KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ayya Daddyn Mimi banda lafiya kuma”da sauri ya kai hannun shi kan wuyanta ai kuwa yaji kamar da alamar zazzaɓi,magani ya bata sannan ya fita ya nemo masu abinda za su ci su da masu gadi.

Sai da aka kwashe wata ɗaya cur sannan Mami ta fara sakin jikinta ta koma kamar da,Mimi kuwa na gidan Hajiya Babba zamanin ta.
Tun da safiya ta waye ta ke zabga amai,babu ɓata lokaci Daddy ya kaita asibiti awon farko Dr Ibrah yace mashi “congratulations kai ma ka kusa zama baba”da murna Daddy ya rungume shi can kuma ya sake shi yayi sujada shukur.

Gira Dr Ibrah ya ɗagawa Mami ya mata nuni da cikin jikinta sannan ya nuna kan shi ma’ana dai ciki na shi ne ba na Daddy ba,kawar da kai tayi gefe dan dama tun farko ba tayi wata murna ba.
Murmushi ta saki tare da ambaliya hawayen baƙin ciki na da aurenta za ta haifi shege a zuci tace “lalle na tabbata KARUWAR GIDA tunda har zan haifi ɗan da ba na mijina ba”Daddy kuwa a tunanin shi kukan murna Mami ta ke a haka ya kwasheta suka wuce gidan Hajiya Babba…..
[05/12 à 14:08] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822

Page 35-36

Haka Mami tayi rainon cikinta har ta haifi ƴarta mace aka saka mata suna Ameera,sosai Daddy ke nunawa ƴaƴan nashi so amman ya fi ƙaunar Mimi.
Sam ba za ka ce Mimi ba ƴar su ba ce yadda suke ririta ta da nuna kulawar su fiye da Ameera,lokaci zuwa lokaci Dr Ibrah ya na kawowa Mami farmaki a duk lokacin da Daddy ya fita tun ta na kaucewa har suka ɗinke kullum sai sun yi RDV.

Ameera na da 3years Mami ta kuma samun wani cikin,sosai Daddy ya nuna murnar shi.Ita kuwa Mami masifa ta rinƙa yiwa Dr Ibrah na ya munafinceta bai yi mata allura hana haihuwa ba,to daga nan ne suka yi baran-baran suka rabu Mami ta tuba.
Cikinta na shiga watan haihuwa ta haifo Twins duk mata aka sa masu Imane da Ihsane to tun shi ba ta sake haihuwa ba.

***Cigaban labari

Wani irin gumi ne ya shiga ketowa Daddy,sam bai tsammaci haka ba tunanin shi ma bai taɓa kawowa da rainon ƴaƴan wani ya ke ba.

Ana cikin haka wayar shi ta ɗauki ringing Dr Ma’aruf ya gani cike da mamakin kiran Daddy ya ke kallon screen ɗin wayar dan an fi shekarar da tafi goma rabon shi da Dr Ma’aruf ɗin,zai iya cewa ma tun tashin su daga gidan da ya basu saboda ya sha gwada lambar amman ba ta shiga.

Sai da ta tsinke Daddy bai ɗaga ba,wani kiran ya shigo danne zuciya yayi ya ɗaga kiran ba tare da yace komi ba “Assalamu alaikum Alhaji na zo gida ne sai na gan shi a rufe”
“Ina Clinic Agaji ne Madam babu lafiya”ba’a ƙara cewa komi ba daga ɗayan ɓangaren aka kashe wayar.

Can kamar minti ashirin sai ga wata dalleliyar mota tayi parking a harabar asibitin,su uku ne duk sukafito Alhaji ne,sai Agaishat da kuma Ma’aruf wanda shi ya tuƙo motar.

Dialing number Daddy yayi ya na ɗagawa yace “am ka fito mu na harabar asibitin”da “toh”Daddy ya amsa ya miƙe a kasalance ya fito.
Gaban shi ne ya faɗi lokacin da yayi tozali da Agaishat wacce ta ƙurawa hanya ido,ƙarasowa yayi amman ya kasa ɗauke idon shi kanta saboda tsantsar kama da Mimin shi da ya ga ta na yi.
Hannu ya basu suka yi musabaha yayinda suka fara tambayar shi mai jiki,jin murya Agaishat kuma ya sa zuciyar shi yin rauni tabbas ko makawo ya laluba ya san wannan jinin Mimi ce.

Murmushi Dr Ma’aruf yayi haɗi da sosa ƙeya yace “in ba za ka damu ba ina son mu ɗan zauna za mu yi magana”ya faɗa ya na mai ɗan waige-waige.

Murmushi Daddy yayi yace “maganar mi kuma Dr ?bayan tun kafin ka faɗa na san kun zo nan ne dan ku raba ni da Mimina”ya yi maganar cikin tausayi yayinda idon shi da suka yi ja tun ɗazu suka cika da ƙwalla.

Alhaji yace “Ma’aruf kenan dai dagaske ɗin ne Allahu Akbar”ya faɗa ya na mai zubewa ƙasa ya na sujidah shukur kafin ya ɗago ya fashe da kuka kuma???? Agaishat ma kukan ta taya shi.

Waje suka samu can ƙarƙashin innuwar mangwaro suka zauna Dr Ma’aruf ya shiga baiwa Daddy labarin komi dangane da haihuwar ƴaƴa Mazan da Allah ke azurta Abban shi sai Mimi ce kaɗai mace.

Ajiyar zuciya Daddy ya sauke yace “to miyasa ba ka barta cikin gantan ta ba?”Dr Ma’aruf yace “saboda kar a cutar da ita,na san in na barta za’a kasheta ne saboda su sauran matan ba sa so ace an fifita ƴar kishiyar su fiye da nasu ƴaƴan kuma maganar da ni ke yi maka yarinyar da na masayan tuni suka kasheta duk da ƙoƙarin kariyar da nayi ta bata”

Cikin son kawar da zancen tashin hankali nan Daddy yace “yanzu dai Mimi ta na Niamey in shaa Allah gobe zan sa su dawo”

Mimiƙewa suka yi sun so shiga duba Mami amman Daddy ya hana ta hanyar ce masu barci ta ke,su na tafiya Daddy ya kira Alhaji Kamal yace ya yiwa su Hajiya Babba réservation ta dawowa gobe ya na gama faɗa ya kashe wayar shi kwata-kwata.
Takarda ya samu gun Dr ya yi rubutu ya aje ta kusan kan Mami kafin ya fice,bai zarce ko ina ba sai gidan Hajiya Babba .
Toilet ya shige ya sakarwa kan shi shower,a sannu ruwan ke dukan fatar jikin shi lumshe ido yayi ya na tunanin rayuwa hawaye idon shi suka shiga fitarwa.


Arerewa haɗi da shewa Lami tayi tace “wuuu KARUWAR GIDA an kusa saukewa,a toh dama ƴan jami’a ai duk ƴan iska sun fi yawa yanzu ba sai ayi mu gani ba in tusa ta hura wuta sai mu ga yadda za’a yi karatun hhh”ta ɓaɓake da wata dariya mugunta.

Shiru Anna tayi ta na nazartar kalaman Lami kafin ta maido duban ta ga Fadila wacce tayi fari fyarau ta ƙara ƙiba,kallon da Anna ke yi mata ne yasa ta tsargu kawai sai ta miƙe ta nufi ɗaki.

Tafiyarta Anna ta bi da kallo ta na sake tantance ta,ko minti ɗaya Fadila ba ta yi ba Anna ta shigo.Da sauri ta juyo ta na kallon mahaifiyarta ta haɗi da zare ido kamar wacce ta yiwa sarki ƙarya.
“Cire min hijabin jikin ki baƙar munafuka”cewar Anna ta na harar Fadila,kasa cire hijab ɗin tayi hakan yasa Anna ta ja hijabin da ƙarfi ta cire.
Taɓa hannuwa ta shiga yi ta na salalami sakamakon cikin Fadila da ta gani kamar ƴar ƙwarya ya fito yayi mata wani cercle ai Anna ba ta san lokacin da ta ɗauke ta da mari ba ta shiga dukanta haɗi da tambayarta uban wa yayi mata ciki amman ta ƙi faɗa.

Sai da taji wuya sosai sannan tace “Nasir ne Anna”wata uwar gwabza ta kaiwa bakinta nan take jini ya ɓalle,ƙetare ta Anna tayi ta shiga ɗakinta ta ɗauki hijabi ba ta zarce ko ina ba sai gidan su Nasir .

“Uban da ya ɗaura auren uwarka da uban ka Allah ɗebe masu albarka,asarare haihuwar asara da yarda Allah ba za ka gama da duniya lafiya ba”wannan shine abinda Anna ta faɗa lokacin da ta shigo gidan su Nasir madadin sallama.

Duk fitowa suka yi suna kallon ikon Allah, Iyani ta fito daga banɗaki kallon kwabo saura takwas ta yiwa Anna kafin tace “baiwar Allah daga gidan mahaukata kika gudo da za ki shigo mana gida ki na zage-zage?”

“Kutumar uban can!ba ki ma gane ni ba?to uwar Fadila ce wanda tanbaɗaɗen yaron ki ya ɗirkawa ciki”dariya Iyani ta fashe da shi tace “to sai mi dan yayi mata cikin?ai haka duniya ta ke dama abinda aka yiwa naka wata rana na ka ɗin ne zai yi ma wata dubi can ƴata ce nima wanin ne ya mayar da ita haka”ta ida maganar ta na mai nuna mata Fauziya wacce ke tsaye da ƙaton cikinta duk ya mayar da ita wata kala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button