KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kallon gidan saurayin nata tayi wanda shine ke tura mata blue Film,kawai kuma sai ta fashe da kuka ta na girgiza kai a fili tace “ai babu babban tonon asiri kamar Allah ya tsare ka gaban bainar nas ana bincikar ka tare da bankaɗo mugan halayen ka, Allah na tuba ka yafe min nayi alƙawarin ba zan taɓa barin idona ya kalli haram ba sannan zan zama mutumniyar kirki ta yadda Manzon Allah SAW zai yi alfahari da ni a ranar alƙiyama”ta na tafe ta na jaddada tuban ta gun shugaban talikai babu zato kawai sai ji tayi an kwasheta ta faɗi ƙasa daga nan kuma ba ta sake sanin abinda ya faru ba.

A ruɗe ABU MALEEK(Nimcyluv)ya fito daga mota ya na mai furta “Innalillahi wa’inna iley raji’un”sungumarta yayi ya saka bayan mota ya na mai tambaya inda zai samu asibiti nan kusa,nan wani ya kwatanta mashi.

Da isar sa Clinic Khasum Moctar aka shiga dubata,ashe suma ne tayi saboda furgici sai kuma kanta da ya bugu an wanke gun a naɗe sa da bandeji.
Shiga yayi ɗakin da aka shimfiɗe ta,tsayawa yayi ya na kallon ƙyaƙyawar fuskarta da hawaye ke shatata daga cikin manyan idonta masu dogayen gashi.
Ƙarasawa yayi ya saka hannunsa mai dogayen yatsu ya fara goge mata hawayen sai dai wasu kuma ke sake zubowa,”ya Allah!”ya furta a hankali cikin muryar shi mai sanyi buɗe idonta tayi suka sauka kan chocolat face ɗin shi mai ɗauke da jan leɓo.

Maida idon tayi ta rufe ta na tunanin abinda ya faru da ita,”buɗe idon ki petite beauté”ya faɗa ya na mai ɗaga fatar idonta wanda yasa doli ta buɗe su “ya jikin ki?”ya tambaye ta,samun kanta tayi da murmusawa kawai shi ma sai yayi murmushin yace “mi sunan ki?”
“Ameera”ta bashi amsa “Meera,ni sunana Abu Maleek yau ɗin nan na shigo garin Maradi cike da zumuɗin zan je na ga ƴar little sis ɗina da aka gani ga shi kuma gobe za’a ɗaura aurenta sai kuma Allah ya katse min hanzarin na banke petite beauté”ya na maganar ne ya na murmurshi mai nuni ya na cikin farin ciki sai kuma da ya zo ƙarshe ya kwaɓe fuska.

Murmushi Ameera tayi ta yunƙura za ta tashi da sauri ya taimaka mata “yi a hankali,bani number wani ɗan gidan ku sai na shaida masa ki na asibiti kar aje ayi ta neman ki”ai tamkar ya caka mata wuƙa haka Ameera ta shiga rera masa kuka.

“Oh my god!”ya faɗa ya na mai dafe goshi, Dr ya shigo ya na tambayar lafiya ko jikin Abu Maleek yace a’a nan ya basu takarda sallama gami da ordonnance ta maganin da zai saya.
Hijab ɗinta da fille de salle ta wanke aka ɗauko mata ta saka,hannunta Abu Maleek ya kama da sauri ta fuzge saboda wa’azin Malam Bashir Ghana ya ratsata kuma ya na zaune cikin zuciyarta daram.

“Yi haƙuri petite beauté”ya faɗa ya na murmurshi yayi gaba ta na bin sa a baya har mota,ko da suka shiga ya yiwa mota key bai zarce ko ina ba sai gidan su saboda kiran Alhaji da ke ta shigowa wayarsa ita kuwa Ameera kamar wacce aka rufewa baki ta kasa tambayar sa.

Cike da zumuɗin zuwan Yayana wanda duka-duka jiya ne kawai mu ka yi waya da shi amman yanayin barkwancin shi da yadda ya nuna ya na sona ya sa ni jin ƙagu.
Sai shagwaɓa ni ke zubawa Abba na har yanzu bai shigo ba alhalin yace ya na cikin garin Maradi wannan dalili yasa Alhaji ke ta kiran Abu Maleek.

Motar na tsayawa na rugo da gudu waje daidai nan Ameera ta fito daga mota goshinta naɗe da bandeji cak na tsaya ina ƙare masu kallo yadda suka yi wani masifar dacewa shi ya buɗe mata ƙofa….
[14/12 à 15:50] Cham~rose????: LITTAFIN KUƊI NE KI BIYA KI KARANTA HANKALI KWANCE,DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK KYAUTA DA WACCE TA TURO DA WADDA TA GAN SHI A WANI GROUP ITA MA TAYI SHARING IN KUN YI DAIDAI KUN SANI????????‍♀️ mai son biyan kuɗin karatu sai ta tuntuɓe ni ta WhatsApp +22795045822

Page 45-46

Da gudu mu ka ƙaraso muna masu rungume juna,wani marayan kuka Ameera ta saki ta na mai ƙanƙame ni kamar za ta huda jikina ta shiga.
“Ya isa haka mu je ciki”na faɗa ina mai cireta daga jikina,Abu Maleek ya ƙaraso murmurshi kan fuskarsa ya kama kumatuna duka biyun ya lotsa ƴan yatsunsa ya na jujuya su kamar wata baby haka ya ke min wasa “my rigimamar sis”nayi dariya ina mai ɗora tafukan hannuna kan hannuwansa nace “Ni dai ba rigimama ba, welcome my Bros”
“Merci bcp ma belle”ya faɗa ya na mai sakina ya kalli Ameera ya ɗan ɗaga gira “kin san ta ne?”ta gyaɗa kai alamun eh ni kuwa nace “she is my little sis fah”da mamaki yace “au ita ma nan gidan ta ke?” “A’a can gidan da aka raine ni dai”Na faɗi haka a daidai lokacin da mu ka ƙaraso ciki inda ahalin gidan ke zaman jiran mu.

Rungume Abba yayi yace “nayi kewar ka sosai Abbana”shafa kan shi Abba yayi yace “nima haka ya Mamar ka ya hanya kuma?” “Lafiyarta lau tace na gaishe ka ha…”tsukin da Hajiya uwar gidan Abba ta ja ne yasa shi juyowa da sauri ya sauke idonsa kan fuskar da har gaban abada ba zai taɓa manta ba domin ita tayi sanadiyar korar mahaifiyarsa daga gidan ubansa.

“Ina kwana Hajiya ?”ya faɗa murmurshi kan fuskarsa mai cike da ma’anoni,kawar da kai gefe tayi ta ƙi amsa gaisuwar shi kuwa ya gaishe da sauran matan Alhaji da Yanunsa.
Momy tace “Al Maleek mi ya tsayar da kai tun ɗazu mu ke jiran ka”ya sosa ƙeya dan shi sam ya manta da Ameera “wlh accident nayi ga yarinyar da na banke nan amman alhamdullah da sauƙi”
“Innalillahi to Allah ƙara kiyayewa”cewar Momy ni kuwa nace “amen,Momy ƴar Daddy ce fah “da sauri Abba ya ɗago kai yace “Mu’azam?”murmurshi kan fuskata nace “eh Abba”fuskokin Abba da na Momy ne suka canza yayinda Ameera ta sunne kai ta fara hawaye ganin haka na ruɗe na shiga tambayarta amman ta kasa bani amsa.
Hannunta na ja zuwa part ɗin Momy,nan fah Ameera ta faɗa min abinda yasa zuciyata daina bugawa na wani lokaci.
Hawaye ne sharrr suka shiga zubo min a fili na furta “why Mami? miyasa kika zaɓi tozarta mu a duniya da auren ki kin mayar da kan ki KARUWAR GIDA babban baƙin ciki har da haihuwar ƴaƴa Innalillahi wa’inna iley raji…”kasa idawa nayi saboda wani abu da naji ya tokare min zuciya idona suka kakafe yayinda ciwona na huka ya tashi zubewa nayi kan capet ina fidda numfashi dakyar da sauri Ameera ta fita waje ta na kuka wanda yayi daidai da shigowar Dr Ma’aruf “Mimi ciwonta ya tashi”ta faɗa cikin kuka da sauri Momy wacce ke zubawa Abba abinci ta aje ludayi yayinda shi kuma yayi zumbur ya miƙe Abu Maleek da Dr Ma’aruf suka rufa masu baya.

Taimako Dr ya fara baiwa Mimi wacce ba ta san halin da ta ke ciki ba,”ina ga fah doli sai mun je asibiti”cewar Dr Ma’aruf,Momy tuni ta fara hawaye nan suka ciciɓi Mimi suka fita da ita zuwa mota.
Ameera da Abu Maleek suka bi motar su Abba a baya,yayinda Hajiya ke addu’ar Allah sa Mimi mutuwa ce tayi.

Fitowar Daddy daga wanka kenan kiran Abba ya shigo mashi,da tsananin tashin hankali ya shirya ko mai bai shafa ba ya fice ba tare da ya baiwa Hajiya Babba amsar tambayar da ta ke mashi ba,mutanen da suka zo biki kuwa kallon shi suke suna addu’ar Allah sa dai lafiya.

Ikon Allah ne kawai ya kai Daddy lafiya,idon shi sun kaɗa sun yi jajur sabada tashin hankali.
Tamkar wani ƙaramin yaro haka ya bi ya ruɗe dan ma Dr Ma’aruf na kwantar mashi da hankali,ɗaukar lokacin da aka yi ba’a fiddo Mimi ba shi ya haifarwa Daddy kwanciya kan gadon asibiti aka sa mashi ƙarin ruwa.
Ameera ta zauna kusa da shi saboda in sérum ɗin ta ida ta je ta faɗawa Dr sai ya zo ya cire,hawaye ta goge ta kalli Daddy wanda idon shi ke lumshe ya na sharar barci “Mami kin cuce mu da kika ruguza rayuwar familyn mu ga shi sanadin ki Mimi da Daddy na kwance babu lafiya,ta yaya ne ma kike tunanin Daddy zai tsaya kusa da ke bayan kin zaluncesa zalunci mafi muni a duniya…”ta tsaya da zancen da ta ke ganin Abu Maleek ya shigo ya na kallonta,kallo mai cike da tausayi Allah ya gani tun farko yaji son Ameera ya ɗarsu a zuciyarsa yanzu kuma da yaji ainahin tarihin rayuwarta sai ya ƙara lunkuwa abu guda ya ke tsoro kar Abba ya hana shi auren ta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button