KISSA KO MAKIRCI 1-END

KISSA KO MAKIRCI Page 41 to 50 (The End)

Yau salma ta tashi da mugun ciwon mara, saiya tashi ya lafa, Mahmud yana lura da ita, yace suje asibiti taki, sai da kyar da taga ciwon na karuwa, suna zuwa asibiti akace haiyuwa ne, nan aka kaita labour room, Mahmud ya kira hjy binta da hauwa, kusan a tare suka zo, asibitin, salamtu tare dasu salma suka zo, kowa yana rokan Allah ya sauketa lafiya, cikin ikon Allah bata wuce 30mnt ba ta haifo yan uku, maza biyu mace daya, waiyo Allah zo kuga murna wajan Mahmud da hajiya binta, abun ba’a magana, a ranan suka dawo gida basu kwana ba, Mahmud sai kashe kudi yake komai ya bayar yace a siyo shima ya siyo da kanshi, salma tace tana son ran suna a daura auren Mahmud, bata fada mishi ba, ta fadama hjy binta aiko hakan akayi ta tura mutane aka tafi ba tare da sanin Mahmud din ba, balle salamtu ita da bata san komai ba, an kashe naira kaman babu gobe, mazan ansa sunan mahaifin Mahmud el-hassan suna nickname nashi farhan, sai dayan kuma sunan baban salma Muhammad, nickname dinshi anan, sai macen kuma sunan Hjy binta fatima nickname dinta zarah, anci suna an watse har yan daurin aure sun dawo an daura, dama salma ta kira mai lalle ana gobe suna ta musu, kayan dakin fauxiya gaba daya an kwashe akasa sabo, tace salamtu taje tayi wanka ta bata kaya tasa, ta amsa tayi wankan sannan tasa ta fito, ta kaita dakin fauxiya tace ta zauna tana zuwa, Mahmud dake dakinta yana kallon yaranshi yana dariya, tazo itama tayi dariyan tare da kama hannunshi tace suje ya gani, bai musa ba yabi bayanta yaga tayi dakin fauziya din, ganin salamtu a ciki yasa abun ya bashi mamaki, itama kanta salamatu sai da taji faduwan gaba, salma tayi murmushi tare da fadin yau ka zama mijin salamatu itama ta zama matarka an daura muku aure yau, yace salma miye haka, nan ta fada mishi yanda akayi shuru yayi yana kallonta, salamatu kuma kuka takeyi, salma ta kama hannun Mahmud tare da zaunar dashi akan kujeran da salamatu take tace Allah ya baku zaman lafiya sannan ta fita, tana zuwa daki ta fashe da kuka tare da bakin kishi da taji yana taso mata, Lokaci daya ta share hawayen tare da koran shedan ta matsa kusa da yaranta tana kallonsu tana dariya tare da godema Allah, 

BAYAN WASU SHEKAR

salma ta kara zama babban mace, ga naira tana juyawa sosai, yanzu tana da yara biyar, ta kara haifan yara biyu maza duka, aka sa musu yusuf da Ibrahim, yayinda salamatu kuma take da yara biyu, mace daya namiji daya, zainab da usman, salma ta kara mallake zuciyar Mahmud da kissa irin nata, ga wani irin girma da salamatu take bata, sai abun da salma tace akeyi a gidan, komai na Mahmud yaso yasa sunanta tace a’a yasa na yaranshi, hakan kuma akayi, hjy zaliha itama Allah ya mata rasuwa bayan tayi jinya mai tsawo taji jiki sosai tare dayin dana sani keya ce, 

Hauwa tazo gidan salma ita da yaranta su uku, suna ta fira da salma, hauwa tace wai salma har yau baki fadamin irin naki kissan ba, tayi dariya tace bari in fadamiki ba wasu abu bane masu Wuya kema kin sani sai dai kikiyi, hauwa tace inaji, salma tace hauwa da farko mace ta fara sanin waye mijin ta, tasan miye halinshi, tasan miye yake so miye baya so, babban abu shine kisa ma kanki hakuri, domin shi namiji a koda yaushe yana daukan kanshi sarki matarshi kuma baiwa, yana so Idan ya miki abu duk da shine da laifi ki bashi hakuri ki nuna kece da laifin bashi ba, sannan kuma duk wani hanya da zai sa ke kiyi mishi laifi karki bita, sannan Idan namiji yana fushi kar ki kai mai wata bukata naki kiyi hakuri har sai ya sakko koda kuwa bukatar babba ce, ki ajiyeta a gefe kisan yanda zaki rarrashe shi ya sauko, kar kice ke bai dameki ba tunda a waje aka bata mai rai kema bari ki kara mai wani toh kinga in kikai haka kinja ma kanki matsala, sannan karki dinga yima miji wasa da abinci koda kuwa kina fushi dashi kiyi mishi abinci dan namiji ya tsana yazo gida ya tarar ba’a mai abinci ba, wannan abun zai iya ja muku mugun matsala, sannan ki zama mai tattali da dukiyar miji, sannan Idan yace yana son abu ki nuna kin fishi so indai bai sabama addini ba, kaman ni a lokacin da yace zai kara aure mahaifiyarshi ta matsa mai, nace na amince banyi wani hayaniya ba, kinga a lokacin ji nayi kaman zanyi hauka dan tsabar kishi amma na daure na hakura, inda na tada hankalina na mishi hauka duk da yana sona sai yaji wani kala hala son ya ragu yazo ya fara gayamin magana shikenan na xubar da kimana wani namijin ma saiya sake ka, in kuma ka sami mai surutu saiya fadama amaryan haukn da kikeyi kinga tun kafin ta shigo ta raina ki, shima kin xubar da kimarki a wajanshi, amma da nayi hakuri kinga komai ya wuce, harta fauziya da aka daura mishi wani irin asiri ne ba tayi ba, amma da yake Allah yasan bani da hakki, sai abunta ya koma mata, mata da yawa inda zasu duba zasu ga asiri wlh baya aiki biyayya da iya kissa shike sa namiji ya soki, in kuma Allah ya jarabta mutum asirin yayi kwana arba’in ne fah ya karye, in Allah ya dauki ranki kina wannan aikin mai zaki cema Allah, sannan ko su bokayen zasu ce asiri baya yi sai da biyayya, Idan kikayi tunani tunda sunce haka sai ki duba dan me toh zan kashe kudina a banza, sai kiyi biyayyan kawai ki gani, hauwa tace wlh salma haka ne kinyi gaskiya, amma mai yasa kika karama Mahmud aure toh? Tayi murmushi tace hauwa duniyar guda nawa ce, mata da yawa sun sa bakin kishi akan kishiya inda zaki tara mata dari kice wai akan mai yasa suke kishi da kishiyoyinsu wlh dakyar ki sami guda goma wacce Zata ce ga dalili, kuma fah kar ki manta duniyar ba zama muka zo yiba, zamu mutu mu barta in kin hana mijinki aure Idan kika mutu zaki hanashi yine, ba zaki hanashi ba, gashi kin bata duniyar ki wajan malamai lahirar kuma kije bata samu ba, yanzu dana hada Mahmud da salamatu ba karamin kara daukaka nayi aranshi ba, haka itama yarinyar tana bani girma sosai mai yafi wannan dadi mijinka duk inda ya zauna yace ke yar aljanna ce, ya dinga labarin alherin ki a ko ina, salma tayi shuru tare da cewa kin san wani abu hauwa? Ta girgiza kai alaman a’a? Tace wannan abun da nayi shine kissa wacce babu bokan da zai baki ita, yanzu sai ki fadamin tsakanin KISSA KO MAKIRCI, Wanne yafi, hauwa tace KISSA nima na koya zanje inyi dan in gyara rayuwar gida na suka sa dariya tare da tafawa…. To nima dai anan zan tsaya.. 

      ALHAMDULILLAH

INA MIKA GODIYA GA MASOYA NA, WANDA DA BAZARKU NAKE RAWA ALLAH YABAR KAUNA MASU YIMIN MSG SUNA CEWA BANA REPLY KUYI HAKURI INSHA ALLAH ZAN DUBA SAKON KU ZAN BAKU AMSA NGD

GODIYA TA MUSSAMMAN GA

hajiya nafisa 

Amina aliyu 

Nana fiddausy 

Kawata hibbat 

Hassan atk 

      Ina godiya gareku akan karfafa min giwa da kukeyi ??

MASU SON MAGANA DANI SU NEMENI TA EMAIL DINA KAMAR HAKA: MARYAMALHASSAN206@GMAIL.COM

Share this

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button