KARUWA GIDA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ina tsaka da kurɓar tea Daddy ya dube ni yace “Mimi ɗazu wata ƙawar ki taje office ɗina”wani irin tari ne ya zo min ban san lokacin da na saki kofin tea ɗin ba ya zuba a cinyata.
Ban damu da zafin da naji ba dan maganar Daddy ta fi min raɗaɗi fiye da zubar shayin,”subahanallah! Mimi lafiyar ki kuwa?ba ki ji ciwo ba?”Daddy ya faɗa ya na mai sa wani ɗan hankicip ya na goge min inda tea ɗin ya zuba tsananin zafin shi har tururi bujen nawa ya ke.
Tarin da ni ke sam ya ƙi lafawa kamar ma asama ɗina ke son tashi ,ruwa ya bani a kofi na sha yayinda Twins duk suka kewaye ni.Ƙirjina na ɗan bubuga da hannu saboda ko naji sauƙin abunda ya tokare min shi,”Daddy mi sunanta ne?”na faɗa ina mai danne tarin,ƙin faɗa min yayi ko dan ya ga Mami ta fito ne oho sai ma sannu da ya shiga jero min.
“Minene ya sameta daga in shiga ɗaki in fito?”cewar Mami da alamun damuwa a fuskarta “babu komi tea ɗin ne ya ƙware ni”na faɗa cikin kawar da zancen ƙawata da tafi office ɗin Daddy.Magani Mami ta ɓalle min ta bani na sha nan ta sake haɗa min wani tean,babu yadda na iya haka na rinƙa shan shi amman a zahirin gaskiya sam ya fita raina.
Miƙewa nayi na koma ɗaki,yau ma kamar jiya a kwance na tarar da Ameera ta sa écouteurs(abun sauraro na kunne)ta na kallon wani abu a wayarta wanda ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba Film ɗin batsa ta ke kallo.
Teddyna da ke kan gado na je zan ɗauka da sauri ta kife screen ɗin wayar wai dan kar na gani,a falo na koma dan bata liberté saɓawa Ubangijinta yadda ta ga dama dan dai kuwa duk wanda yayi daidai a duk inda ya ke ya sani haka ma akasin haka.
Kira Nabee nayi sai dai tayi ta sonné ba ta ɗauka ba har sau biyu,wasu hawayen baƙin ciki ne suka silalo min “ta yaya ma zan bari KARUWAR GIDA tauraruwa mai wutsiya ta kafawa uba mahaifina tarko na ƙyaleta?to wai yanzu minene mafita koko na roƙi Daddy akan ya aureta tunda ya fi dai ace ƙawata ta san sirrin mahaifina ta hanyar zina?”na faɗa a zuci tare da ƙanƙame Teddyna gam kamar zan shige cikin shi.
Turo ƙofa aka yi,Mami ce ta shigo kawo min chocolat ɗin da na sa a sawo min.Tsayawa tayi ta na nazarina bayan na karɓi robar, “Mimi ko sai mun je asibiti sai na ga kamar ma kin ɗan rame lokaci ɗaya”cewar Mami ta na shirin zama kusa da ni mu ka jiyo ihun Ameera.
Zuciyata ce ta bada dam ganin Mami ta nufi ƙofar kamar na riƙe ta na hanata zuwa sai dai bakina ya yi min nauyi,ko second ɗaya ba tayi da shiga ba naji ta na salalami da sauri na tashi na mara mata baya.
Tsaye cak Mami tayi ta na kallon Ameera wacce ta haye pilow ta na….ga kuma video ta na kallo,har mu ka ƙarasa kusa da ita ba ta san mun zo ba sai ihunta ta ke saboda ta ƙure ƙarshen volume ɗin.
Kujerar dressing mirror Mami ta ɗauka ta buga mata ita a tsakar baya babu shiri tayi watsi da wayar tare da cire écouteurs ɗin ta na mai fasa uwar ƙara.
Da kujerar Mami ta shiga jibgarta har sai da ta kare,Ameera na ta kuka a ƙarshe Mami ta mayar da ita kujera ta ɗale sai kishi take ta na buga kanta da ƙasa.
Ganin abun ya yi yawa na ruga aguje dan kirawo Daddy kar Mami tayi kisan kai,a yadda na ga Mami ta haɗa mata jini da majina ba ƙaramin tayar min da hankali yayi ba ina zuwa na faɗa jikin Daddy a sume……
Comment and share Please
Jikar Rabo ce ????
[18/11 à 15:29] Cham~rose????: KARUWAR GIDA…????????♀️LOVE and ROMANTIC STORY
```MRS SADAUKI```????
☀️ FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️
I selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
10GB@===2,600
15GB@===3850
20GB@===5000
40GB@===9900
Dial 460260# to check Data balance.
Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
Whatsapp OR Call 08066268951
PAGE 7-8
Frigo Daddy ya nufa ya ɗauko ruwan sanyi ya malala mani,ajiyar zuciya na sauke tare da yi mashi nuni da ɗakina.
Shi sai yanzu ma ya tuna a firgice na fito ashe,bisa moquette ya shimfiɗe ni ya nufin ɗakin wanda tuni Mami ta sumar da Ameera ta koma gefe ta na rusa wani irin kuka mai taɓa zuciya.
“Innalillahi wa’inna iley raji’un”cewar Daddy ya na mai nufar inda Ameera ta ke a sheme babu numfashi,bai samu damar tambayar Mami abinda ke faruwa ba ya ciciɓeta ya nufi waje da ita tuni mai gadi ya wangale mashi get.
Tun a hanya ya yiwa Dr Ibrah magana wanda shi ma tun a waya ya nuna tashin hankalin shi,suna zuwa tuni nures sun fito da gado aka ɗauke ta aka aza bisa tare da turata zuwa emergency.
Idanun Dr Ibrah sun yi jawur saboda tashin hankali da ɓacin rai,sam ya kasa tambayar yadda aka yi wannan lamari ya faru ko kuma akan minene.
Tagumi Daddy yayi ya rasa mi ke mashi daɗi, Allah na gani ya na son ƴaƴan shi fiye da komi da na duniya da ya mallaka,wayar shi ya zaro daga aljihu ya danna kiran Mimi bugu biyu na ɗauka cikin sanyi murya nace “Daddy…”ajiyar zuciya ya sauke yace “Mimina ya jikin naki?”nace “na warke Daddy ina Ameerai?”
“Ta na can likitoci na kula da ita”cewar Daddy,”ok Daddy ga mu nan zuwa ita kanta Mamin ba ta ji daɗin abinda ta yi ba kuma kamar ciwon ta na son tashi” Daddy ya tambaye ni “Mimi minene ya faru?laifin mi Ameera tayi da har Mamin ku tayi mata wannan dukan?”shiru nayi na kasa cewa komi dan tuni Mami ta fita ta shiga motar da drever zai kai mu asibitin,jin na ƙyale yasa Daddy kashewa.
Twins na ja mu ka nufi mota,a baya mu ka shiga dukan mu drever ya ja mu zuwa babbar asibitin Dr Ibrah abokin Daddy,duk in ba mu lafiya can ake kai mu ko kuma shi ya zo har gida ya duba mu.
Da taimakona Mami ta shiga cikin asibitin,ba tare da wani ɓata lokaci ba aka bata gado tare da saka mata ƙarin ruwa duk da na lura ba da son ran Dr Ibrah ba dan sai wani hararen Mami ya ke kamar zai doke ta.
Mu na nan jungum har aka fito da Ameera an wanke mata fuska tayi fyau yayinda aka naɗe wuraren da taji ciwo da bandeji,sai a lokacin naji hankalina ya ɗan kwanta dan tuni ta na ta barcinta.
Ina nan zaune kusa da Daddy yayinda na sa su Mami da Ameera ina kallon yadda kowa ke sauke numfashi,shi kuwa Daddy ina lura da shi sai satar kallona ya ke ya na danna wayar hannun shi.
Kamar an ce in juyo nan idona suka yi tozali da hoton Nabee bisa screen ɗin wayar Daddy,ta sha riga da wando baƙaƙe yayinda ta baza sumar kanta irin ta Bugajen asali a kafaɗunta ,laɓanta sun sha man leɓe sai ƙyalli suke yayinda ƙwala-ƙwalan idonta fara ta ranbaɗa masu kwalli sai ya fito da tsantsar kyawunta.
Zuciyata ce ta fara tafasa ta na halbawa da ƙarfi lokacin da na ƙara ƙarewa hoton kallo ta wutsiyar ijiya,a gaban rigar kusan a buɗe ya ke wanda hakan ya baiwa dukiyar Fulaninta fitowa kusan rabi ga wata irin gantsarowa da tayi irin dai na ƴan duniya.
Hawayen da suka cika min ido ne suka samu damar silalo min,tabbas zuciyata ta yarda kan Daddy ya faɗa tarkon Nabee tunda har ya kasa ɓadda hoton ta ya tsaya ya na ƙare mashi kallo.
Fita nayi waje nan na tarar da twins suna cin biscuits da chocolat ɗin da na san bai wuce Dr Ibrah ya saya masu,suna ganina suka taso su na gwada min abubuwan da ke cikin ledar.
Ban iya ce masu komi ba sai bajewa da nayi a kan tabarmar da ke shimfiɗe ina sauke numfashi,saƙo ni ke son turawa Nabee to amman mi ma zance mata alhalin tuni wuri ya ƙure min har ta turawa Daddyna karuwan hotunan ta uwanda hatta mace ƴar uwarta ta gan su sai ta yaba da kyawun hallitarta balle namiji?.