KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kin yi shiru ko ba ki shirya zuwa gidan ba?”ya tambaye ni,a sanyaye nace “na shirya mana amman gun Hajiya Babba zan zauna”dariya Daddy yayi yace “naji kar a kawo ki guna kenan?”da sauri nace “eh” “tsorona kike Mimi?”yayi tambayar cikin kalar tausayi nace “a’a Daddyna”ya sauke ajiyar zuciya yace “kin ci abinci ne ?”na bashi amsa da “a’a Momy dai ta bani zuma ga kuma madara ta kawo min jira ni ke ta wuce in sha”shiru Daddy yayi ya na jin tausayinta a ran shi dan kuwa tuni ya gane an fara gyaran amarya ne.
“Ok to ɗauki ki sha da zafin ta sannan in kin yi wanka ki saka kayan da na kawo maki jiya Please kar kice ba za ki saka bra ɗin ba”Daddy ya faɗa ya na yanke kiran.
Ajiyar zuciya na sauke na ɗauki madarar da Momy ta aje na fara sha ina yamutsa fuska saboda goût ɗin hulba da naji.
***Bayan 1week
Tuni aka kawo lefena akwatina dozin kowane cike da kaya,tuni kuma Momy ke ta min gyaran jiki da na km.Cikin ƙanƙanan lokaci na canja na ciko sai sheƙi ni ke yayinda kuma ko muryar Daddy naji sai na wanke pant???? ban san dalili ba,sosai mu ka shaƙu da Daddy na ɓangaren soyayya sam bai nuna wata kunya dan zai aure ni balle ni da dama na mutu cikin ƙaunarsa da son shi.
In muna waya da Daddy za ka ɗauka da wani ƙaramin yaro ne ɗan 27years yadda ya ke tsayawa ya saurare ni ya biye min wajen shirme da sangarta haɗi da shagwaɓa.
A yanzu na saba da gidan mu ga kuma Fatima da ta dawo gidan mu wacce kusan sa’ata ce sai dai na girme ta,duk da ta na zaman ɗiyata amman ni a abokiya na ɗauketa.Ita ke min rakiya in zan je wani gun sai Daddy ya zo ya kai mu in mun gama abinda muke ya je ya ɗauko mu.
Abu guda ne ya tsaya min a rai yadda kwata-kwata Daddy bai son nayi mashi maganar Ameera balle uwa uba Mami,yanzu ma mu na zaune a mota mu na hira bayan ya maido ni daga gyaran gashi.
Wayar shi na karɓa ina kallon hotuna cikin gallerie yayinda shi kuma ya ke kallona lokaci zuwa lokaci ya na sauke ajiyar zuciya wacce tuni na gane ta bege na ce dan ni ba yarinya ba ce na san da Daddy ya na fama da sha’awa haƙuri kawai ya ke yi.
Hoton wata mage na gani na ɗago ina cewa “ina son irin wannan magen Daddy please ka sa a nemo min”laɓana ya tsurawa ido,babu zato babu tsammani naji saukar bakin shi kan lips ɗina da sauri na rumtse ido ina jin zuciyata na bugawa yayinda jikina ya ɗauki kyarma.
An ɗauki tsawon min biyar kafin ya janye daga jikina,sunkuyar da kai nayi ina jin wata kunya.
Kan shi ya ɗora saman volant ya rumtse ido ya na sauke ajiyar zuciya “bani gorar ruwa “ya faɗa cikin kasala duƙawa nayi kusan ƙafafuna na zaro ɗaya na miƙa mashi ya ɓalle murfin ya fara shan ruwan.
“Mimi dan Allah ki fara shirin tarbata tun ranar farko kin dai ga halin da ni ke ciki”Daddy ya faɗa ya na mai jingina da kujerar mota, rau-rau idona ya kawo ruwa dan tsoro da jajayen idon shi ya tsare ni…..
[10/12 à 16:05] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822
Page 41-42
“Ni dai a’a sai na gama karatu”na faɗa ina matsar ƙwalla,shiru Daddy yayi ya na kallona can ya nisa yace “sam hakan ba zai yiyu ba Mimi kuma maganar karatu ki mayar da shi gefe sai wata shekara kuma,yanzu time ɗin kula da ni ne”ɗagowa nayi ina kallon shi jin abinda ya ke faɗa kai na girgiza nace “please Daddy”kawar da kai yayi gefe dan kuwa sam bai ji zai iya cutar da kan shi ba alhalin Mimi ta isa ɗaukar nauyin namiji.
Jiki na min rawa na kamo tafin hannun shi wanda ya ke masifar sanyi ba kamar nawa ba da ya ke rau da zafi,dan kuwa kullumin jikina cikin ɗumi ya ke.
“Daddyna please ko yi za kayi ka bari har mu saba”cike da mamaki ya juyo yace “Mimi wane sabo kuma bayan wanda mu ka yi?”na turo baki nace “ni dai ban saba da kai ba”lips ɗin ta ya ƙurawa ido kafin kuma ya kawar da kai gefe dan ya na tabbacin in ya cigaba da kallonta to tabbas sai ya sake kai bakin shi ga laɓanta.
“Ki shiga ciki Mimi in na isa gida zan kira ki”Daddy ya faɗa ya na kunna mota,cikin ƙin jin daɗin rabuwar da za mu yi na fita bayan nayi mashi kiss ga kumatu.
Wajen da sanyin laɓanta ya sauka ya shafa ya na murmurshi kafin ya fara tuƙa motar mai gadi ya buɗe mashi gate.
“Wayyo Allah Anna zan mutu,wai wai Allah Innalillahi Allah na tuba ka yafe min wayyo na shiga uku na lalace”Fadila ke faɗa ta durƙushe tsakar ɗaki farin ruwa gami da jini na zuba ta ƙasanta yayinda Anna ke gefe ta na kallonta sai da kan ɗa ya sawo kai sannan Anna ta matso ta fara taimaka mata.
“Inyaaa”jariri ya canyara kuka yayin shaƙar iskan duniya,reza ta sa ta yanke cibi kafin ta aje babyn gefe ta kimtsa Fadila wacce ke fitar da gumin wahala.
Duk muƙu-muƙun Anna na kar ƴan unguwa su san da Fadila na da ciki ya tashi a banza,domin kuwa Lami ta fita ta gayyato matan unguwa suka kusa cika gidan a kunnen su kukan farko na yaro ya sauka ai suka shiga taɓa hannuwa kowa na faɗin albarkacin bakin sa.
A harzuƙe Anna ta fito ta na masifa ta na cewa “to ƴan gulma miye sabo a duniya?ina ce dai ba gare ta farau ba balle ya ƙare kanta kuma mutum bai san mi zai faru gobe ba sannan mai baya dayawa(zuri’a)bai faɗin aibun Ɗan wani”ai fah kuwa da sannu suka fara sulalewa.
A ɓangaren Nabee kuwa duniyar ta bisa tsinke ta ke ci musamman da ta samu wani Alhaji Waleed,duk da dai ya na da halin banza na bin mata amman shi tsakani da Allah ya ke son Nabee.
Cikin sigar roƙo yace “my Nabee kiyi haƙuri na turo manya su sa baki ayi auren nan da wuri wlh a matuƙar matse na ke na gan ki a gidana”kallon ƙaton tumbinsa Nabee tayi sannan ta ƙirƙiro murmushin ƙarya tace “haba dai duka-duka nawa na ke da zan yi aure yanzu?a’a ka bari duk ranar da na shirya ni zan faɗa ma lokacin da za ka turo kayan auren “ta ida maganar ta na sunne kai wai ita ala doli kunya.
Wani daɗi ya luluɓe zuciyar Alhaji Waleed ya samu mace ta gari mai kunya,cikin nuna ƴar damuwa ya kuma cewa “to bbna Allah matso lokacin da wuri ungo ga wannan kin sayi hoda”ya miƙa mata kuɗi amman Nabee ƙememe taƙi karɓa kamar kullum.
Hannunta ya jawo ya saka mata kuɗin, tsabar jaraba sai da yaji wani abu daga haɗuwar hannunsu.
A kunyace ta jimƙe kuɗin ta na godiya “Allah saka da alkhairi ya biya ka da gidan aljanna mafi ƙololuwa”Alhaji yayi murmurshi haɗi da jin daɗin addu’arta yace “haba ai babu godiya a tsakanin mu”ta ƴar dariya gami da fari da ido kafin ta gyara dogon hijab ɗinta ta fita daga mota.
Turus tayi tsakar gida ganin Iyani ta saka Nasir a gaba ta na zagi shi kuwa ya sunne kai “ai yanzu sai ka tashi ka sawo rago dan ni kuwa ko ƙwandala ta a to???? a bar ni da baƙin cikin wacan asararar kawai ina dalili kai kaje ka ɗirkawa ƴar mutane ciki ni ma an zo an yiwa tawa Ƴar masifar ka ce ka zoza mata”shi dai Nasir bai ce komi ba har sai da ta gama sannan ya miƙe ya bar gun.
Can tsakar dare ciwon mara da azaba iri-iri suka ishi Fauziya ta miƙe zaune ta na sharar hawaye.
Kallon Nabeela ta tsaya yi wacce ke sharar barcinta hankali kwance,wani irin da na sani ne ya wanzu a zuxiyarta kawai sai ta fashe da kuka.