KISSA KO MAKIRCI Page 1 to 10

Hajiya zaliha tana sa kaya fauziya tace ina zaki kuma kike ta sauri tace wajan malam mana inje inji yanzu miye abun yi dan kin San dole sai mun san yanda mukayi muka rabashi da wannan matar tashi dan yana bala’in tsoran ta, itama kin San a tsaye take sai munyi dagaske karta bata mata shirin mu sai yasa gwara ma ayi abun da wuri fauziya tace nima ai banga ta zama ba, tare zamu hjy zaliha ta saki dariya tace yauwa yar gari gwara muje in kina da wata matsalan saiki fada mai ma ya miki magani, suka fita.
Sun isa gidan boka yau sunyi sa’ a babu kowa a wajan, nan suka zauna a kasan carpet din dake falon, hjy zaliha tace kaga likita mai bada maganin ko wani ciwo, mai yaye ma mutum damuwa wanda ya bika ya more wanda ya bijire maka yana cikin wahala, wa’iyazubillah Allah yasa mu dace, ya saki dariya wanda tun shigowansu idonshi nakan fauziya yace wannan fah, zaliha tace y’ata ce, wanda na baka labari ya lashe baki tare da fadin toh toh barka yan mata naji duk matsalanki, yanzu mai kikeso ai miki, tace ina so a mallake min mahmud sai abun dana ce ya soni kaman zaiyi hauka, yaji ya tsani matarshi, sai kuma mahaifiyarshi ita inaso a mallake min ita, boka ya fara dariya ya fara duba kasa lokaci daya ya daure fuska gaba daya muninshi ya fito, ya kalli fauziya yace kina da aiki a gabanki domin mallakan mahmud abune mai wuya dan matarshi tana yawan tsayuwan dare shima yana yi, tace toh yanzu miye abunyi yace abu daya ne shine Zan sa ayi auran da wuri in kin shiga gidan sai muga ko zamu iya mallake shi, ga wannan ki dinga amfani dashi kullum ta amsa turare ne sannan ya bata wani laya yace tasa a jikinta ta daure ta amsa tare da fadin to, yace karta taba kwance layan sai anyi bikin yace suje gida zasu ga abun mamaki suka bashi kudi suka wuce……
Fauziya tace anya wannan bokan ya iya aiki kuwa? Hjy zaliha tace tabdi ai bana tantama akan aikin sa wlh, suna firan har suka je gida suna isa kofar gida suka ga mota ko ba’a fada ba sun San hjy binta ce, cikin sauri suka shiga gidan, suka ganta zaune kan kujera a tsakar gida, hjy zaliha tace a’ah yaushe kika zo badai kin dade ba tace a’a ban dade da zuwa ba, fauziya ta gaidata ta amsa cikin fara’a tace nazo miyi maganan bikin nan ne tun da kika zo na jiki shuru hjy zaliha cikin jin dadi tace aida kirana ma kikayi, fauziya cikin murna tace gskiya wannan bokan ya iya aiki……… Hmmmm
Share this
[ad_2]