KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 21 to 30

Washe gari tunda mahmud ya nufi masallaci da asuba, bayan an idar da sallah ya nufi dakin salma, ya ganta akan dadduma, nan ta gaidashi ya amsa cikin fara’a yayin da ita kuma take jin kishi dan tana ganin komai ya faru yanzu, ta tashi ta dauki dadduman ta ninke, mahmud yazo yayi hugging dinta yace dear mai yake faruwa, tayi murmurshi tace babu komai, babyna ya kamata ka koma dakin amarya tunda mun gaisa, yace salma korana kikeyi koh? Ta zaro ido tare da fadin ni na isa in kori king dina, wanda duk duniya babu abunda nake son inga ina gani kaman ka, kaine kake sani farin ciki kaine rayuwa na, bana so kona minti daya kayi nesa dani, yace mai yasa toh yanzu kike korana? Tace dear ina sonka banso ka tashi cikin maza marasa adalci indai bazan daura ka akan hanya ba ai bana sonka ta karashe maganan cikin sanyin murya, yayi murmurshi tare dajin dadin kalamanta salma kina sani farin ciki sai yasa koda ina fushi ke daya ce zaki iya sani dariya da nishad’i ya bata fake a saman goshinta tare da fadin ngd dear sannan ya fita, bayan ya koma dakin fauziya ya sameta kwance yanda ya barta, ya girgiza kai ya fara tashin ta, tace mai nene? Yace kinyi sallah ta amsa da eh nayi, amma badan tayi ba dan dai kawai kar yasa ta tashi daka baccin ta. 

Salma bayan mahmud yabar dakinta kitchen ta nufa dan ta hada breakfast, cikin lokaci kadan ta gama ta jera a dinning sannan ta koma dakinta, tayi wanka ta shirya cikin wani atamfa dinkin riga da skirt ya mata kyau sosai, ta koma parlor ta zauna dan jiransu su sauko, wajan 10 mahmud ya fito yace dear kinyi kyau mahmud a kullum salma kara kyau take mai, yazo ya zauna kusa da ita tare da kafeta da ido, tayi dariya tace my lafiya? Yace ina kallon halali na ne, tayi dariya tare da tashi zata bar wajan ya janyota ta fado jikinshi, ta fara mai magana kaman mai rad’a tace dear bafa mu kad’ai bane yace sai akayi ya, tayi shuru ba tare data bashi amsa ba, tace muje kayi breakfast ina sister na? Ya gane tana so ne ya saketa daka rikon daya mata dan ya fahimci bata so fauziya ta fito ta gansu a haka, yayi murmurshi tare da fadin tana d’aki, tace go and call her, yace kyaleta zata fito da kanta, tace dear itafa bakuwa ce bata riga ta saba ba, plx ka kirata yace ok my lovely wife, bari in kirata tayi murmurshi ya tashi ya nufi sama, Jim kadan sai gasu shida ita, tasa jallabiya, ko kallo salma bata isheta ba, ta nemi waje ta zauna, salma tace morning sister, kaman ba zata amsa ba, komai ta tuna kuma tace antashi lafiya? Salma tace lafiya qalau, ta tabe baki, salma ta hadama mahmud abinci sannan ta xuba nata, tace sister bismillah kar in xuba miki inyi miki kauro, fauziya cikin isa tace ai dama an saba tunda gida babu, mahmud yace aifa kam yanzu ne naga an shigo gari tunda kin fara neman kudi, ta daure fuska, mahmud yasan ta gaya ma salma magana ne shi kuma, ya bata amsa dai2 da ita, har suka kammala fauziya bata ce komai ba, sai mahmud da salma wanda suke fira jefi2, mahmud yace bari inje office yanzu Zan dawo akwai masu jirana, salma tace ok saika dawo take care, ya tsaya yau daka nan zaki min sallama, tayi dan murmurshi ta tashi ganin ta Mike fauziya itama ta tashi tana huci salma sukai waje mahmud ya wuce, tana shiga falo fauziya ta tareta tace naga kina wani rawan kai toh bari kiji kinga duk wannan abun da yake miki ni nace ya miki dan kar kice ya canza miki dan ya kawo ni, amma da kinga yanda yaban wuya jiya da kin tausaya min yace min baki da dadi kaman dusa kike, salma tayi dariya tace eh toh kin san indai namiji yaji dadin mace bazai barta ba ya fita koda wa yake jiranshi musamman a ranan daya fara saninta, ni nasan da hakan kuma sai yasa nace ya kara aure inda ban yarda ba aida bai auroki ba, so kuma maganan kice ya dinga kulani plx daka yau kice karya kara kulani indai ki kai hakan xan San dagaske ke Zuma ce tana fadin haka ta wuce tabar fauziya da bakin ciki, xan nuna miki ni Zuma ce kuma na isa nan bada dadewa ba….. 

Maryam Obam????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  40to45

Salma d’aki tayi abunta dan bata son dangin fauziya din suxo su sameta a falo, tana ko yin d’aki bata dade da shiga ba taji shewa da gud’a tare da habaice2 abun ko a jikinta ta kwanta abunta, ta fara bacci taji kaman mutum a kusa da ita, tayi sauri ta farka sukai ido biyu ya sakar mata murmushi tare da fadin wannan irin razanar fah? Ta kasa magana dan ta tsorata dan ita a zaton ta tasa key a dakin kuma ba tayi zaton mahmud din bane, saida ya janyota jikin shi, sannan tayi ajiyan zuciya, shima da kanshi yasan a tsorace take da zaman dan ya shigo yaji irin zage2 dasu fauziya sukeyi suna ganin shi sukai shuru, ta katse mai tunani da fadin yanzu ka dawo? Yace eh ban dade da shugowa ba, tayi murmushi tare da fadin wlcm, ban san zaka dawo yanzu bah gashi ban daura lunch ba am so sorry bari inje inma, yace no barshi na siyo mana gashi nan, ta kalleshi da mamaki tace siyo abinci kuma? Yace nasan yau gidan mutane zasu zo sai yasa nace bari in kawo, tayi dan murmushi tare da sauka a kan gadon ta dauko ledan fried rice ne da garden salad, sai kuma kaza, ta dauko musu drinks cikin fridge din dake dakin, nan suka ci suka koshi..

Su fauziya ana falo ita da kawayenta da yan uwanta, suna cin abinci yayin da ita fauziya din bata abincin take ba, wata daka cikin kawarta mai suna jamila suna kiranta da jamcy, kana ganinta kasan yar bariki ce wacce ta goge a harkan ansha mai fatar nan tayi jawur, tace fauzy ke yanzu a nan zaki zauna kina ganin yayi sama tun daxu ke an barki a nan, fauzy data qumu da bakin ciki ta tabe baki tace jamcy to mai kikeso inyi nan jamcy ta saki dariya tace lallai fauzy, ashe za kiyi sanyi dama akwai abun da xai sa kiyi shuru, tabdi amma kin ban mamaki ina zafin naki? Ina rigiman ki? Fauzy tace jamcy kin san mahmud shine namijin da nake so, ke kin san yanda akayi na shigo komai sai na bishi a hankali kin san dan rainin wayau babu abun daya hada ni dashi jiya sai bakaken maganganu, wai bazai taba niba, sai anyi min test, jamcy tace toh fah mai yake nufi? Fauziya tace abun da kike tunani, jamcy tace toh gskiya sai kinyi dagaske inba haka ba zaki zama yar kallo, dan wannan matar tashi ba’a zaune itama take ba, dan yanda yake sonta ai yayi yawa, wlh gwara ki farka kisan abunyi da ita, fauziya tace karki damu ni yanzu matsalata daya yanda zani wajan malam yaban wani abun, jamcy tace toh gskiya kema kin san wannan abune mai wuya, keda kike amarya ai babu hanyar fita, fauziya tayi dan gajeran tsaki tace ina zuwa tayi sama, kai tsaye dakinta ta shiga ta dauki waya ta kira mamanta, hjy zaliha ta dauka cikin fara’a nan fauziya tasa mata kuka tace lafiya fauziya mai aka miki? Nan ta zayyane ma mamanta abunda ya faru, tace yanzu ma daya shugo yana dakinta Tun dazu, koda ya shigo ko magana bai min ba, yayi wajan matarshi, nan hjy zaliha tace kiyi shuru fauziya karki damu yanzu zan fita zani wajan malam komai ya faru zaki jini, kar ki kara xubar da hawayenki a banza, dan kuka ba naki bane, tace mama kisan duk yanda xa’ayi aban abunda xan mallaki mahmud, sannan a rabashi da salma, hjy zaliha tace an gama bari inje yanzu banso mutane su shigo suji abunda ke faruwa, sai kin jini ta kashe wayan, ta yayibi gyale ta fita. 

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button