KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 1 to 10

Maryam obam????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  6to10

Washe gari da safe salma tana kitchen tana hada breakfast mahmud ya shigo daka shi sai gajeran wando da singlet a jikin shi, kasan cewan yau sati babu office duk ranan da yake gida tare suke girki suna yi suna fira cikin so da kauna har suka kammala suna cikin yin breakfast wayan shi yayi kara ya duba yaga Hajiya a screen din wayar cikin ladabi ya dauka tare da gaida ta, ta gefenta ta amsa cikin fara’a, tace anjima kazo ina son ganin ka, ya amsa da toh insha Allah zanzo bada dadewa ba, ta kashe wayan, salma wacce tayi shuru ko ba’a fada ba tasan mamnshi ce, suka hada ido ta sakar mishi murmushi yace Mata Hajiya nason gani na bari inzo inje tace gaskiya ya kamata kaje kaji ko miye, mahmud yana matukar son salma yanda take nuna ma yan uwanshi kulawa duk dasu basa ganin hakan komai tayi a wajansu bata iya ba, amma bata taba nuna gazawa wajan yi musu hidima duk da Halin da suke nuna Mata, mahmud yayi daki baiyi 30 minutes ba ya fito cikin kananan kaya wanda ya kara fito mishi da kyawunshi, salma tace anya ba zance zaka ba kuwa yayi dariya tare da fadin haba dai ina da kamarki a gida ai babu ni babu zuwa zance ke kadai kin isheni tayi dan murmushi tare da fadin Hajiya na jiranka gwara ka tafi yace hakane bari inje in dawo ya fita…..

Mahmud yana bayan motar driver yana janshi sunzo wajan traffic suka tsaya tazo ta wajan motarshi tana fadin sadaka fisabillillahi, ganin fuskanta yasa yayi saurin saukar da glass din motar amma lokacin traffic ya basu alaman su wuce driver yaja motar sukai gaba, har suka karasa gidan Hajiya yana tunanin yarinyar wanda baiga dacewan ace tana bara ba, tsayuwan motar da yaji yasan sun karaso ya fito cikin tafiya irin ta wanda yaji naira, masu aikin gidan suna ta gaidashi cikin girmamawa suna Jin dadin ganin shi domin indai yazo gidan to ranan suna shan kyauta, kai tsaye falo ya nufa yako ci Sa’a hajiyan na falo nan ya zauna yana gaidata ta amsa cikin fara’a, suka dan taba fira na tsakanin d’a da uwa, tayi gyaran murya tace abun da yasa na kiraka na yanke wani hukunci duk da ba yardan ka nake nema ba, yace Hajiya ai duk abun da kika yanke nasan bazai cutar dani ba, tayi dan murmushi tare da fadin na maka Mata lokaci daya yaji zufa ta keto mai kuma wannan karon na gida ne, fauziya na zaba ma, nan yaji gabanshi ya fad’i yace Hajiya Wace fauziya? Tace wacce ka sani mana yar uwarka, ji yayi komai nashi ya tsaya, yace Hajiya da an zabo min wata amm…….  Dakata malam wato a zabo maka wata bare wacce matar ka zata koreta koh toh wlh baka isa ba, koh kaki koh kaso saika auri fauziya, yai kasa dakai tare da fadin Hajiya kiyi hakuri Allah yasa hakan shine alkairi tace amin cikin fushi, tabbas an cuceshi domin fauziya ba irin tsarinshi bace bata da tarbiya uwa uba bata da kamun kai ga shegen sangarta da rashin kunya babu mai fada Mata taji, shi baima cika shiri da ita ba, ganin tunanin bashi da amfani yasa yama Hajiya sallama ya wuce…… 

Tunda mahmud ya koma gida salma taga yana yinshi tasan akwai abun daya faru, tamai Sannu da zuwa ta koma kitchen ta kammala hada lunch, kai tsaye bedroom dinsu tayi ta ganshi a kwance yayi shuru yana tunani, tace dear lafiya kuwa naga kayi shuru haka, yayi dan gajeran tsaki tare da fadin lafiya babyna, ta kafeshi da ido tace kar muyi haka dear nafi kowa sanin ka, in kana farin ciki na sani haka in kana da damuwa na sani, yayi shuru can yace salma dazu da naje gidan Hajiya tayi min maganan aure, nan taji wani iri amma saita dake, tace kai dear shine kake damuwa, yace babyna Kin San ko wacece kuwa? Ta girgiza kai alaman a’a yace fauziya ce fah wacce Hajiya tace zan aura, nan taji dus domin tafi kowa sanin waye fauziya, wani kishi ya taso Mata amma saita dake, tace dear aiko abu yayi kyau kaga tuwo na mai na, kaga da auran wanda baka sani ba gwara wanda ka sani, kallon salma kawai yake domin yasan dama hakan zai faru, sai yasa a kullum yake son salma tare da tausaya Mata, duk abun daya kawo za tayi na’am dashi duk munin abun indai bai saba ma addini ba, ya dan janyo ta jikin shi tare da fadin Allah yayi miki Albarka, tayi murmushi tare da fadin muje kaci abinci, yace no ki kawo min nan tace ok sir, tayi waje, tana shiga kitchen ta saki kuka mai zafi tare da wani zafin kishi daya taso Mata, yanzu mahmud fauziya xai aura wani abu ya taso mata a wuya…….. Hmmm anya salma zata iya jurewa kuwa????? 

Maryam obam????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  10to15

MASOYA KUYI HAKURI NAJI NA SHURU YANZU INSHA ALLAH NA DAWO ZANCI GABA NA DAN DAKATA NE SABODA RASUWAN MAHAIFINA ALLAH YAJI QANSHI YASA YA HUTA, WA INDA SUKA KIRANI SUKAI MIN TA’AZIYA DA WANDA SUKA ZO DA WA INDA SUKAI MIN MESSAGES  INA MIKA GODIYA TA A GAREKU ALLAH YABAR ZUMUNCI????????

Wannan page din naki ne kawata ta rai da rai habiba s Ali????????

Salma taci kukanta lokaci daya ta share hawayen tare da wanke fuskanta dan kar mahmud ya gane tayi kuka, ta gama hada mai kayan abincin ta dauka ta nufi dakin dashi kallo daya yayi mata ya gane tayi kuka dan idanta ya dan sauya kala duk sai yaji babu dadi ta kuma bashi tausayi inda badan karya saba ma mahaifiyarshi ba toh wlh daya fasa auren fauziya dan baya kaunar ganin bacin ran salma ko abun da zai daga mata hankali, bayan ta ajiye abincin ta koma gefe ta zauna tashi yayi yaje kusa da ita yayi hugging nata tare da mata magana cikin kunne salma mai yasa kikayi kuka kin san bana San ranki na baci dan Allah ki daina sama kanki damuwa please my dear kinji tayi dan murmushi tare da fadin waya cema nasa ma kaina damuwa ka daina tunanin haka babyna ina farin ciki yanda baka misali yayi dan murmushi tare da kara janyota jikin shi….. 

Hajiya zaliha na zaune a tsakar gida tana gyara shinkafar tuwo fauziya ta shigo tana sanye da riga da wando na yan kanti duk sun matse ta, ga wani kitso da tasha na attachment ta yafa wani siririn gyale waita rufe gashin amma gaba daya rabin gashin a waje yake,tace Amma yau tuwo kuma za kiyi daka shugowa na nayi Karo da tuwo, hajiya zaliha tace wai ina kikaje baki dawo gida ba tun jiya sai yanzu nayi ta kiranki baya shiga, fauziya ta dan tabe baki tare da fadin daka dawo wana har kin fara jeromin tambayoyi ko zama banyi ba ta daure fuska ganin haka hajiya zaliha tace kiyi hakuri y’ata hankalina ne ya tashi da ban ganki ba wlh, ta dan ya matse fuska tare da fadin gidan kawata na kwana sai yasa ban dawo ba, hjy zaliha ta washe baki tare da fadin yar albarka mai kashin Arziki albishirinki tace goro, ta mika mata hannu fauziya ta xaro dari biyar ta bata, tace wlh yayi kadan ai dubu goma zaki ban sai kiji albishir mai dadi, fauziya tace ni banda kudi in zaki fada ki fadamin in kuma ba zaki fada ba kinga bani kudina, hjy zaliha tayi dariya tace shikenan bari in fada miki na shawo miki matsalanki binta ta yarda mahmud ya aureki tsalle fauziya tayi tare da fadin Amma ban San wasa fah, tace wlh y’ata dagaske nake nan fauziya ta tashi tana rangada bud’a tare da rawa ta zaro dubu ishirin taba maman tace ga kyautar albishir Amma ya akai ta yarda haka cikin sauki, hjy zaliha tace ni wasa ce wajan wani boka naje yaban wani turare yace indai zani gidan insa komai nace mata zata yarda, fauziya tace amma ina tsoran ta canza ra’ayi kin san yar uwarki din nan sai a hankula, hjy zaliha tace wane ita indai akwai bokaye kuma ina da rai ai Sai kin auri mahmud wlh munci daula mun barta suka saki shewa cikin jin dadi duniya tasu, 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button