KISSA KO MAKIRCI Page 11 to 20

Mahmud yana mota yana bakin cikin wannan auren da ake son yi mishi, shi baiki kara auren ba amma wacce aka bashi ne yake ganin ba’ayi mishi adalci ba, gashi kuma auren zumunci yayi dan tsaki tare da fadin Allah ka zaba min mafi alkairi.
Biki ya rage saura kwana biyu, amarya tana ta shan magani kala2, dan so take ta nuna ma mahmud itama ba’a baya ba, kawayenta sun cika gidansu komai naci dana sha hjy binta ta bayar da kwangila ana kai musu, har wanda xa’aci ran daurin aure, fauziya sai cika take tana batsewa cikin kawayenta, yayin da suke ganin tayi sa’a babba domin samun namiji kaman mahmud ba abu bane mai sauki yaro mai tashe ga naira kaf garin babu wanda bai san shiba, bama garin ba kawai kaf kasan zance babu inda sunan shi bai jeba, yayin da wasu daka cikin kawayen fauziya din suke ganin mahmud bai dace da ita ba, dan yafi karfinta, sun dai ja baki sunyi shuru suna dan gwalan Arziki.
Mahmud yama salma akwati set 12 yace na fitan biki ta amsa tana ta godiya tare da mai addu’a, nan tace yama amarya itama dai koh dan tasan halin kayanta, yace a’a mama ta mata, nan salma tace bata yarda ba shima ya kamata yayi yakai nashi, yace na mama ya isa babu abun da zai kuma yi, tace toh shikenan ni Zan dauki 6 ka kai mata 6, kima daina bata bakin ki dan babu abunda zaki dauka wallahi duka amarya xa’a kaima nan duka suka waiga salma tace sannu da zuwa mama tace dallah yimin shuru makira kai kuma sannu shanyayye ka kyauta wannan shine adalcin to wlh baka isa ba duka za’a kaima fauziya yace haba mama ita salma fah ta daka mai tsawa kai mahmud ka shiga hankalinka wlh tun kafin inci maka mutunci, naga wuyanka yayi kauri ina fada kana fada toh baka isa ba nice mai iko dakai kuma yanzu xan nuna maka ikon, ina so ka saki salma indai nice na haifeka………..
Maryam Obam????
????????????KISSA KO MAKIRCI????????????
NA
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA
(Mrs nura kuriga)
25to30
Faduwa yayi kasa da gwiwowin shi, yana hawaye kaman wani karamin yaro wanda bai ma san yana yiba, salma koh gaba daya komai nata ya tsaya ko miyau ta kasa hadiye wa saboda firgita da kalaman hjy binta, ta kalli mahmud cikin fushi tace bada kai nake ba, amma ganin halin da dan nata ya shiga yasa taji wani iri domin duk duniya bata da kaman shi, kuma ita da kanta tasan yana mata biyayya, tabbas idan ta matsa mishi zai iya shiga wani hali, ta kalli salma ji take kaman ta kasheta dan haushi yarinyar nan na rasa wani kalan asiri tama mahmud da baya ganin kowa sai ita, mahmud dinne ya katse mata tunani da fadin mama zanyi duk abunda kika ce, bana fata Allah ya nuna min ranan da zanyi miki gardama a rayuwa na, tabbas salma itace macen da nake so kuma nake son in rayu da ita, rabuwa na da ita kaman barazana ne da rayuwa na, wlh indai na rabu da salma zan iya shiga cikin wani Hali, hjy binta tasan tabbas abunda ya fada hakan ne dan tasan akan wannan makiran salman zai iya shiga ko wani hali, tace dakata mahmud naji wannan karan zan hakura amma ka sani duk ranan daka nuna ma fauziya rashin adalci akan salma saika rabu da ita wlh kaji na rantse, tun yanzu ya kamata kasa son fauziya ma a ranka, in banda abun yaro wake Kin nashi yaso bare, fauziya yar uwarka ce inma abu zakayi sai nata yafi yawa saboda yan uwantaka, Amma kai naga baka san haka ba toh tun yanzu ka dai daita sahun ka, kar inji kar ingani maza ka kwashe akwatin ka kaima fauziya yanzu ya amsa da toh tare da fadin ngd mama, tace ni xan tafi, salma tace ki gaida gida mama, ta sakar mata harara tare da fadin idan ina magana da d’ana ki daina sa baki, salma taja baki ta tsuke tare dayin kasa dakai, tayi tsaki ta fita, shima ya bita,
Nan salma ta saki kukan da take boyewa tare da fadin wannan wani irin rayuwa ne, dan mijina ya nuna min so sai dangin shi su tsaneni shin laifi ne dan ya soni a matsayina na matarshi, na rasa mai yasa suke cemin na shanye shi, ladabi da biyayya ya zama shine tsafi, ni da ko hanyar zuwa gun boka ban sani ba, mai ya hadani da tsafi, jin motsin kaman mahmud yana shigowa yasa tayi sauri ta goge hawayen amma lokaci ya Kure dan ya ganta, ta sakar mishi murmushi tare da fadin har ta wuce? Ya kafa mata ido tare da fadin salma kukan mai kikeyi? Tace babu komai dear, yace kar kimin karya ban sanki da hakan ba, kiyi hakuri salma nasan abunda mama take miki ne yake…… Tayi sauri ta toshe mai baki tare da fadin dear mai kake fada haka, mama ta isa tace komai a kaina kuma ta isa tamin ko wani irin abu dan a matsayin uwa nake kallon ta, kaga mahaifiya tana da ikon tayi ma yaranta fada babu mai cewa komai kuma, wani irin son salma yaji yana shigarshi, tabbas salma samun mace mai irin halinki sai an tona, tayi dan murmushi tare da fadin tashi muje in tayaka diban kayan nan ka kaima kanwata, ya janyota jikin shi tare da fadin nop ki zauna zansa a diba a kai, nan suka shiga faranta ma juna rai.
WAI WAYE MAHMUD
mahmud El-hassan ya taso cikin gata, kasan cewan shine d’a guda daya wajan iyayenshi duk wanda mahaifiyarshi ta haifa sai su koma, shine kawai ya rayu, babu wani abu daya nema ya rasa, mahaifinshi tsohon minister ne na agriculture, sai da yayi shekara takwas akai, sannan aka canza wani ya koma kasuwanci ya tara dukiya wanda shi kanshi bai san adadinta ba, ya rasu a lokacin mahmud yana shekara ishirin da uku a duniya, yayi dan gajeran jinya, gaba daya komai na dukiyar shi ya koma hannun mahmud da mahaifiyarshi, wanda suka sa wasu suna kula da wasu aikin kasuwancin mahmud ya koma company din kera motoci wanda yake garin Abuja, lokaci kadan mahmud yayi suna kaman mahaifinshi, ya hadu da salma a garin katsina lokacin yaje bikin wani abokin shi, nan suka kulla soyayya abun daya burgeshi da ita, kunyanta da addininta dan a lokacin daya fara nuna yana sonta tace yaje ya fara ganin iyayenta kafin ya fara mata magana, aiko anan yace ya sami matar aure, kafin yabar katsina sai da yaje gidansu salma ya gabatar da kanshi kuma iyayenta mutanan kirki ne, mahaifin salma yana da rufin asiri, ya yaba da hankalin mahmud sosai yayi na’am dashi yace ya bashi izini in sun dai daita to shikenan nan mahmud yayi godiya ya bashi kudi yaki ansa yace bazai amsa ba, baya son haka, babu yanda mahmud baiyi ba yaki amsa, tun daka lokacin mahmud ya fara zaryan zuwa katsina wajan salma har mahaifiyarshi tace wai mai yake yawan zuwa yi katsina ne, nan ya sosa keya yace wajan salma, tace wacece salma kuma? Nan ya bata labari tace waye babanta yace sunanshi alh Muhammad, yana da mata daya yara biyu salma da hauwa, nan hajiya binta tace miye aikin shi? Yace yana dai da rufin asiri tsohon ma’aikacin gwamnati ne, ta tabe baki tare da fadin wannan maganar ka barta mahmud ka nemi dai dai kai kaji, abun da mahaifiyarshi ta fada bai mishi dadi ba, domin ita ta nuna yar masu kudi take so ba tarbiya ba, yace mama salma tana da tarbiya sai yasa nake sonta, ta nuna mai Sam yabar maganan, ganin taki na’am yaje ya sami wani yayanta wanda suke uba daya ya fada mishi nan yazo ya mata nasiha akan taji tsoran Allah Arziki da talauci duk na Allah koh ita lokacin da mijinta ya aureta suna da Arziki ne, babu shiri tace babu komai suyi duk abun daya dace, kaf yan gidansu hajiya binta suna tsoran haruna shine babba, yayin da gaba daya dangin ta suke girmamata dan tana da kudi shine kawai yake gaya mata magana ya zauna lafiya, mahaifinsu matanshi uku, jamila tana da yara uku, haruna shamsu, rabi, sai aysha itace ta biyu , tana da diya daya fatima binta,sai larai itace ta uku tana da yara biyu zaliha, habiba