka tafi ka bar ni please mafarkina ka tsaya na kalle ka”jin wani abu mai shegen nauyi ya sa ni firgigit na farka daga ɗan barcin da ya ɗauke ni,ture Ameera nayi wacce ta faɗo jikina ta na dariyar da ban san ta mice ce ba.
Kallona tayi ta na nuna ni tare da cigaba da yi min dariya,shiru nayi ina tunani nan take mafarkin da nayi ya faɗo min a rai wanda kuma babu shakka yau ma ɗin a bayyane nayi ta kiran masoyin mafarkina.
Ban tankata ba na jimƙe Teddyna ina mai jin wata irin kewa wacce ban san ta mice ce ba,kawai dai ina jin nayi missing wani abu mai muhimmanci da rayuwata ta ke buƙata.
Ina nan kwance har aka fara kiran sallah Asar na miƙe na ɗauro alwala na gabatar da sallah,haka ma Ameera ta zo tayi sallah dan gaskiya a gidan mu kowa na yin Sallah kan lokaci hatta da twins da ba za su wuce 8 years ba.
Da dare bayan duk mun gama dîner na wuce ɗakina,sai da nayi wanka sannan na saka spleeping dress uwanda suke dogaye ne masu rufe jiki saboda ɗan sanyin da aka fara.
Har na jawo Teddy zan kwanta na ga saƙon Daddy ya na kira na a ɗakin shi,miƙewa nayi wayata a hannu na nufi part ɗin shi.
Sallama nayi bayan an bani izini na shiga,a zaune ya ke kan sallaya alamun idar da sallar shi kenan ya na jan tazbaha.
Har ƙasa na durƙusa cikin sanyin muryata nace “Daddy ga ni”ɗagowa yayi ya ƙare min kallo tun daga yalwatacen gashin kaina wanda ya zubo kan kafaɗata har zuwa farcen ƙafata,wata leda ya miƙo min na karɓa ina jiran yayi bayani sai naji ya ƙyale hakan ya sa na ɗago dan ganin ko lafiya da sauri na mayar ganin ashe ni ɗin ya ke kallo.
Sai da yayi gyaran murya sannan yace “Mimi ga kaya nan na sawo maki,ki bar zama haka nan kin ji ko?”kai na jinjina ba tare da na buɗe ledar ba na gani “tashi kije ki tabbtar kin sha maganin ki”miƙewa nayi nace “toh Daddy mu kwana lafiya”.
Ina zuwa ɗaki na zazzage kayan, breziya ce wajen kala biyar sai wasu ƴan riguna ƙanana masu kamar bra ɗin sai dai su ba suda soso hasalima kamar dai riga suke.Cike da murna na ɗauki ɗaya na saka sai na ga tayi min tsaf kwanciyata ,ina jin Ameera na yaba bra ɗin kasancewar lokacin da na shigo ta na toilet.
Washegari tun da safe na shirya cikin uniforme ɗin makaranta dan yau mu na da lectur da na fi so wato English,a falo na fito inda na tarar tuni kowa ya na cikin shirin sa na tafiya school.
Gaishe da Daddy da Mami nayi na ja kujera na zauna,tea ɗin da Mami ta haɗa min tun tuni na ɗauka na fara sha,”Mimi in kin tafi school please ki kula da kan ki banda shiga wajen mai ƙura sannan ki guji duk abinda zai saka ki yawan dariya”cewar Daddy ya na mai aje spon ya na kallona, jinjina kai nayi nace “to Daddy in shaa Allah can ma kuskure ne”na faɗa ina ɗan ɓata fuska saboda ni kaɗai na san irin uwar wuyar da na sha da ciwona na asama ta tashi sanadin dariyar da su Nabee suka sa nayi,a ƙarshe sai kawo ni suka yi gida cikin mawuyacin hali.
Daddy na gamawa ya miƙe yace “in kun gama ku same ni a mota”da “toh”duk mu ka amsa yayinda Mami ta miƙe dan yiwa mijinta rakiya wanda ku san kullum sai ta kai shi har mota ta na yi mashi addu’a wanda hakan ba ƙaramar ɗaga tutar ta yayi kama daga mu ƴaƴanta har izuwa Daddy.
Abincin su Twins na ɗauka ko wace na saka mata a bag ɗin ta sannan na goya masu,kallon Ameera nayi wacce ke ta cin abinci kamar wata shanuwa nace “Malama ke mu ke jira”ta turo baki tace “ba ki ga abinci ni ke ci ba? “gaba nayi Twins na bi na a baya amman sai nayi saurin juyowa ina kallon su zuciyata na bugawa da ƙarfi,sam na tsani halin Mami na rashin kunya ba ta san inda za tayi abu ba ita babu ruwanta yanzu a tsakar gida ta wani shishigewa Daddy ta na sumbata da shafar shi ba ta tunanin akwai ƴan aiki in tace mu ƴaƴanta ne mai gadi fah da mai baiwa fulawa ruwa?ko da wasu su kan ce ki zama KARUWAR GIDA a gaban mijin ki ai ana sirrintawa.
Muryar Daddy naji ya na cewa “ina ita Ameerai?”ban juyo ba sai na ida gyarawa su Twins hijab ɗin su sannan na juyo na kalle su yanzu Daddy ƙoƙarin shiga mota ya ke yayinda Mami ta koma gefe ta ƙura mashi ido,ƙarasawa mu ka yi har yanzu zuciyata na bugawa.
Gidan baya na buɗe mu ka shiga kamar kullum,zuwa can Ameera ta fito ta shige gaba seat ɗin mai zaman banza.
Mami ta ɗaga mana hannu alamun bye bye dan ita ba ta zuwa ko ina,kullum ta na gida duk wata Daddy na yi mata salery.
Ni aka fara ajewa a ISB sannan aka wuce da su,Twins évangélique su ke yayinda Ameera ke Ɗan Koulodo kowa Sarki.
Da gudu Nabee ta tare ni ta na cewa “oyoyo my cakuleti”ture ta nayi ina hararenta nace “ba wani nan tun shekaran jiya da kika kai ni gida ba ki sake waiwayata ba sai yanzu za ki min murnar kare”dariya Nabee ta tuntsure da ita tace “ke rufa min asiri ba ki ga irin masifar da Mami ta dinga yi min ba wai duk laifina ne tunda na san yanayin ciwon ki,shi kuwa dear ɗina ina ji lokacin da ya ke cewa wace ƴar iskar ce Nabeela da har ta tayar mata da ciwon?”buge bakinta nayi nace “Nabee wlh ki fita idona in rufe kar ki sake yi min wannan wasar Daddyna ba tsarar ki ba ne da har za ki rinƙa kiran shi da chéri ki wannan ai cin kashi ne”gira ta ɗaga min tace “to sai mi dan ka cewa wanda kake so chéri ?wlh ni kuwa da zai aure ni da…”ban tsaya saurarenta ba na wuce classe dan kusan kullum sai tayi min hirar ta na son Daddy duka-duka sau biyu ne kawai ta taɓa ganin shi shikenan ta haukace da son shi da roƙona in bata number shi,ta yaya ma mai hali irin na Nabee zan barta ta raɓi wani nawa?macen da ta mayar da kanta KARUWAR GIDA kullum ta na cikin yawon bin hotel-hotel da gidajen rawa?.
Rungumo ni tayi ta baya tace “haba Fadimatuna miye na yin fushi da ni kuma a nan?” “Ba fah fushi nayi ba kawai na ga ba ki gajiya da faɗar abinda ko a mafarki ba zai taɓa yiyuwa ba”na faɗa ƙoƙarin ɓanɓare hannuwayenta da ta riƙe ni da su,tambayata tayi da “dan miyasa kika ce haka?”ba tare da shakka ko fargaba ba nace “saboda inganci da rashin sa ba za su taɓa haɗuwa ba”sake ni tayi ta dawo a gabana ta na kallona cikin ido tace “Ni kam sai na gwada maki ta yadda za su haɗu har su garwaya”ta na gama faɗar haka ta samu waje can ƙarshen classe ta zauna ta bar ni da faɗuwar gaba,tabbas na fi kowa sanin wacece Nabee duk namijin da ya burgeta to tabbas sai ta san yadda ta yi ta same shi.