KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 21 to 30

Kawayen amarya sai wajan karfe goma suka bar gidan, mahmud shida salma suna tare sai dai yaje sallah ya dawo, duk yanda yaso ya sadu da salma taki yarda dan ta nuna mishi bai kamata ba, in sukai haka zasu shiga hakkin fauziya, ganin kaman ya danyi fushi abun da bata saba gani ba a tare dashi, tace dear plx kar kayi fushi dani wlh fushin ka a kaina ba alkairi bane, ya dan juya mata baya, ta juyo ta gabanshi tana hawaye gaba daya ya rude tare da riko ta, cikin tashin hankali yace salma mai yasa ki hawaye, tace ba kai bane, cikin shagwaba, yace sorry my baby, ki daina plz bana so, bana son abun da zai saki bacin rai, tace nima haka yau naga abun da baka taba yi min ba, kayi fushi dani, ban hanaka kaina da gangan ba sai dai gudun kar insa kayi zalinci domin Allah zai kama ka, tunda bani bace dakai, zamu shiga hakkin fauxiya tunda bata yarda kayi hakan ba, kaga gwara muyi hakuri, yayi murmushi tare da fadin na fahimceki salma kuma na gane, bakya taba yin kuskure komai kina yine akan abun da addini ya tsara, ngd ma Allah daya bani ke, tayi dariya cikin jin dadi tare da fadin ngd ina koda yaushe ina godiya da Allah ya bani kai a matsayin miji, domin duk wata mace irin mijin da take son samu kenan, yace waya fada miki? tayi dariya tace abun da yake zahiri ne ai, tace dear ka tashi ka tafi dare yayi dan naji shuru da alama babu kowa, bai musa ba ya tashi ya fita kai tsaye dakin fauxiya din ya nufa, ya ganta a zaune tana waya jin motsin shi yasa tayi sauri ta kashe, kallo daya ya mata ya kauda kai gefe ta tashi cikin isa da gadara tace sai yanzu ta barka kazo, bai kulata ba hakan ya mata xafi, tace anje ana cin amana ta toh wlh baka isa ba yau sai an ban hakki na wlh dan ban san abunda kake nufi dani ba, namiji ya koma mijin tace, yace ki koma ki nemo tarbiya da yanda ake magana da miji, domin mace mai tarbiya ba xatayi abun da kikeyi ba, tace naji bani da tarbiya din, nidai abu daya na sani kaban hakki na, ganin bazai iya da ita ba yasa yayi banza da ita ya kwanta abunshi, nan ta zauna tana ta fadin magana bai tankata ba, haka dai itama ta gaji ta kwanta.

Tunda ya fita sallah sa asuba, ta tashi ta dauki waya ta doka ma mamanta kira, ringing daya ta dauka, fauziya tace wai ina kika shiga tun jiya inata kiranki baya shiga,, tace kedai bari, tunda na fita sai wajan daya na dawo, fauziya tace an dace? Tace eh an dace amma da sharadi, tace name? Yaban na wanda zaki sami mahmud zai fara kulaki Amma yace bazai yi wani tasiri ba har sai kinje da kanki zai baki wanda zaki mallake shi gaba daya, yaji baya ganin kowa sai ke, tayi dariya cikin jin dadi tace an gama yanzu yaushe xan sami wanda ya baki tace anjima zan zo dakai na in kawo miki tace toh sai kinzo amma kixo da wuri tace babu komai, 

Wajan karfe goma koh saiga hjy zaliha taxo gidan, a lokacin salma tana falo, ta shigo da sallama salma ta amsa, tare da gaisheta ko kallo bata isheta ba, tayi sama dakin fauziya, tayi nocking fauziya ta bude ganin mamanta yasa ta saki dariya cikin jin dadi domin yau zata sami cikan burinta, bayan ta shigo ta zauna tace ina mahmud din tace baya nan ya fita, nan ta fito da maganin ta bata turare ne, tace kiyi amfani dashi ki tunkare shi zaki sha mamaki, tace mama Kin tabbata xaiyi aiki tace sai yasa yace ki gwada in yayi kije da kanki tace shikenan, tace mai kuka dafa ne dan ban karya ba, tace tashi muje kitchen din muga mai waccan mayyar ta dafa, nan suka fita salma na nan yanda ta barta daxu, hjy zaliha tace samun waje an tura min y’a d’aki ke kin fito falo kina kallo, koh ke ga mai gida, toh bari kiji kin kusa b….. Lokaci daya kuma tayi shuru tare dayin tsaki, ganin haka salma tayi d’aki, nan hjy zaliha aka zauna a dinning aka bude ciki ana kwasan abinci, sai wajan biyu tabar gidan,. 

Fauziya tana ta jiran mahmud ya dawo taji shuru to wai yau ina yaje ne banji motsin shiba? Wajan 8 taji an bude gate ta leka ta window taga shine ya dawo da sauri tasa turaran da aka bata, ta zauna dan ya shigo, amma taji shuru tace nasan yana dakin waccan shegiyar, ta tashi tayi dakin basa nan, nan tayi falo tagansu mahmud ya daure fuska dan yana yin shigan da tayi night gown ne sai wani da tasa a sama ana ganin jikinta, yace ke wai yaushe xakiyi hnkali ne, bata ce komai ba sai daura hannunta da tayi akan kirjinshi gaba daya ya fita hayyacin shi, ya riko hannunta yana shin shinawa ta kara makale shi, tace dear yaushe ka shigo yace tun dazu tace tashi muje d’aki kai nake jira, ya tashi tare dayin hugging dinta, salma wani irin jiri ta fara gani dakyar ta iya tafiya d’aki fauxiya tace kadan kika gani, mahmud gaba daya ya fita hayyacinshi baya ganin komai sai fauziya. 

Maryam Obam????

????????????KISSA KO MAKIRCI????????????

                 NA

MARYAM ALHASSAN DAN’IYA

(Mrs nura kuriga)

                  50to55

Tana kashe wayan tasa wata doguwar riga, ta dauki gyale, ta fita, tuki take amma gaba daya bata cikin haiyacinta, kai tsaye gidansu tayi, tana shiga tace mmnta taxo su wuce wajan malam, itama ta zira hijab suka nufi wajan malaminsu, sun tarar da Mutane a wajan sai da suka bi layi har yazo kansu suka shiga, yana ganin fauziya ya fara Washe baki, nan suka zauna, yace ya zaku zo ku biyu bayan nace ita daya zata xo? Nan hjy zaliha tace akwai matsala ne sai yasa ka gammu tare, ya daure fuska sannan yace tafita ta basu waje da fauziya zaiyi magana, nan ta tashi tayi waje tana fadin tuba nake, ya kalli fauziya yace ya akayi?? Tace maganin daka bani yayi aiki amma makirar matarshi na rasa mai tamai baya ganin kowa sai ita, yanzu ma tana asibiti ance tana dauke da juna biyu, yayi dariya tare da fadin yanzu mai know kikeso ayi mata? Tace a xubar da cikin domin indai ta haiyu na shiga uku komai nata ne, sannan asa ya tsaneta, inaso asashi ya soni kaman ranshi, na zama komai nace dashi za’ayi aiki a gidan, yace an gama ya taso yazo kusa da ita yana mata murmushi ganin haka yasa ta tamke fuska tare da fadin ya haka kuma? Yayi dariya warin bakin shi ya doketa, yace ta hakan ne kawai Zan baki abunda kikeso, tace bazan iya wannan abun dakai ba ka fadi ko nawa ne Zan baka, yace bana son kudi keee in kin yarda to, in baki yarda ba tashi ki tafi haushi ya kashe ki, nan ta zauna tayi shuru, can tace ta yarda, ya saki dariya nan suka fara aikata zina saboda neman abun duniya Allah ya tsare mana imanin mu, taji jiki sosai yayin da mlm shi kuma abun yamai dadi, nan ya bata magani yace tayi hayaki dashi, sannan ya bata wani turare yace ta feshe duka gidan dashi indai salma ta shaka toh cikin zai zube, sannan ya bata wani kwalli yace tasa indai sukai ido biyu da mahmud toh babu shi babu salma, yace wannan kwallin kar ki kuskura koda da rana daya kiki sawa duk ranan da kika yi fashi toh komai Zai baci, tace toh inya kare fah? Yayi dariya yace bazai kare ba, kullum zaki ganshi a cike, nan tayi godiya ta tashi dakyar ta fara tafiya dan taji jiki, har taxo wajan kofa ya kirata yace duk ranan sati ki dinga zuwa tace toh ta fita tana tsaki, nan taga mmnta tace suje, bayan sun fita tace ya kukayi tace yaban magani tace dakyau kar dai kiyi wasa gaskiya tace hauka nake inyi wasa tabdi da haka har suka karasa gidansu ta sauke mmnta sannan ta wuce gida, har yanzu mahmud bai dawo ba,

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button