KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL

Nabee kuwa shiru tayi ta na ta tunani ashe maganata ta daketa sosai taji haushinta,ni kuwa a gaba na zauna na fiddo book ɗina na fara dubawa kafin malami ya shigo.

Students sai zuwa suke a sannu yayinda kowa ke harakar gaban shi wasu kuma na hira,Nabee na tunani yayinda ni kuma ni ke révision.Babu jimawa duk students suka shigo aji saboda ganin teacher ya nufo ajin mu,”good morning class”cewar teacher lokacin da ya shigo duk amsawa mu ka yi.
Cours ɗin shi ya fara na koyar da mu halshen English saboda ko da wani patient ya zo mai jin language ɗin amman a zahiri babu ma anglais cikin programme ɗin karatun likita.
Question ya fara kamar kullum ni ce ke yawan amsawa ya na gamawa mushen science ya shigo,haka dai mu ka ta yin cours har lokacin récréation yayi.

Fuuu Nabee ta bi ta gabana ta wuce ba tare da tace min komi ba saɓanin yadda mu ke tafiya kullum,har ƙasan raina naji babu daɗi sai na kwashe Books ɗina na bi bayanta ina kiran sunanta amman ta share ni sai da nayi ta bata haƙuri sannan ta haƙura saboda muna matuƙar son junan mu.


“Anna wai Abba cewa Nasir yayi sai na gama jami’a sannan za’a yi maganar auren mu”cewar Fadila ta na mai kallon mahaifiyarta ta wacce ke tatar ƙulun koko,kallonta Anna tayi tace “eh jiya ma mun yi maganar da shi sai na ga hakan ne ya dace kin ga ki na gamawa sai ayi bikin daga nan shi Nasir ɗin ba sai ya nemo maki aiki ba tunda baban shine shugaban ɗalibai?”cike da takaici Fadila ta dubi Anna tace “yanzu ke ma kin yarda Anna?in yi ta zama a har sai nan da wata shekara biyar alhalin ina cikin shekara ta Ashirin da bakwai a duniya?”tatar kokon Anna ta aje tace “Fadila kin san ciwon kan ki kuwa?ana son yi maki gata ke kuma ba ki gani?duk faɗin gidan nan wa kika ga yayi dogon karatu in ba ke ba?ina ce saboda kiyi karatu mu ka sayar da komi na mu dan inganta rayuwar ki,kishiyoyina najin haushin ba ƴaƴan su ba ne ke kuwa ki na baƙin cikin ɗan farin cikin da ni ke burin samu”da sauri Fadila tace “subahanallah haba Anna ta yaya Ƴa za ta yi baƙin cikin mahaifiyarta?”
“Eh ga shi kuwa ke ki na yi min,yanzu in Allah ya sa kun kammala karatun ki kin samu aiki mai ƙwari ai shikenan sai ki saya mana sabon gida mu samu mu fita daga cikin na laka”sororo Fadila tayi ta na kallon Anna kafin ta miƙe ta shige ɗan ɗakin su na laka wanda tsabar tsufan shi har ya fara tsatsagewa.

Nasir ta kira ta shaida mashi yadda suka yi da Anna “Fadila gaskiya ba zan iya zaunawa har 5years ba tare da aure ba,kin fi kowa sanin yadda ni ke son ki”cikin kuka Fadila tace “dan Allah Nasir kar kace haka wlh mutuwa zan yi in ka rabu da ni”cikin ɗan ƙasa da murya yace “naji zan jira ki amman da da sharaɗi”da sauri tace “na yarda minene sharaɗin?”Nasir yace “ki bari har mu haɗu school zan faɗa maki”….

Comment and share Please

Jikar Rabo ce ????
[17/11 à 15:50] Cham~rose????: KARUWAR GIDA…????????‍♀️
LOVE and ROMANTIC STORY

             ```MRS SADAUKI```????

☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️

I selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial 460260# to check Data balance.
Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

Whatsapp OR Call 08066268951

PAGE 5-6

Sai da ta nutsu sosai tace “Nasir ina jin ka tun ɗazu kace na zo kuma kayi shiru”ɗan jim yayi kaɗan kafin yayi gyaran murya har zai yi magana sai kuma ya fasa saboda bai san ta ina zai fara ba.

Fahimtar haka ya sa Fadila miƙewa tako ɗaya tayi taji ya rungumota ta baya,ido ta rumtse ta na jin zuciyar ta na yi mata raɗaɗi “Nasir miye haka sake ni mana”ta faɗa ta na mai son ƙwace kanta amman ya riƙeta gam.

Wani huci taji ya na sauke mata nan take jikinta ya fara kyarma,an ɗauki tsawon minti biyu ya saketa tare da juyota suna facing juna.Kai ta sunkuyar ta na jin wata irin matsananciyar kunya wai yau ita ce namiji ya rungume? “Ki yi haƙuri Fadila abinda ni ke son sanar da ke kenan amman laɓana sun kasa furta min,na sani ke ɗin kamila ce abu mai matuƙar wahala ne ki yarda da buƙatata a gare ki amman ki sani ba zan ɓoye maki ba aure ni ke so dan haƙuri na ya zo ƙarshe”.

Idonta ne ya ciko da ƙwalla tabbas ta san Nasir ya na sonta kuma tsawon shekaru biyun da su kayi tare bai taɓa yi mata magana banza ba balle har yace ya taɓa jikinta sannan ya yi mata nasiha a ko da yaushe,abu guda ɗaya ta sani shine da ta tambaye shi yawan azumin da ya ke ya sanar da ita saboda gujewa zina to amman yanzu miyasa ya ke jan su izuwa gareta alhalin ya san ita ɗin alfasha ce?.

“Nasir zina kake so mu yi?”da sauri ya girgiza kai ya na shirin riƙe mata hannu ta ja da baya,”kar ka taɓa ni”ta faɗa ta na mai ficewa daga cikin ajin.
Bakin titi ta nufa ta tsayar da adaidaita ta tafi gida,ta na shiga ta tarar da Anna ta na ƙullin kafa yayinda gefe ɗaya kuma radiyo ne kunne ta na sauraren wani shiri da ake mai taken Ƙafarka Mai gida.

Har ta kai ɗaki taji Anna na cewa “ke Fadila fito ki ɗauko min ruwa gidan malam Mussa tunda shi wannan bai da niyyar dawowa balle ya buɗe mana pampon an taɓa abu kamar na tsiya ka sa pampo gida amman duk in za ka tafi kasuwa sai ka rufe shi”Anna ke faɗa cikin masifa saboda hali irin na Abba da ya ke rufe pampon cikin gidan tun safe bai buɗe shi kuma sai in ya dawo daga kasuwa da marice.

Kukan da Fadila ta ke ne ya hanata fitowa sai yi ta ke kamar ranta zai fita,jin shiru yasa Anna miƙewa a hasale ta shiga ɗakin.
“Laha’ila mi aka maki kike kuka?”Anna ta faɗa ta na taɓa hannuwa,hawaye Fadila ta goge ta dubi Anna tace “dan Allah ki samu Abba ki yi mashi magana ya bar Nasir ya kawo lefen nan in ya so nayi karatun….”kumbutsar da Anna ta kai mata ne a baki yasa yin shiru tare da dafe bakinta,muciya Anna ta ɗauko ta shiga jibgarta da ita sai faɗi ta ke “ƴar baƙin ciki mai baƙin hali da ki tusa min baƙin ciki gwara na kashe ki na huta,wato gida da mota da kai ni ɗakin Allah shi kike ma baƙin cikin yi min”banda kururuwa babu abinda Fadila ke yi.

Indo ce ta shigo ta ceceta ta na mai baiwa Anna haƙuri amman kamar zugata ma ta ke sai balbali ta ke ta na ƙara nanata mata kalmar baƙin ciki????,ita dai Indo ta na mamakin hali na Anna domin kuwa Fadila ce kawai ƴarta mace duk ɗiyanta maza ne amman babu wanda ta azawa burinta sai Fadilar ƙila kuma dan ta fi su duk ilimi ne,dan su mazan babu wanda yayi boko mai tsayi duk sun kama sana’ar hannu sannan ɗawainiyar iyalinsu kawai suka sani.

“Innalillahi to ɗiyan asara kiyon asara Allah sa duk ku mace da yardar Allah wannan ƙullun kafar tawa da kuka zubar shi zai sanadiyar shigar ku huta da ku da wanda ya sawo ku”cewar Anna ta na mai korar awakin kishiyarta Lami wacce ta kwance su dan zuwa kiyo.

“Wlh can dai ta faltsar maki wacce ba ta ganin Annabi, jarababa mai farar ƙafa tunda kika shigo gidan nan Malam ya talauce”cewar Lami dan ita ma ba baya ba wajen iya masifa, Indo baiwar Allah duk cikin su ita ce babu ruwanta ƙila ko dan ita ce ƙarama kuma ba ta da wasu ɗiya da yawa.

Ta na nan kwance har aka kira sallah Asar ta na ganin appel ɗin Nasir na ta shigowa wayarta tare da saƙonni uwanda rabinsu na ban haƙuri ne da kuma nuna mata zallar soyayyarta gare shi.
Wani murmurshi Fadila tayi mai ciwo lokacin da ta turawa Nasir saƙo kamar haka na amince da buƙatar ka sai dai kayi min alƙawari duk runtsi ba za ka guje ni ba sannan sex sai bayan aure

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30Next page

Leave a Reply

Back to top button