KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 21 to 30

Salma har yanzu bata farka ba, mahmud gaba daya ya kasa sukuni, hankalinshi a tashe yake, ya tambayi Dr yakai sau goma yaushe zata farka amsa dai daya yake bashi, bai sani ba amma koda yaushe zata iya tashi, sai wajan karfe uku na rana ta bude ido tare dayin salati mahmud dake gefen gadon bai san ta farka ba dan a hankula tayi salatin, ta hango mahmud a gefenta lokaci daya abun daya faru ya fara dawo mata nan ta saki kuka tare da tambaya maiya faru dani, mahmud yayi sauri ya tashi dan yaji sheshekan kukanta, yace salma dan Allah kibar kuka, ya kamota tare da rungumeta yace salma dan Allah kiyi hakuri nasan na miki laifi babba wlh salma nima na rasa mai yasa nayi haka ji nayi kaman ana turani, am……, tace mahmud badan haka nake kuka ba komai kayi ai matarka ce, ina kuka ne kawai dana ganni a nan ban san maiya faru dani ba, kalamanta yasa gaba daya jikinshi yayi sanyi tare da kara tausaya mata, ya tabbata abun daya faru jiya shiya sata cikin wannan halin amma gudun karta sashi damuwa tace ba abun bane yake damunta, nan ya tashi yace bari ina zuwa, bai dade ba ya dawo tare da driver dasu flaks da kayan tea, nan ya hada mata ya bata tasha, tana sha gaba daya ta amayar dashi a jikinshi, babu abunda yake fada sai sannu, harta gama sannan ya tashi yayi toilet da ita, ya wanke mata jikinta,ya kalleta yace tana da number din hauwa a kai tace eh, ta bashi yasa a phone din driver ya kirata ya fada mata halin da suke ciki, yace ta kawo ma salma kaya, tace toh, nan ya kura mata ido yana kallonta yana murmushi, tasa hannu ta rufe kirjinta, abun ya bashi dariya yace yau ni akema haka, ta dan saki dariya tace naga kallon yayi yawa ne, yace albishirinki tace goro, yace salma Allah ya anshi addu’ar mu, saimu kara gode mai, cikin kosawa taji abun daya faru tace ina jinka, nan yace salma kina da……… Nocking suka ji, yace waye nan yaji muryan hauwa, ya bude tare da amsan kayan ya rufe kofan, yasa mata kayan jallabiya ce, tace ina da me?? Ya matsa kusa da kunnenta yace kina da ciki, lokaci daya wani hawaye ya xubo mata tare dayi ma Allah godiya, yau itace dauke da ciki, 

Fauziya tunda ta shiga gidan ta feshe shi da turaran da boka ya bata, jiran dawowan salma kawai take, tayi dan dariya badai ki haiyu anan ba wlh domin ni ya kamata ace na haiyu da mahmud bake ba, tabdi wlh zan iya aikata komai akan inga babu cikin nan. 

Dr yazo yaga jikin salma da sauki, yace zasu iya tafiya gida, amma karta dinga d’aga hankalinta, nan ya rubuta mata magani sannan suka wuce, saida suka fara ajiye hauwa kafin suka nufi gida, bayan sun shiga falo nan taji jiri yana neman dauketa tayi sauri ta rike mahmud dan yanda take ganin dishi2 shi kuma gaba daya ya rikice yana fadin salma salma, amma gaba daya bata san yana yiba, fauziya dake d’aki taji maganan shi ta fito da sauri ganin halin da salma ke ciki yasa ta saki dariya tare da fadin ciki sai dai kiga anayi badai ke ki dauka ba, ganin wani ruwa yayi yana xuba daka kafarta da sauri ya dauketa ya kuma fita da ita suka koma asibiti, nan fauziya ta saki shewa burinta ya cika.. 

Maryam obam????

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button